Chapter 20

409 26 0
                                    



Kwanan Alina Yau biyar kenan a hospital din ta saba da mutane ba laifi tafara sakin jiki,
Especially da naja'atu wacce ke kula da ita kan komai nata,
Zaune take kan kujerar kusa da dakin da Aaliyah take taji granny na " doctor! doctor!!",
Da sauri ta tashi ta rufe fuskarta yadda granny bazata gane taba tashiga,
" yan nan Aaliyah ta motsa hannunta" tafada tana nuna mata side din,
Alina wani irin sanyi taji a ranta amma tasan ba'a nan gizo ke sakaba,
" banganiba ba"
Alina tafada tana duba gun ganin ba motsin yasa granny rudani da mamaki " amma yanzu fa naga ta motsa",
" yana faruwa baba karki damu Insha Allahu very soon zata tashi",
" Ameen yar nan",
Gyara mata kwanciya Alina tayi tafita bata tsaya ko ina ba sai direct gun zamansu itada naja'atu,
Tako yi Saar samu ta dan ta tashi duty tana shirin tafiya gida,
" yanzu ko nake tunaninki",
Tafada tana murmushi " eh walh nima cewa nayi bari nazo nasamu naje gida na huta",
Kallonta naja'atu tayi tare da Dariya " da alama dae kinason ganin mutumin naki ne kawae",
" kai haba dae ko daya",
Dariya su duka sukayi " yes ya kuma kamata naganshi danakwai improvement daya kamata yasani tun basu datse ba".

Naja'atu murmushi tayi tana ninke fararen uniform dinta,
" aikuwa bara nakira yarinyar nan dan ta isa gun kafin wani yaje",
Fara tube nata uniform din tayi Alina tare da maida kayan gidanta,
Sunayi suna hira har suka kamalla suka fito,
Inda kowa yayi hanyarsa dan yin abunda ke gabansa.
Tunda ya shigo hospital din yake tambayar dakin da aka kwantar da Aaliyah,
Hango ta yayi tana kokarin fita daga cikin area din zaro ido yayi cike da mamaki,
" Alina!"
Ya fada cike da mamaki ganin da gaske ita yake gani yasa yakai hannunsa idonsa yana sharewa,
Still yana hango ta Tana ta tafiyarta hankalin kwance,
Da sauri ya nufi hanyar da zai sada su da ita sam ita bata San yana yiba da sauri,
Sauri yake kokarin tare ta harta fita gate din sai dai yayi rashin sa'a tana fita tashige ke ke naphep tayi gaba da ita wani irin,
Bakin ciki yaji yana shigarsa " oh my god dama Tana raye",
Tambayar daya ma Kansa kenan sai kuma ya girgiza kai " Anya ba mai kama da Alina bace",
Nan ma still ba answer hakan yasa ya koma cikin asibiti yana dube2 ko zai sama Wanda ysan dakinda Aaliyah take.

Kwana yasha yana dube2 dinsa yaci karo da farida,
Wacce ke dauke da dan tray irin nasu na hospital Wanda bakomai ciki illa su injection da medicine,
" washhhh"
Tafada sanda suka bugu tare da dake tray din a kasa,
" dallah malam baka ganine da tsakar rana amma kana tafiya kamar makaho ji abunda kamun",
" karki yarda kiyi insulting dina ke din baki ganine ko bakisan kwana bace iye ni matsa I have something important to take care of",
Cike da fada takalleshi " au bama hakuri zaka bayar ba to walh saika biya wadan nan abubuwan daka fasa dan medication din mutane ne",
" bazan biya ba"
Yana fada yafara kokarin wuce ta riko rigarsa tayi,
Tuni suka tara yan kallo " malam you must pay",
Aayan kasa cewa komai yayi dan tunda yake baitaba ganin mace masifaffiya irin farida ba,
" dakata sakeshi" doctor ne yamata magana saida ta harareshi kafin ta sake shi,
Banda kallon ikon Allah babu abunda Aayan yake,
" yanzu farida Ina hanaki fada da mutane amma kullum bakiji da dambe kikeso kiyi da namiji,
" baki tsoron ya miki mugun duka",
" tabdi Allah ya kiyaye wannan girman biredin ya dukeni",
" to naji malam kayi hakuri kaje kawae abunka",
Doctor yaba Aayan hakuri tabe baki farida ta dunga yi tana hararshi,
Bataso ya tafi bai biya ba amma saboda jama'ar dake gun da doctor da kuma yan uwanta nurses,
Dake ganin fadanta da rashin hakurinta yasa ta hakura tabarshi yatafi,
Cikin ikon Allah yana kwana ya hango ta ta window kan bed,
Wani irin dadine ya rufeshi da sauri ya isa gunshiga yaji wani mugun mari a fuskarshi,
Wanda har saida ganinsa ya dauke na wasu second.

