Chapter 28

374 32 0
                                    



Aayan ne zaune falon baki sanda momyn Aaliyah tashiga ciki tashi yayi ya tsuguna yana kwasar gaisuwa,
Amsa mishi tayi ciki2 badan tanson magana dashi ba,
" momy dama nazo duba jikin Aaliyah ne",
Murmushi tayi tare da girgiza kai " kazo duba ta ko karasa mun ita iye meye mission dinda ubanka ya turo kai inba shiba",
" momy walh ba haka bane taya zan kashe yar uwata tajini",
" Au ho ta inda ya billo maka kenan wato kazo a matsayin dan uwa ka cutar mun da 'ya,
" to ka koma kace ma Usman din yayi karya wannan karon bazaiyi nasara ba Insha Allahu",
"Mo....",
" kai dakata! Tashi ka fice kabarmun gida dalilin dayasa nace a bari ka shigo bai wuce dan naja maka kunne kafita hanyar Aaliyah",
Yayi kokarin rokanta amma Sam momy ta rufe ido haka nan yatashi yabarta zaune falon,
Yana fita yaci karo da Aaliyah dake tsaye Tana hawaye baice mata komai ba ya wuce ta,
Falon tashiga momy na ganinta ta tashi " muje ki kwanta dan me kika taso",
" momy please I want to know meyake faruwa koyaushe kike hanani hulda da Aayan kuma kina yawan cewa mahaifinsa why momy",
Kallon Aaliyah tayi tabbas lokaci yayi da kowa zai San sirrin amma bazata iya fada mata yanzu ba sai ta warke,
Nan tayi ta rokon ta dakyar Aaliyah ta hakura.

2WEEKS KENAN

" granny doctor yace yanzu I am perfectly owk meyasa baa barina naje office",
Rike baki granny tayi tana kallonta " Zaki amma ba yanzu ki bari momyn ki zata baki dama",
Turo baki Aaliyah tayi a dole baa kyau ta mata tunda yanzu jikinta da kwari zaman gidan ya isheta,
" muje muyi kallon wadan nan India din naku zee world kike ce mata naga wannan muguwar ya akeciki",
Dariya Aaliyah " granny kice Nisha kike son gani walh I am very tired of them nafison na tanu da Aaliyah",
Dariya granny tayi " dake me sunan ki ce shaidaniyar ae dole kiso su" Dariya su duka suka shigayi,
sallama momy tayi suka amsa tace " surprise",
Murmushi Aaliyah tayi momy ta kalleta da kyau karasawa tayi kusa da ita,
" please Aaliyah kome zan nuna miki karki tsorata kinfi kowa sanin bazan taba hurting dinki ba ko",
Murmushi Aaliyah tayi " yes mom I am waiting",
" close your eyes first",
Take Aaliyah tayi closing eyes dinta momy tace,
" kushigo",
Asiya da Alina ne suka shigo tare da Faruk dake bayansu,
" now you can open them".

A hankali ta bude idannun nata ta daurasu kansu kasa kwakwaran motsi tayi sai lips dinta dake rawa,
" Alina ce Aaliyah bata mutu ba wannan is your twins ta bace tun bayan haihuwarku",
Still Aaliyah batace komai ba murza idannunta tayi dan a tunanin ta mafarki take,
" mom please pinch me kina nufin ba mafarkin nake ba",
Mintsininta mom din tayi " ouch da zafi mom that means reality ne",
Tuni ma'aikatan gidan suka firfito hatta me gadi ganin ikon Allah tashi Aaliyah tayi,
A hankali takarasa gaban Alina takai hannu zata tabata sai kuma ta cire da sauri ta waiga Tana kallon mom dinta da ido mom din tamata alamun bakomai,
Tana tabata ta dauke sai kuma ta jawota ta rungume,
" Alina!"
Fashewa sukai da kuka su duka daga bisani sukai shiru sai kuma ta juyo kan Asiya,
Kai hannu tayi fuskarta tana shafawa ta dago hannunta nan mamaki ya rufe ta dama Tana da yar uwa,
Zame wa tayi tayi kasa ta fashe da kuka ganin haka sosai ran Asiya ke sosuwa kasa itama tayi,
Sukaita kuka aka rasa wazai ba wani baki bawanda baiyi hawaye falon ba sun jima a haka,
Daga bi sani aka shiga hira.

