" officer dan Allah kutaimake ni naga familyna please akwai abunda yasa nakeso naje,
" inaso naga yar uwata na basu hakuri kayima Allah",
Girgiza kai police din yayi ya kalleshi " zanyi magana da manya na insun ban dama zamuje,
" amma Yau zamu sake daya dan bin cike ya nuna bashi da laifi dan haka yanzu zanje mukammala inmungama maybe na nema permission",
Godiya dady ya dunga masa yana mai addu'a dan shi kam yasan mutuwa zaiyi bazai jima ba,
Bare ciwon dake cikinsa yadda yake mishi (wato inda aka harbeshi),
Officer din ya jima kusan 1hr yadawo yace ma dady yazo suje dan nan shima wancan da aka sake zaije." Dije inaso kifada mun gaskiya taakaninki da Allah waya miki ciki",
Shiru Dije tayi Sam takasa dago kanta falon daga momy sai ita dan Aaliyah taje wanka,
Sun shafe tsawon lokaci amma taki fada,
" momy wae tun tuni taki fada miki",
" eh walh taki magana",
Saukowa su Aaliyah sukai su duka kayan jikinsu iri daya ne har zan iya cewa inba abu sukai ba bazaka gane su ba,
" gani nan ae walh in bata fada ba hmm ",
Karasowa sukai inda Aaliyah takai ma Dije duka,
Asiya na kokarin tarewa amma saida ta same ta tashi Dije tayi tana Kara ihu kamar wacce akai mata mugun duka " walh Aayan ne!",
Dukansu are very shocked da sunan Aayan da tayi taking Aaliyah ce tace " what! Banjiki da kyau ba waya miki ciki",
Cikin rawar murya Dije tace " Aayna ne",
Zama Aaliyah tayi take idanunta suka sauya sukai ja cike da bacin rae,
Sallamar momyn Aayan ne falon ya yakatse su,
Suka shigo gefenta Aayan ne shima yayi sallama Jin muryarsa yasa Aaliyah ta tashi,
" Aayan meya kawo ka gidanmu gate out!",
Tafada da karfi kuka ne yazo mata dakyar Asiya da momy suka nitsar da ita,
Nan su Alina suma suka shigo dasu umman Asiya ae da gudu Asiya taje ta shige jikin ummanta.Alina kuma ganin yanayin Aaliyah yasa tajata zuwa daki suka bar jama'ar a falo suna gaggaisawa,
" what is going on na jiki kina screaming why?",
Kara fashewa Aaliyah tayi da kuka " tell me mana",
" Alina kinsan Aayan yama Dije ciki" zaro ido Alina tayi cikin shock sai dai batai mamaki ba,
" Aaliyah kin tuna nafada miki Munyi soyayya da Aayan amma yayi cheating dina",
Daga kai alamun eh Aaliyah tayi " amma ban fada miki irin relationship din da mukai ba ko",
Nan ma shiru Aaliyah tayi " to Aayan and I has being sleeping with each other",
Tashi Aaliyah tayi " what! Even you" girgiza kai Alina tayi,
" yes Aaliyah I was madly in love with Aayan a lokacin babu abunda bazan iya mishi ba a duniya kuma kinsan Ina clubbing sosai,
" inada Samari sosai masu sona ba Wanda yataba sanin ribar kwanciya dani sai shi infact,
" Aayan shi yayi disverging dina Aaliyah nasha zuwa gidansu a dakin Faruk muke love making lokuta da dama",
Girgiza kai Aaliyah tayi " wannan labari ne kawae Alina kike kirkiro mun amma Faruk bai saniba",
" walh ya San komai kawae yajima yana sona tun bansan kaina ba",
Nan Alina taba Aaliyah labarin abubuwan da suka faru." Tabbas Aayan ya cika mayaudari" nan suka cigaba da hira,
" kufito su momy na neman ku",
Asiya tafada ta juya tabarsu " muje ko",
Aaliyah tafada tashi Alina tayi suka fita inda suka tarar anata hiran abubuwan da suka faru,
Baba da umma da ya Aisha sosai suka Jin jina lamarin abubuwan da suka faru,
Inda baba ke basu labarin yadda ya sama Asiya,
" wata rana da raddare nafito massalaci zan koma gida wasu mutane nagani suna tsaye,
" a hannun dayan jaririya ce wacce keta tsala kuka naji zuciyata Sam bata aminta dasu ba,
" har zan tunkaresu naga ba kowa kuma na hangi maka mai a tattare dasu hakan yasa naga gwanda na wuce,
Har zan wuce naji dayan yana cewa " boss me zai Hana muka she yar jaririyar w huta",
