" kindai ga karshen yanmata irinku masu biye ma son zuciya suyi ta aikata abubuwa marasa kyau,
" da sunan wayewa to yanzu Aisar wa gari ya waya kinji yace bazai iya aurenki ba",
Kuka sosai Aisar take ganin hawayen ta tuni yaji zuciyarsa namai zafi,
Kallonsa dr.bilki tayi tare da cire farin glass dinta ta ajiye gefe Tana kallon shaheed Wanda Kansa ke kasa ta tabbatar da maganganun ta sun fara ratsa zukatansu,
" kana da sana'a"
Daga kai yayi tare da cemata " eh" girgiza kai tayi,
" na tabbatar kuwa kai kai rike mace malam Aayan Baka tsoron abunda kai aikata kaima nan gaba ka Haifa 'ya mace a mata",
Cikin sauri ya daga Kansa yana kallonta sai kuma ya maida Kansa zuwa kasan,
" yes shiyasa a kace Ayi aure Wanda hakan bisa dokokin shariar musulunci ta yadda kowani daya zai hallata ga dayan,
" yadda zasu iya kadai ta su biya bukatar junansu ta hanyar saduwa kuma su rayu a matsayin miji da mata kuma harsu sama zuria,
" sai ga akasin hakan gunka kana son kasancewa da ita amma gashi Baka son aurenta",
Girgiza kai Aayan yayi " Hakane mana malam Aayan ko kana nufin dan ka saketa a bulus shikenan sauka nema wacce Baka sani ba"." Aa"
Aayan Yafada a hankali " Ga wani labari ku saurar a ku duka kuji",
Dukansu shiru sukai Aayan yana mamaki shin Ana iya samun mata masu wayewa da ilmi boko yaratsa irin ta kuwa,
" wata rana wani mutum yazo gun manzo (S.A.W) yana neman a bashi iznin yayi zina, sahabbai sukai masa tsawa, sai manzon Allah (S.A.W) yace su dakata,
"Ya tambayeshi shin ko yana so ayi zina da yarsa ko kanwarsa ko matarsa ko mahaifiyar sa?" Sai wannan mutumin yace " A'a",
" sai manzon Allah (S.A.W) yace " to kasani duk wacce zakayi zina da ita lallai ta zama yar wani ko kanwar wani ko matar wani ko mahaifiyar wani suma kuma basa so ba",
" a nan wannan wannan mutumin ya gano illar da zina ke haifarwa, sannan manzon Allah (S.A.W) ya dafa kirjin mutumin yace,
" Allahumma ahdi kalbahu wa sadid lisanahu",
Allahu Akbar ance tundaga wannan rana wannan mutumin baikara Jin sha'awar zina ba,
" kunji wannan kenan a nan nake jan hankulanku da kuji tsoron Allah kudaina aikata abunda kuke kuyi aure",
Sosai Aayan yake hawaye saboda abunda dr.bilki tafada tabbas gaskiya ne,
" Insha Allahu zan aureta"
" Alhamdulillah haka akeso Masha Allah" sosai Aisar kejin dadin abunda Aayan yafada.Shigowar su nafeesat office din ne ya katse masu tattaunawa da suke " kai dama Ashe Baka da mutunci",
Gadan2 ya nufi Aayan Wanda duk tsoro ya kamashi,
Take abbansu Aisar ya sheka masa mari,
" Yau sai usman Yafada mun inshi ya aiko ka kabata mun 'ya walh",
Ganin yadda Alhaji sani ke shiga yana fita yasa dr ta kira security dakyar aka Karba Aayan a hannunshi,
Iya mari kam Aayan yasha shi dan baa magana Sam,
Banda bala'i babu abunda Alhaji.sani ke yi a asibitin,
Dakyar nafisat tasha Kansa kansu tafi gida saboda Aisar da bata da lafiya sosai yakeson,
Dukanta amma ganin jikinta is serious yasa yabarta dan daya sauko dr.bilki ta masu bayanin komai kan ba raping bane,
Inda ta daura masu iyaye laifin abubuwan da Aisar din take Wanda su basu sani ba,
Faruk kuwa raba hanya sukai da Aayan kan yana da important abu ranar Aayan sukuku yadawo gaba daya,
" tabbas neman mata bai man rana ba" Yafada yana zaune,
Kiran dije ne ya katse mishi tunani ganin sunan ta a screen din yasa yaja dogon tsaki,
Yasan itama nata matsalar zata zo mishi dashi Wanda a yanzu baison komai da zai hadashi da wata mace." karki damu duk naji abunda kuka fada Insha Allahu Yau zankira meeting inda dukanmu har momcyn su Aaliyah zamu hadu",
" but Faruk how can we get Aaliyah out of the hospital",
Naja'atu ta tambayeshi murmushi yayi tare da girgiza kai,
