🅿️196 to 200
" doctor kana tare dani"
Cike da tashin hankali doctor ke cigaba da goge zufar dake karyo mai,
" inasaurarenka Alhaji",
" good choice" Alhaji Yafada tare da tashi tsaye yana zagaye tsawon 1mins baice ma doctor komai ba,
Sai can ya zagayo tabata tare da dafa kafadar doctor,
A hankali yafara mai bayani " inaso kasata taita bacci kamar yadda tafara yanzu",
Adan zabure doctor ya juya suka hada ido da doctor Wanda ke dauke da murmushi,
"You mean she should sleep forever" doctor ya tambaya a tsorace,
Girgiza kai Alhaji sani yayi " no sam she should not die kawae make sure she stay in that coma until I ask you to ka fahimceni",
Nodding din head dinsa doctor yayi " what about my son",
" karka damu as long as you keep following my orders your son will be spare so what are you waiting for",
Yafada tare da kwashewa da Dariya kai kace ya zaucene,
" zan tafi yanzu but zan dunga shigowa every 2days to check any mistake will not be forgiving,
" sanin Kanka ne Waye Alhaji sani i am a man of my word bye",
Yana kaiwa nan yafice abunsa yana murmushi yabar doctor cike da tashin hankali da damuwa,
Sai yanzu yake Dana sanin sanin Alhaji sani tunfarko." Aayan why do you have long face" kallon sa Aayan yayi tare da nodding din kai,
" ae dole kaganni a haka is obvious" murmushi Faruk yayi,
" ko kabata da Aisar ne"
Tabe baki Aayan yayi " walh ko daya dake dama niba wani sonta nake ba mezai sani daga hankali kanta",
Dariya Faruk yayi tare da dan bugunsa " you are such a bad boy kasani",
" yes walh nasani you can say anything ma dan i don't know meke damuna a yanzu nasan gaba daya bana cikin farin ciki Sam",
Kallonsa Faruk yayi " kayi sounding serious I am just joking" Yafada yana dafe da kafadunsa,
" I know but I deserves bad words maybe even more than that",
Yakara kamar me shirin kuka " wai frnd Yau meke damunka you are sounding different",
"Yes dole friend koka san Aaliyah na hospital saboda ni",
Cike da mamaki Faruk ke kallon abokin nashi,
" kamar ya kake nufi"
" yes I am responsible for her condition a yanzu ",
" kana getting dina worried be more specific please",
Shiru sukai na mins batare da kowa Yama dan uwansa magana ba sai can tukunna yake ba Faruk abunda yafaru sosai yake feeling guilty.Jawo shi Faruk yayi ya rungume shi saboda ga duk alama kuka yake shirin yi tunda yake kusan this is the first time dayaga Aayan cikin damuwa,
" kayi hakuri is not your fault dama can abunda ya faru a rubuce yake",
" but Faruk da banje da niyyar cutar ta ba da hakan bai faru ba gaskiya inason Aaliyah,
" koba komai she always love me I want to love her back and protect her"
Sosai Faruk yaji dadin abunda Aayan ke fadi " yes my friend this is the kind of friend I always want you to be",
Kwacewa Aayan yayi " so bakason nada kenan",
Dariya Faruk yayi " no but today is the first time danaji kafadi sensible kuma I always know tun a school kana son Aaliyah kaki accepting ne",
"No!"
Oh yes!!"
