Zaro wayarsa dady yayi ganin tafiyar Faruk din yayi dialing yasa a kunne " yafito kabisa duk inda yayi I want every detail on everything he does",
Ya kashe wayar ya fita yabar haarun kwance yana ihun naiman taimako yafita yana dariya,
Haarun bai taba ba dama a rayuwarsa irin wannan ba sam,
Damuwar sa bai wuce matarsa da 'yan 'yayansa ba da kuma 'yan uwansa hakan yasa,
Yake ta addu'oi dan ya samu ya kubuta da alkawarin bazai kuma aikata irin abunda yayi ba,
" ta Ina zan kalla Aisha nafada mata abunda na aikata"
Sai kuma ya fashe da kuka mai zafi." Aisar kin bani mamaki walh har garin yaya kika yarda hakan ta kasance dake taya Zaki maida kanki dabba",
Cikin kuka Aisar ta kalla yar uwar ta tace " haba sis ya Zaki kirani da dabba menayi",
Hararta nafy tayi jikinta har karkada yake dan bacin rae,
" uhmm abunda kike aikata wa shiga tabbatar da hakan walh kinbani kunya da mamaki,
" shin kinsan meye babancin mutum da dabba kuwa akan irin abunda kika aikata tunda ba alkairy kikaiba sai zina da kuma zubar ma kanki mutunci",
Tashi Aisar tayi zata fita inda nafeesat ta jawo ta tamaida ta kan bed din,
" Ina Zaki ae bangama dake ba sam yanzu ma nafara"
Nafeesat sosai ranta yake mata kuna da abunda Aisar din tayi ita kanta tajima Tana son Aayan amma saigashi kanwarta ta rusa komai."Baki san abune me hatsarin gaske kika aikata ba Aisar kiba namiji kanki a waje ba,
" bare ke da yanzu ya bata miki rayuwa tun kina budurwa kina ganin iyayenshi koshi zai aureki",
" eh yace zai aureni"
Murmushi nafeesat tayi " karki manta bashi ke da kanshiba kuma nasan badan yana son aurenki ya amince ba kinsan me",
Girgiza kai Aisar tayi tana sauraron yar uwar ta tabbas ta aikata kuskure me girma,
Kuma bawani yajawo mata ba illa kanta tunda ita takai kanta ita kuma tayi abunda yasa hakan faruwa,
" tabbas abunda yar uwarki take fada miki gaskiyane abunda kika aikata Sam ba abu mekyau bane,
" walh ni Ina mamakin yanmatan yanzu da kuke yarda kuna ba maza kanku tun a waje da sunan soyayya Wanda,
" baku San mekuke jawo ma kanku ba na farko kuna zubar da kimarku da mutum cin ku kai harma Dana iyayenku," shiyasa sai ayi aure kwana biyu kinga komai ya lalace saboda an riga anzubar da komai a waje,
" kun dau kwadayi da buri kunsa a rayuwarku duk da wasu laifin iyayen su ne dan suma suna taka rawar gani gurin lalacewar yaransu Allah dae yasa mudace",
" Ameen umma nikaina abun yana bani mamaki ta yadda Aisar lalata rayuwarta",
" bari dai abbanku yadawo muji yadda suka kare da Alh.usman di..."
" meko zaku jira ai Usman Yau yabani mamaki ya cimun mutum ci sosai Wanda bakowa yaja mun ba sai wannan yar iskar yarinyar",
Yatafi yana shirin Kamo Aisar ya daketa ihu tashiga yi tana buya jikin nafeesat,
" Ae gwanda ka duketa dan walh nima dauriya naketa yi ganin zaku sassanta ayi auren tunda tuwona mainane"
" Abba dan Allah kayi mata hakuri dan girman Allah",
Dakyar nafeesat ta rokesu suka fita suka barsu inda baban ke basu labarin yadda sukai da dady,
Cikin fada." momy dan Allah kiyi ma dady magana kan zancena da yarinyar nan" kallonsa ta tsaya tanayi,
" ae ni bansan wace yarinyar kake magana ba meya hadaku kaida shi baajin kanku Yau kuma",
Sosai yake son fada mata amma kunya ta hanashi sai kame2 yake yana kallonta,
Ganin bazai iyaba yasa ta kalleshi sosai yake son dan nata,
" Aayan!"
" na'am momy"
" naji labarin abunda ya faru a bakin mahaifiyar ta tabbas abunda Kayi Baka kyau ta ba,
" amma naji dadi da kake tunanin gyara abunda ka aikata Insha Allahu zanyi kokari naga an rufe zancen,
" Amma ya batun yar uwarka Aaliyah"
Dagowa yayi yana kallonta sai yanzu ya tunada ita tunda yashiga matsala baya cikin hayyacinsa,
" Tana hospital",
" shin ko kasan dangan takar dake tsakaninku",
Girgiza kai yayi yana mamaki dan ya tuna kwanaki wani abu daya faru tsakanin momyn Aaliyah da Dadynsu Wanda dady yaki bashi amsa,
" dangan taka"
Daga kai tayi " kwarae kuna da dangan taka me karfi dan Aaliyah jininka ce nasha son fada maka amma Dadynku ya hana kusani"," amma momy wace irin dangan taka kike magana",
" Aaliyah kanwarka ce ma'ana cousins kuke"
Cike da mamaki Aayan ke kallon momynshi,
" cousins!"