" karku damu indai wannan ne I have a plan and I am sure zaiyi working",
Nan suka cigaba da planning yadda abubuwan zasu kasance inda daga karshe kowa yakama hanya,
Dan fara shirin yin part dinsa na aikin " all the best",
Faruk ya fada musu yana murmushi suma duka murmushi sukai suka maida mishi same word,
" all the best too".Da misalin 3pm momcy ce a kofar dakin da Aaliyah ke kwance tare da bodyguards dinta,
Inda suke ta musu da doctor ya dage shi bai sallama Aaliyah ba,
Amma ita sam ta dage Yau Aaliyah bazata kwana a hospital din nan ba yayi iya yinsa,
Amma karshe haka dole hospital din suka bar mata yarta,
Tafe suke a mota text message ya shigo wayar ta,
Cire black glasses din dake manner eyes dinta tayi tana dubawa,
" driver take us to the warehouse"
" yes ma'am",
Girgiza kai tayi " I just hope I am doing the right thing",
Suna karasawa Faruk ya isa garesu inda yasa aka fiddo Aaliyah aka shiga da ita ciki,
" meyasa ka kirani nan gurin"
" bari sukaita ciki akwai doctor zai duba ta",
Cijewa tayi tace bazaa shiga da yarta ba sai taga evidence din daya turo mata live,
Murmushi Faruk yayi yaciro wayar sa yayi latse2,
" kufito ta iso",
Momy sosai take jin tsoro but Tana son tasan gaskiya bazata iya ki ba da tunda ya mata text din farko zata share,
Fitowar Alina da Asiya tuni mom hankalinta ya tashi Tana kallon Aaliyah dake fama da oxygen ga kuma me kamanin ta sak gabanta,
Ganin ga kuma Alina a gefe yasa mom taji kanta yana juyawa batare da bata lokaci ba tafadi ta sume agun.Asiya itama mamaki ne ganin Aaliyah gabanta suna kokarin taimakon mom itama take ta sume,
" subhanallahi momy tashi momy"
Abunda Alina ke fada kenan nan da taimakon driver din mom da guard dinta,
Suka samu suka shiga dasu ciki inda doctor yayi kokarin basu taimakon gaggawa,
Baa dau lokaci ba Asiya ta farfado Tana farfadowa juyawa tayi inda cikin sa'a set din da fuskar Aaliyah yake ne wani irin,
Hawayene ya cika mata ido rasa me zatai tayi murna zatai ko kuka sauke legs dinta tayi,
Alina zata tabata Faruk ya mata alamu data barsu,
Karasawa gaban Aaliyah tayi ta fashe da kuka " dama kece Aaliyah da nake yawan mafarki koyaushe nake ganin nice a gidan masu kudi,
" Ashe dama inada yar uwa me komai iri daya dani",
Tafada tana rike da hannun Aaliyah cikin ikon Allah Aaliyah tafara motsa hannunta,
Jin hakan yasa Asiya tashi da sauri ta rungumota,
Ganin idanunta da jikinta na motsi yasa Faruk yace " doctor kaga" da sauri doctor din ya nufesu,
Inda ya bada iznin a fitar da Asiya haka ko akayi dakyar Asiya ta yarda ta saki Aaliyah.Koda haj.maryam ta farfado rungume yarta Asiya tayi tana kuka sosai dan tabbas tasan yan biyu ta haifa,
A kace mata dayar ta rasu sanda dan uwanta ya gudu da yar,
Amma haka nan ta danne tsawon shekaru tayi shiru da bakinta dan ko granny bata dan da itaba,
Baa jima ba doctor ya fito tare da good news dan Aaliyah ta tashi and she is fine,
Sai dai ya gargadesu da karsu nuna mata Asiya dan zai zo mata a shock inba'ayi wasa bama Tana iya Kara komawa coma din,
Dukansu basu ji dadin hakan ba nan dai Faruk yaba mom labarin komai inda mom taji dadi sosai,
Tayi ta samai albarka Tana godiya tayi alkawarin bafa taimakonta dan kawo karshen,
Dan uwan nata da amininsa taji dadin samun Asiya sosai tayi alkawarin zasu kauye amma sai komai ya dai2 dan a yanzu bataso a gane a ganta ko su sama labari Sam.Toko ya gurin su alhazan yake oho Ina boss ne ya zaiji plans dinsu ya rushe........sai a next page in Allah yakaimu👏
KAMU SEDANG MEMBACA
KOREN MACIJI
Fiksi UmumA story about twins sisters who got separated during birth but later got reunited in strange way.