Dariya su duka sukayi sai kuma fuskar Aayan ta sauya sosai tunawa da bukatar dad dinsa,
" what is wrong again yanzu fa kake dariya",
" just kawae natuna bukatar dady ne kana ganin dady zai taba accepting din naso ta da gaske na aureta",
" why not bafa dady zai zauna make da mata ba hope kasani",
" yes amma what of in Aaliyah tasama labarin komai",
" she won't kota samu she will forgive you tunda Tana sonka itama",
Murmushi Aayan yayi " I will be her protector from today ko dady bazan bari ya cutar da itaba",
" hooo aikam lover boy is in real love after all the fake journey you are such a green snake friend",
Dariya su duka sukai.BANGAREN SU ASIYA
Tafe take zuciyar ta cike da damuwa gane wa da tayi tabbas ita ba yarsu ummanta bace,
" to su waye iyayena"
Tambayar datai ma kanta kenan tare da komawa gefe jikin bangon wani gida ta tsaya,
" Asiya kwaila" musa Yafada sanda yazo wucewa ko kallon inda yake batai ba harya wuce yadawo da baya,
" Asisi Asiya Asiya mekan zawayi" kallonsa tayi tamaida kanta kasa batare data tanka shiba,
Ganin haka yasa yamatsa gabanta " lafiya Asiya ko kinzubda kudine" girgiza mai kai tayi,
Wata motace tayo kansu Baka da gudun gaske tuni musa yafara kokarin gudu,
Asiya ko suman tsaye tayi cak burki a kasa inda aka bude motar wasu karti biyu sukayi ciki da Asiya,
Musa ganin sun sata mota sunyi kwana yasama ikon ihu yana neman taimako ina tuni sunyi gaba,
Gidansu Asiya ya nufa da gudu yana ihu ya burma ciki bako sallama umma Tana tatan kamu,
Sai ya Aisha dake ma afranta wanka a tsakar gidan,
Ganin musa da gudu bakaramun tada masu hankali yayi ba,
" lafiya musa meyake faruwa" umma ta tambaya sanda ta yarda abun tatar nata " umma! umma!! Wasu sunzo Sundau Asiya"
" a ina musa mekake nufi" ya Aisha ta tambayeshi,
" a bakar mota suka zo suka sata ciki suka tafi",
Umar ne ya shigo gidan saurinsa " umma kinga wasu shegun motoci da suka shigo kauyen nan Yau kuwa",
Salati umma tayi dan zancen musa ya tabbata " shikenan Asiya na" zama tayi gun tana kuka,
Ya Aisha kanta hankalin ta atashe yake kasa rarrashin imman tayi dan itama cikin yanayin la haula take." umar jeka nemo babanku maza yasan meke far...",
Shigowar babane ya katse maganar da take son karasawa,
" menake ji agari yanzun nan nakejin wasu motoci sunshigo gari sunfi ta ba'a sansu,
" nace bari nazo gida na duba ku dan ance tayo ta nan",
Kuka umma takara fashewa dashi " malam sun dauke mana Asiya ga musa yaga sanda suka sata a mota",
" hasbunallahu wani'imal wakil" abunda baba ya iya furtawa kenan tare da zama,
Ganin haka yasa umar matsawa kusa dashi meya tuna kuma sai ya tashi tsaye,
" musa Anya Kodai mafarki kayi ne bari naje a tambaya me gari kafin nan kaida umar kuje ku duddubota",
Basu musa shiba tuni suka fice inda suka bar umma nata sambatu,
" Aisha kinga irinta kunsa yarinya agaba da zagi da mugun ta yanzu Allah kadai yasan inda taje",
Sosai ya Aisha ke Dana sanin abunda ita da ummi sukai mata da safe Wanda shine dalilin fitarta,
Dan sunce Sam ita ba yar uwar su bace haka dai gari yadauka cewan masu babban mota Asiya suka dauke,
Wasu na ganin ' yan yankan kaine ma dan har anata zuwa masu umma jajen batar nata.Tunda suka dauketa Sam batasan inda hankalin ta yake ba,
Wani irin ruwa me mugun sanyi taji anwatsa mata cikin firgici da tsoro ta tashi Tana ihu,
Ganin mutanen dake gabanta tafara tika2 ai tuni ta hasko abunda yafaru hankalin ta yakara tashi,
Wata budurwa ce ta shigo rike da kaya a hannu fuskarta bako alamun Dara's aciki,
Watsa ma Asiya kayan tayi yayinda Asiya jikinta ke bari hatta hakoranta kana iyajin kararsu,
" dauki kisa!"
Cikin tsawa taimata magana Asiya batasan sanda ta diba kayan ba tafara kokarin cire rigarta,
Sa hannu matar tayi ta rike hannunta " ki shiga can kicanza ki fito and make no noice the boss is waiting",
Da sauri Asiya ta dau kayan tashige inda ta nuna mata dan yin yadda tafada matan.....
Tambayar shine waye boss? Meyasa ya dauko Asiya? Shin Aaliyah zata taba farkowa? Muhadu a next page dina.

DU LIEST GERADE
KOREN MACIJI
Aktuelle LiteraturA story about twins sisters who got separated during birth but later got reunited in strange way.