" Nan dinma ka biyota ne bayan asanadiyarka tashiga cikin wannan hali iye",
Granny tafada tana nunashi rike da kuncinsa yake kallonta wasu irin hawaye ne masu zafi kebin kuncinsa " walh kayi kadan daga kai har uban ka yadda,
" uban ka yasa narasa dana a duniya bazan yarda kaima kayi sanadiyar jikata ba sam walh",
Jin kalamanta sosai Aayan ke mamaki especially ji dayayi granny tace dalilin dadynsa tarasa danta,
" maza ka bace mun da gani tun kafin namaka wani mugun abun ko mugun baki",
Karasawa yayi gabanta ya tsuguna " dan Allah baba kiyi hakuri kibarni naga Aaliyah dan Allah,
" walh banzo da niyyar cutar da ita ba sai dan naga lafiyar ta walh inaso ta kiyi hakuri",
Yadda yake kuka sosai taji kuma takasa korar tasa,
Yana kokarin shiga ne sukaji muryar momyn Aaliyah wacce ke dakatar dashi " karka kuskura ka karasa cikin dakin nan Aayan",
Juyowa su duka sukai suna kallonta ajiye babbar ledar dake hannunta tayi tana kallonsa,
Cike da bacin rae " Me kazoyi mekuma uban baka ya turo ka",
Sunkuyawa yayi kasa " inawuni momy" wani tsawa data dakai mai saida ya tsorata yatashi,
Ko kadan bata saurareshi ba ta koreshi yanaji yana gani aka hanashi ganin Aaliyah Sam,
Haka yabar asibitin cike da damuwa da fargaba da kuma son yasan asalin matsalar dake tsakanin iyayen nasu dan ada yazata dukiyane amma a yanzu yana tunanin akwai wani abun.

" yane boss na ciki ne"
Girgiza kai me aikin yayi Jin boss baya nan yasa haarun Jin wani irin nishadi nashigarsa,
" zan shiga ciki na duba wannan yarinyar ga wannan kasai nama kaci" da sauri yakarba kudin,
Shikuma ya wuce ciki  sai dai koda yakai kofa kofar da key a jiki knocking yafara,
Shiru tayi bata bude ba ko yunkurin budewa,
" Asiya yayanki ne haarun ki bude kofar magana kawae zamuyi ba abunda zanmiki",
Shiru Asiya tayi tana Kara shigewa cikin bargain ji take kamar kasa ta tsage ta shige ciki,
Komawa yayi da baya inda yaje yasama me aikin yana gyara gyare,
Ya tambayeshi key na dakin yayi ko sa'a akwai spare key din dakin,
Da murnanrsa yaje yasa key din yabude itako Jin yana kokarin budewa yasa taita nannade kanta da bargo,
" Asisina kinyi bacci ne" shiru tamai sanda yakaraso bakin bed din,
Jikinta har wani kakkarwa yake tsabar tsoro,
Sa hannu yayi ajikinta tana jinsa Kara matse ido tayi,
" Asiya meyasa kikeso kiba kanki wahala ki kuma bani iye dagaske sonki nake,
" zan iya komai akanki ba abunda bazan miki ba indai kika amince dani kinji kanwata",
Kara sake damkar bargon yake da karfi ita dai Kara shegewa take cike da tsoro sosai,
" Asiya ko kina tsorone karki rasa budurcinki",
Yakarasa yana dariya " to banda abunki zan iya aurenki indai dan wannan ne kawae kibada kai,
" a hankali zanmiki is a promise bazan bari kiji zafi ba sam ki daure nayi koda sau dayane",
Kara matse jikinta take batare da tace mai kalla ba ganin hakan yasa yatashi tsaye,
A tunanin ta zai barta ne saikuma yadawo yayo kanta inda yafara fizgar bargon,
Tana janshi a cikinta Tana kuma nannadashi yana warware shi sosai hakankalin Asiya yake a tashe.




             Sorry for my short page muhadu next page Insha Allahu zakuna samuna akai akai yanzu👏 dan Nima inaso na nannade tabarma na soon kan KOREN MACIJI.....

KOREN MACIJIWhere stories live. Discover now