" kwarae kuwa dan mahaifiyar Aaliyah kanwar mahaifinka ne uwa daya uba daya"
Wannan karon Aayan is very shock hakan yasa yakasa magana Sam " nasan abunda ke ranka bai wuce gaba da suke ba,
" wannan bazan amsa maka ba sai nan gaba kadan inaji ajikina komai zai tonu nan bada jimawa ba",
" Gabarsu tayi tsanani ko makiyi albarka",
Girgiza kai momynsa tayi tare da murmushi " Hakane kam amma kacigaba da kula da Aaliyah dan abubuwan nakara zama sai a hankali kwana kin nan",
Nan dai sukai hirarrakinsu karshe yabarta cike da mamaki ya nufi hospital din,
Amma ga mamakinsa ya tarar ansallameta Sam labarin bai mai dadi ba,
Ya juya ya nufi gida dan ganinta.Tunda Faruk yakama hanyar zuwa gida ya lura Ana following dinshi hakan yasa,
Maimakon yaje inda su Alina suke sai ya koma gidansu Aayan direct part dinshi ya wuce,
Sai da yashiga can ciki bayan ya rufe kofar kafin ya kira Alina,
" Faruk kana inane",
" Alina bazan fito ba sai komai ya lafa a yanzu",
" amma meyasa"
Shiru yayi yana tunanin Yafada mata koya sai dai yasan suka sani zasu shiga damuwa sosai,
" zanzo amma inaso kar Wanda yafita cikin ku har sai nazo zan dunga kiranku awaya Muna gaisawa",
" toshikenan Allah yakiyaye we gonna miss you",
Batare da yace mata komai ba ya kashe wayar cinno baki tayi tana kallon su khadijah,
" ke kuma lafiya kike cinno baki keda mutumin naki",
Khadijah Tafada tana mata Dariya kai mata duka tayi nan suka cigabada hira suna wasa,
Yayinda Asiya takasa uhm ko uhm uhm dan tayi zurfi a cikin duniyar tunanin mahaifiyar ta da sai yau tasan dasu da yar uwar haihuwarta.Alina ce ta lura da Asiya ta tabo Khadijah dake sheka Dariya tare da nuna mata,
Sosai sukaji tausayin ta Alina ce ta matsa ta rungume ta,
" kidaina damun kanki Insha Allahu komai zai dai2 Asiya ba gashi Yau har kinga mahaifiyarki da kawata yar uwarki Aaliyah ba",
" Hakane naji dadi sosai ganin su amma matsala ta bai wuce su zauna lafiya batare da ancutar mun dasu ba" Kara fashewa tayi da kuka,
Nan suka shiga rarrashinta sosai a hankali suka samu tayi shiru ta sama natsuwa,
" uhm dan Adam basu da ta ido daga taimako anba mutum makwanci da ci ya tashi yana Kara rarrime2 kamar gidan uwansa da ubansa",
Yunkurin tashi Alina tayi cike da fada sai Khadijah ta rike tare da mata alamu karta biye mata,
" sai an kula kashi yake doyi mtsw",
Asiya tafada dan ta lura hansai yar rainin wayoce takin karawa,
Dariya su Khadijah sukai Jin tafara sakin ranta,
" ke kuma ubanwa yasa sanwa dake uwar shishigi",
" hehehehe hansai kike kowa kike kikiyayeni idan akuyarki tana cin kasa ta kiyayi ta shuri walh",
Nan Asiya tafara kokarin tashi ganin fadan nasu na karuwa yasa Khadijah taja Asiya da Alina zuwa daki." matsoratan banza da wofi kuma bari inna tadawo saina hadaku da ita",
" kinji ma baki hadamu da ita ba yar rainin wayo kawae",
Asiya ta bata amsa " please Asiya shareta rashin aikinyi ke damunta" Khadijah tafada,
" aikam da alama" Alina ta cafke nan dai suka cigaba da sabgoginsu abunsu tuni matsalolinsu ya mantar dasu wata hansai.Bangaren Alh.Sani kwance yake a makeken falon nasa amma zuciyarsa banda,
Damuwa da fargaba babu abunda yake damunsa Sam tunda sukai magana da Alh.Usman yakasa samun natsuwa,
" Abba! Abba!! Lafiya"
Nafeesat take kiran sa sanda tashiga cikin falon Sam haryanzu baisan Tana kiran ba,
" Abba!!!"
Tafada da dan karfi hakan yasa yadawo hayyacinsa agigice,
" A'a nafeesatu kece"
" eh dady nashigo tuntuni ina magana Baka jiba Sam meyake faruwa ne",
Kura mata ido yayi sosai sai kuma yatashi zaune,
" bakomai Ina tunanin yadda zamu kare da Alh.Usman ne kinfi kowa sanin tsakaninmu,
" kinsani sarae ba lallai yabarni haka nan ba bama kaina nake jiye ma ba irin keda yar uwar ki da mahaifiyar ku da baruwanku",
Girgiza kai nafeesat tayi " Abba ba Wanda ya isa yamana abunda Allah bai mana ba walh,
" shiyasa nake yawan hanaka shiga mugayen ayyukan da yake saka kai amma ka rufe ido kai abokin kane kaima zai baka in ansama dukiyar koda nake tayaku kasan a dole nakeyi",
" bar wannan zancen yanzu mafita nake nema",
Shiru tayi dan batasan me zata ce mishi ba amma tabbas tasan Alh.Usman mugune bazai barsu ba,
Shiru sukai su duka ba Wanda ya kuma cewa kowa komai kowa da abunda yake sakawa a ransa.Sai mun hadu a next page Insha Allahu👌👏
YOU ARE READING
KOREN MACIJI
General FictionA story about twins sisters who got separated during birth but later got reunited in strange way.