Chapter 4

672 31 0
                                    

          🅿️111 to 115

" Wayooooo!!!" Ihun da tayi kenan tare da rufe kunnuwanta da idanunta,
Ihun da ya Aisha tajine yasa tafito dakinsu Adan guje a tsorace ta tura kofar dakin da Asiya take,
Amma gam tajita a rufe sai surutan Asiya datake ji " umma kitaimakeni zaikasheni",
Surutai take tana ihu sosai " lafiya!" Yafito da sauri ya Aisha takalleshi cikin damuwa,
" Asiya ce naji ihunta gashi ta rufe kofar ta ciki" kallon kofar yayi tare da yin murmushi ta gefe,
" bari nagwada kozan iya balleta" baya yayi yadawo ya bugi kofar,
Haka yayi sai da yayi na hudu kafin kofar ta budu,
" Asiya meya faru" ya Aisha tafada sanda ta karasa dakin da gudu,
Dago Asiya tayi da tayi jagab da gumi amma me ture ta Asiya take cike da tsoro har a lokacin idonta a rufe yake,
" Asiya ki tsaya yayarkice" tafada tana kuka ganin yadda yar uwarta ke cikin wani hali.

" matsa Aisha saketa" yafada sanda yasa hannu yajawo Asiya wacce dai2 ta bude idanunta,
Idanunsu ne suka hade sanda yake rike ta cikin sauri da tsoro tashige jikinsa,
Shiru tayi a wannan lokacin sai ajiyyar zuciya da take cike da mamaki ya Aisha ke kallon su,
Mamakin ta baiwuce yadda akayi har takita amma sai baban salim ba,
" Aisha yi maza kije kidauko ruwa" jikinta a sanyaye ta tashi tafita zuwa dauko ruwan,
Gogan kuwa Jin Asiya jikinsa tuni yake shafa gashin ta yana lumshe ido,
" ya isa babyna you are safe" abunda yake fada kenan kamar me radi yana shafa gashinta,
Jin motsin Aisha yasa yayi sauri ya saketa yakwantar da ita " bakomai Asiya nida yar uwarki muna nan ba abunda zai faru kinji",
Yafada kamar gaske taji meya fada hakan ya kwantar ma ya Aisha hankali,
Tashigo ganin Asiya kwance yasa tayi murmushi " inaga fa mafarkine",
Girgiza kai yayi " ba shakka bata ruwan tasha kilallaba ta tasamu takoma bacci" Yafada cikin dakakkiyar murya yafice dakin,
Asiya ba uhm ba uhm2 Sam bata ce komai ba haka sukai kwana nan.

Koda suka tashi da safe Asiya tamanta anyi Sam bare wani mafarki duk yadda ya Aisha taso tambayarta hakan baisamu ba,
Kamar kullum yau ma baban salim ne yasauke ta school sai dai yau dari biyar yabata kudin break tayi mamaki,
Juyawa yayi yatafi tana mai godiya ta wuce ciki abunta shima yakama nasa hanyar,
" malam haruna kenan daga Ina kake ne" kallonsa baban salim yayi cikin Jin haushi,
" meyasa bakajine Kabir nasha fada maka kadaina bata mun suna kana kirana wani haruna in zaka kirani haarun fine kokayi shiru",
Dariya Wanda yakira Kabir din yayi " to naji ayi hakuri me ya meye labari to",
Murmushi baban salim yayi " hmm kai dai bari aikin nan yayi kyau fa amma akwai yar matsala",
Matsawa kusa dashi Kabir din yayi " mekake nufi wace matsala kuma",
" Aisha! Walh itace matsalar bazata bani damar samun abunda nake so ba inhar tana cikin hayyacinta" dariyar Kabir yayi,
" wannan ae karamar matsala ce indai kan wannan ne zamu koma gun malam anjima inmun tashi aiki",
" amma Kabir a matse nake fa" dariya Kabir yayi tare da kai mai dukan wasa,
" wato dai kai yanzu kahada biyu ya matar ka kanwa kuma ta hutu" Sam baiji dadin kalaman Kabir ba Kansa " walh son Asiya nake kuma zan aure ta ba lalata nakeso da itaba zan aure ta very soon" Yafada Kabir dai kada kai yayi " muje yau akwai aiki fa sosai" nan su duka suka shige kowa yayi nasa bangaren.

Shigowa gidan tayi cikin bacin rae " Aaliyah! Aaliyah!! Aaliyah!!!",
Duk gidan muryarta ce ta karade ko ina Aaliyah dake kwance cinyar granny tashi tayi cikin sauri,
" lafiya momy kemun irin wannan kir...." kafin ta karasa suka ji anbude kofar,
" dan iskanci how many times have I warn you cewan kidaina barin office batare da kin fadamun ba" sosai take fada idonta ya rufe sosai ko sanin da da granny dakin bata lura ba,
" ya hakuri kisaurareni" granny tafada sai a lokacin mom tagane tana gun,
" muje dakin ki" granny tafada sanda ta tashi ta nufi mom,
Juyawa sukai suka bar dakin Aaliyah kuwa zama tai kan gado,
" why is she so angry like na kashe mutum" ta fada tana turobaki,
" ko dake haka take always my God but I love my mother so much yakamata naje nabata hakuri" tafada maimakon ta tashi saita koma ta kwanta,
" not now saita sauko maybe zaifi" tafada tare da gyara kwanciyarta.

KOREN MACIJIDove le storie prendono vita. Scoprilo ora