Chapter 18

337 27 0
                                    



" what do you think we should do for now",
Alina ta tambaya Faruk " abunda zamuyi shine musa ido kan dukkan motsinsu,
" so that we can sabotage all their evil plans"
Kallonsa Alina tayi " but how" murmushi Faruk yayi " good question but inaso Zaki yi wani aiki",
Cike da alamun tambaya ta dubeshi " something like..",
" being a nurse"zaro ido tayi tana kallonsa,
" nurse fa kace but you know I am a doctor why zan zama nurse ba field dina bane",
Rike head dinsa yayi yana nodding " oh my god just listen to the plan",
Khadijah dake saurarensu ne ta kalleta tamata alamun tayi shiru cinno baki tayi,
Dan Sam ta tsani aikin nurse " amma meyasa kakeso naje hospital meya faru",
" I want us to save Aaliyah" zaro ido su duka sukai,
" Aaliyah!!!" Suka fada a tare suna kallonshi,
" yes Tana coma yanzu haka and I found out jiya wani guy dina cewan Alhaji suna da plan da doctor din akan Aaliyah",
Dukansu basuji dadin labarin ba " I will surely do this kodan nayi saving Aaliyah",
Nan dae sukaci gaba da tattauna yadda zasuyi saving din Aaliyah nan sukaita tattauna wa karshe dae Alina zata hospital din.

" mama kiduba halin da Aaliyah ke ciki a dalilina"
Hawayen dake zuba fuskarta granny tashare " karki damu maryam wannan a laifinki bane sam,
" kiyi ta mata addu'a nasan Aaliyah na zata tashi nan kusa yadda take son granny",
Shigowar Nurse din ne yasa su duka suka dago,
" inaga su mama kudunga zama daga waje saboda hayaniya",
Kadai kai granny tayi " ba inda zanje Ina kusa da yar jikata koyaushe",
Girgiza kai nurse din tayi tashiga tayi abubuwan daya kai ta dakin tafita tabarsu,
Nan suka cigaba da kallon Aaliyah wacce Sam bako alamun motsi a tattare da ita.

Karban kayan tayi kamar yadda budurwar ke mata tsawa hannunta na rawa,
Zuwa tayi dan tasa amma me Sam tarasa yadda zatai,
Dan Sam bata saka kananun kaya hakan yasa tayi shiru agun kamar daga sama takarajin muryar budurwar,
" kiyi sauri dallah ke muke jira" daya daga cikin guard din ne ya matso kusa da budurwar,
" Boss yabada order she should be treated with respect like a queen so no shouting",
Kallonsa tayi tare da hararsa " I won't stop deal with it",
Nodding din Kansa yayi yakoma gefe saboda sanin halinta,
A hankali Asiya ta leko saboda yadda taji kayan sun kamata banda kunya ba abunda takeji,
Ganin zata bata masu lokaci yasa budurwar taje ta jawo hannun Asiya Tana tirjewa amma haka tafita da ita.
Zaune yake fuskarshi na kallon Tv da alama kallo yake,
Jin fitowar su da magiyar da Asiya ke yi na rokon da budurwar yamata baida ya waigo ba,
" Samir! Samir!!" Mutumin ya kira sunan ba'ayi 2sec ba Samir din ya bayyana a falon,
" Sir!" Yafada da karfi kamar wani soja saboda kirar halittar sa,
Dagani kasan irin masu training din nan ne.

" inaso kaduba hannun Salma kaga da wani hannu ta rike yarinyar nan",
Kallon juna sukai shida Salma dake rike da hannun Asiya,
" hannun hagune sir"
Kada kai boss din yayi " gud now i want you to take Salma out and cut her hand inaso yanzu naji ihunta",
Tuni Salma ta zube agun Tana kuka " kayi mun rae kayi hakuri dan Allahwalh bazan kuma ba",
" mekake jira!"
Tuni Samir yakira daya daga cikin su sukai waje da salma,
Jikin Asiya ne yakara bari akan Wanda takeyi da saboda tsoro,
" Asiya!"
Yakira sunanta tuni jikinta ke kakkarwa wani irin Kara Salma tasa Wanda yakara tsorata Asiya take tafadi kasa sumammiya,
Nan da nan boss yakira doctor zuwa inda yake koda doctor yazo ya duddubata mamakine kwance a fuskarshi,
Rasa ma meyake faruwa yayi inda boss yayi threatening dinshi karya kuskura yaji labari a waje,
Dole haka doctor ya yarda kodan lafiyarsa data iyalansa,
Bacci sosai Asiya tashiga yi me dadi saboda laushin bed din ma daban ne kallonta yayi,
Ya girgiza kai yaja kofar ya fita abun shi.