Jin haka yasa Wanda ke dauke da yarinyar ya wanke shi da mari yana cewa,
" Baka da hankali jinin nawa zan kashe ba zan taba kashe ta ba",
Jin hakan yasa naji kwarin gwiwar tunkararsu inda suna ganina suka fara muzurai." batun Allah karku cutar dani banzo dan na cuceku ba nima dan Allah meyasa kuka dauko jaririn nan a cikin wannan dare ga sanyi",
Dayan cikin su ne yayo kaina " dallah malam kayi wucewarka Ina ruwa...",
Me jaririyar hannu ne yaban answer koda idonsa rufe yake shidin dan bangs fuskar shiba Sam,
" kashe ta zamu yi karshe",
" subhanallahi me tayi maku zakuce zaku kashe ta abunda batasan komai ba haba kuji tsoron Allah kumaida ma mahaifiyar ta",
" kaga malam gata inkana so munbaka" ya miko mun jaririyar,
Kin mika hannu nayi ya kalleni " inbaka karba ba kaima sai mun sheke ka",
Jin hakan yasa na amsheta su kuma suka tafi Ina kallo sukai kwana najima tsaye agun,
Kafin me rike da itan yazo naji tsoron sake ganinsa,
Nan ya yayi ta rokona da Allah da annabi kan na rike ta amana wataran zai dawo ya nemeta,
Kamar bazan karba ba amma tunda yace Allah da annabi naji na amince na wuce gida da ita,
Nasama uwar dakina na sanar mata komai ta amsa hannu bibbiyu washe gari naje gun megari,
Da zancen kowa yabada shawarar na rike ta sosai kuma cikin ikon Allah dake me dakina bata jima da haihuwa ba,
Yarinya ta sama ruwan Nono tashiga ranmu sosai hakan yasa bamu babban ta ta da yaranmu sam,
Sai da ta girma yayyun kingansu ya nuna ya Aisha su suka fito suka bayyana mata sirrin,
Dan son zuciya.Ba Wanda labarin bai ratsa ba a falon daga nan ne suka juya kan batun Aayan bayan angama jajanta zancen Asiya,
" Aayan kaji me maman ma tafada shin kai kama yarinyar nan ciki",
Bai musa ba ya amsa inda ya basu labarin duk abunda yafaru,
Har zuwa gunsa da Dije take sosai mom tayi mamaki,
" lallai yaron Yau ka Haifa da da cikin ka",
Nan dai sukaita mai nasiha nan aka ita cigaba da jajanta ma juna,
Aisha sai zare ido take tana kallon katon gidan ga ma'aikata ace wannan shine gidansu Asiya yarda ta wulakanta kan dan iskan mijin ta,
" Ya ina yarana"
Murmushi ya Aisha tayi " walh suna gida muka barsu gun ummi",
Jin ummi yasa yanayin fuskar Asiya ya sauya ganin haka yasa Aisha ta riko hannunta,
" Asiya kiyi hakuri ki yafe mana ummi ma tace na baki hakuri kafin ku hadu walh rudun shaidanne,
" yasa muka aikata abunda mukai miki kiyi hakuri dan Allah",
Murmushi Asiya tayi tace " bakomai na yafe",
Abinci Chris ya jera masu nan momy tafara serving dinsu gidan ba laifi yadau jama'a,
Dan Ana shirin cin abinci momyn Alina da yarta suma suka shigo inda suma baa barsu a baya ba.Basu kammala ba megadi ya shigo yace akwai baki a waje harda police,
Nan su duka suka fita dan ganin meke faruwa,
Asiya na ganin haarun tafara buya jikin ya Aisha sosai jikinta ke bari tuna abunda ya mata,
Wasu hawaye ne masu zafi da tausayi suke zuba idon Aisha tabbas haarun ya kwaresu bashida imani,
Nan ya tsuguna gabansu yana bada hakuri inda baba yace dole ya sakar masu 'ya,
Shima dady rokon yar uwar sa ya shiga yi,
Inda ya tabbatar mata shiya sama mijinta guba a abinci kuma ya kashe har babansu Faruk,
Bawanda yayi mamaki sai dai abunka da yar uwa tuni ta rungume shi Tana kuna sosai,
Dakyar police suka tafi dashi dan in 2days za'a kashe shi shima court ta riga ta yanke mai hukunci,
Ihun Chris yaja hankalinsu zuwa cikin gidan inda suka tarar da........
Sai Allah ya hadamu a page dinmu na gaba Wanda shine last page👌Insha Allah
![](https://img.wattpad.com/cover/179699177-288-k782076.jpg)
YOU ARE READING
KOREN MACIJI
General FictionA story about twins sisters who got separated during birth but later got reunited in strange way.