Shigowar iyayen Alina ne ya dakatar dasu nan aka kuma shiga wata murnar inda,
Alina tashiga basu labarin rayuwar ta shiga ba abunda ta boye masu ba Wanda bai tausaya mata ba,
" shi kuma Faruk da kuke gani dan marigayi ne Alh.Habib",
Momy ta fada masu nan Faruk yaba dadyn Alina labari dan abokin mahaifinsu ne sosai,
" nagode Allah daya rayani ya rayaku muka ga wannan rana mai albarka Faruk,
" naji ma Ina naimanku kodan na damka maku dukiyar mahaifanku dan anyi nabayar danginku amma Sam naki kamar nasan akwai wannan ranar,
" dan Ana ganin kuma ankashe ku araba dukiyar to Alhamdulillah komai naku yana nan Ana juya maku hatta company din mahaifinku",
Nan Dadynsu Alina yakira commissioner Yafada masa komai da yake tafiya,
Nan take police suka shiga binkice dan gudanar da aikinsu.

Aayan ne zaune gaban dadyn shi a falo " dady gaskiya abunda ka aikata Baka kyauta ma yar uwarka ba,
" Baka ma momyn Aaliyah Adalciba ko kadan wal.....",
Tassssssss  kake ya dauke Aayan da mari me zafin gaske,
" ni zaka iya duka na amma me zaka ce da ubangiji kan mugayen abubuwan daka aikata iye",
" kai banson sakarci fa maza ka bace mun da gani yanzu nan",
Tashi Aayan yayi yafito sosai yaji ya tsani kanshi saboda mugun mahaifinsa da Allah yabashi,
Dady wayarsa ya jawo baa dau lokaci ba aka daga,
" ka samu labarin inda yake ",
Shiru yayi sai kuma ya cire wayar kamar zaiyi jifa da ita,
" search for him I need him to be found right now",
Yana fada yatashi ya dau key dinshi crime house dinshi ya dosa batare da sanin Ana biye dashi ba police,
Da Faruk a cikin motar saboda koda sunyi loosing,
Driving dady yake amma hankalinsa a tashe na rashin ganin Faruk bare yayi aikin sa,
Na kashe mishi Alh.sani suna biye dashi sai dai a hold up sukai loosing din motarshi.

" damn it we loose him"
" don't worry kai ba kasan inda yake zuwa ba",
Daga kai Faruk yayi yacigaba da kwatanta masu dan nemoshi,
Alh.Usman na horn aka bude mashi gate yana shiga yayi parking ya wuce ciki,
Bai jima da shiga ba yafara Jin gun shot da yaransa,
Yana lekawa yaga tare harda Alh.sani daga gefe nan akaita exchanging wuta cikin ikon Allah,
Suka gama da yaran dady inda suma da yawansu are shot suna gab da kofa ne police suka iso,
" hands up you are all under arrest" murmushi Alh.sani yayi ya daga hannu sai dai aka sama akasi,
Daya daga cikin Samarin ya bude wuta  police basu saurari komai ba suka bude masu wuta gaba daya,
Inda har sukai nasarar samun Alh.Usman dake cikin gida ya zube kasa sumamme,
Yayinda Alh.sani ya rigamu gidan gaskiya nan suka shiga cikin gidan inda gidan yazama crime scene gaba daya ansamu an kubutar da haarun yayinda aka dau Alh.Usman kwanco kam zuwa hospital.

Tuni gari ya dauka yan jarida da yan kallo sukayi yawa umman su nafeesat na kallon news,
Taji labarin Rasuwar mijin nata ae tuni tashiga kwala ma yaranta kira,
" innalillahi Wa'inna Ilaihir raji'un" tafada ta Yankees jiki ta sume,
Ranar dai a shiga tashin hankali sosai dan suma su Aayan tashin hankali suka shiga ba kadan ba,
Inda suka run kaya dukansu gidan harda kanwarshi zuwa hospital yayinda gun su momy yake kamar ranar Sallah duk,
Da cewan Tana Jin zafin abunda yasama dan uwanta sosai abun ke damunta,
Amma idan ta tuna hakan ne samun zaman lafiyarta da 'ya 'yanta sai taji dadi,
Bama kamar yadda su twins ke dauke mata kewa suna faranta mata rae sosai da sosai,
Rayuwa kenan.  Oya don't go akwai sauran stories fa😂😂😂 trust me dan ni Mimsqueen saina ga wa Aayan zai aura ya Aaliyah zataji kan playing dinta dayayi.



           Mimsqueen takuce a kullum masoyana Inayinku sosai irin totally din nan😍😍😍😘

KOREN MACIJIWo Geschichten leben. Entdecke jetzt