" Sir why did you change the iv injection that is suppose to be given to that girl",
Wani irin kallo ya watso mata tuni taja bakinta tayi shiru,
Maida Kansa yayi yacigaba da rubuta abubuwan da yake bukata a paper din yana gamawa ya dago ya mika mata,
" get me this things right away" batare da tace komai ba tajuya,
Tana tafe Tana tunanin abunda doctor ke shirin yima patient Wanda yasaba Shari'ar likitanci sam,
Direct pharmacy din ta nufa da paper din,
" Nurse! Nurse!!" Juyowa tayi da sauri Tana kallon mekiran nata,
Ganin ta cikin kayan nurse itama yasa ta maka mata uban harara tare da yin tsaki,
" dawa kike tsaki"
Tabe baki nurse din tayi " banda kin Rainani ma taya kina new a wannan wajen ki dunga kwala mun kira",
Mamakine ya rufe Alina yasa ta sake baki Tana kallonta,
" kintsai dani inzakiyi magana do it now or leave kinzo kina wani kirana nurse as if you are different mstw",
Alina naso ta biye mata ta hango Khadijah namata alama da tayi hakuri haka nan badan tazo ba ta hadiye,
" bakomai dama doctor ne yace kiban takardar na karbo mai magungunan",
Fari tayi da ido tare mika mata takardar har Alina ta juya ta kirata,
" jimana"
Cike da takaici Alina tajuya Tana kallonta.

" you look like a new comer ke sabuwace"
Daga kai Alina tayi alamun eh Kara tabe baki nurse din tayi,
" hope ba volunteer bace ke ko yar practical",
Nan ma Alina daga kai tayi alamun ita nurse ce sosai,
" sunana farida but Zaki iya calling dina senior farida saboda na rigaki zuwa wannan hospital din",
Daga kai Alina tayi tana kallon mummunar budurwar data kira kanta farida harda wani senior,
" owk Toh"
" what was that meye owk to" farida tafada tana kallon Alina wacce tuni takai bango da halin yarinyar,
" Farida! Mekike a nan kizo maza zamu fara aiki yanzu",
Jin an kirata yasa ta bar Alina tsaye agun wacce takaici da zafin da zuciyar ta ke mata yasa takasa koda kwakwaran motsi,
Kiran ta Faruk yayi ganin yanayinta dake yana daga nesa Tana ganin abunda ke faruwa,
Bata ce mai komai ba yagama bata hakuri yasa ta tayi abunda yakawo su na sauya takardar,
Alluran saida suka sauya masu takardu dan suyi matching na doctor din a mota dan gudun karya gane,
" I think you can start going now" dafa kirjinta tayi tana kallon su Faruk,
" walh inajin tsoro Faruk yanzu aka kamani fa ya zanyi"
Murmushi Faruk yayi me sauti " haba bayan duk mun gama shirya komai karki manta munada mutane a hospital din,
" zasu dunga taimakonki a ko wani step ko stage Wanda a hankali Zaki Sansu ba 1time ba",
Fita tayi daga motar sukai sallama takama hanyar hospital din.

Guri ne me kyau harda furanni tafe take tana wake2 dinta nakauye,
Tunda take bata taba ganin gu mekyan wannan ba,
Jin alamun numfashi no mutum tafara yi a bayan wata bishiya Wanda akeyi kamar sheshekar kuka,
Ganin  wata budurwa tayi kanta cikin guiwowinta Tana shesheka da alama kuka takeyi,
A hankali ta isa gun budurwar takai 2mins Tana kallonta,
Can takai hannunta da niyyar tabata kan ta tabata budurwar ta dago sak kamanin su daya,
" kitaimake ni! Help me please!!" Bude baki Asiya tayi a tsorace,
Ita kuma waccan tanata Kara maimaita mata wannan kalmar,
Wani KOREN MACIJI ne yafito daga cikin koren ciyayin gun yana kokarin sarar wannan mekama da itan yayinda take dada daga muryar ta taimaketa,
Wani irin ihu Asiya tayi tare da bude idonta daga mafarkin da karfi ta tashi zaune,
Tana wani irin zufa Tana nishi jikinta har wani bari yake yi.

 

                   Muhadu a next page in Allah yakaimu👏

KOREN MACIJIKde žijí příběhy. Začni objevovat