" Nice babba kafin ke"
Aaliyah tafada tana dariya Asiya bata face tayi tana tabe baki,
" Granny kina jinta ko ae nice babba kafin ita ko",
Dariya granny ta kallesu " A'a niba ruwana ku tambaya uwarku" har cikin ranta take jin dadin ganin jikokin nata sosai,
" woo granny dae taki amsawa",
" Aaliyah ke baki girma da tsokana ne dan Allah why are you troubling your sister iye,
" oya come on I have something to give you guys",
Da sauri Aaliyah tace "wow Irin hadin fura da nonon nan naki me kwakwa wow",
Da sauri ta sauka ta dau cup daga cikin tray din da mom ta ajiye ta tsiyaya shiru Asiya tayi tana kallonsu,
" Aaliyah zubo min maza"
Dariya Aaliyah tayi " su granny baa girma da kwadayi ba",
Mom ce ta lura da shirun Asiya da yadda take kallonsu,
Matsawa kusa da ita tayi inda ta fashe mata da kuka,
Kukan nata ne yajawo hankalinsu Aaliyah sosai suke Jin kukan nata Sam basu son bacin ranta,
Tashi Aaliyah tayi taje kusa da ita kamar yara ta riko hannun yar uwar tata,
" sis Nina bata miki rae ko to kingirmeni tsokanarki nake dan Allah kiyi shiru",
Tuni idanun Aaliyah ya ciko da kwalla itama saboda Sam taki jinin abunda zai taba yar uwarta Sam." yan biyu kyautar Allah o daya yayi sai daya yayi",
Granny tafada tana kallonsu cike daso da kauna,
" nima inaso naje school na koya turanci irin naki sis",
Dariya su duka suka kwashe dashi " oh yaran nan dama wannan ne matsalar ki ki bari komai ya lafa Zaki yi har aiki Zaki kema kinji",
Daga kai tayi still goge hawaye take akan kyakyawar fuskar tata,
" kuma inaso naje naga su ummana dasu baba dan Allah momy",
Murmushi momy tayi tace " Insha Allahu",
Sake rungumarsu tayi gaba daya sosai take jin wani dadi a ranta,
" oya kuzo Musha haka nan Nina gaji da jiranku",
Granny tafada kwashe mata da Dariya sukai su duka bayan sun zuba sun fara Shane Aaliyah ta tabe baki,
" gaskiya saina Kara sugar momy"
" uhmm ke ae kinfiya son sugar sosai Allah yaraba ki da Zaki kam",
Murmushi Asiya tayi kawae taci gaba da Shan nata,
" Dije! Dije!! Dije!!!"
" Na'am"
Da gudu Dije tafito Tana goge hannunta da alama aiki take a kitchen din,
" ke yanzu wato sai ankira ki sau uku kike amsawa mutane ko tsabar iskanci ko",
Aaliyah tafada cike da masifa take kallonta kamar zata cinyeta." A'a walh Allah ba haka bane ban....",
"Shot up! Who ask for your useless explanation kawae kikawon sugar saura ya daukeki 1yr,
Dagata Asiya tayi takalleta alamu Asiya tai mata da ido da ta hakura,
Murmushi tamata ba yau kadai ba tagane yar uwar tata nada soft heart fiye da ita,
Sosai mom sukaji dadin yadda Asiya ke dan mata gyara kan rikicinta da masu aiki,
Da sauri Dije ta dauko abun sugar din ta kawo ma Aaliyah,
Sai dai Tana kokarin ajiye mata amai ya taso mata kafin ta rike shi tuni ta wanke Aaliya dake kokarin daukar abun sugar din,
Kasa motsi Aaliyah tayi yayinda kowa na falon yakasa magana sanin lallai akwai matsala,
Dije kuwa cigaba da sheka amanta ta cigaba saida ta idashi,
Tana kokarin ba Aaliyah hakuri wani a man ya taho ae da gudu ta kwasa tabar falon,
Tazo wucewa ta window Chris yaganta "ewooo!"
Yafada yana sa hannayensa akai yafito yabi bayanta inda ta tsaya pampo din baya Tana karasa amanta,
" Chaiiii na who give you belle for this house"
Shiru tamasa dan dukanta yayi a baya " I dey ask you something na who you gave you that thing which dey inside your belle".Sharesa tayi ta kama hanyar wuce sa fisgota yayi,
" you are such a useless girl I keep begging you to give me make I dey warm you from inside,
" and you carry everything go give for another man who piking you carry I want to know",
Kallonsa ta tsaya yi " ka sake ni na wuce",
" naki I swear baze sakakaba sai tell me gaske",
Yafada harda sa hannu ya lasa ya daga sama a dole shi ya rantse,
" what is going on here Chris"
Muryar momy yaji ya saki Dije "madam she carry someone piking oo inside",
Yafada yana kokarin taba cikin dije tsawa momy ta daka mishi yayi sauri ya janye,
Nan tayi ta surfeshi da fada daga bisani kuma suka shiga gida da Dije da alama Dije zata amsa tambayoyi.
(Nima Mimsqueen I want to who give her belle oooo who dey my back?)." mom ankirani daga hospital kan batun jikin dady ance yaji ciwo sosai idan ya farfado yayi ta kiran sunanmu especially maryam momynsu Aaliyah",
" uhm ko bacin duk mugayen aikin da ya aika ta",
Tafada cike da bacin rae da damuwa kan abunda mijin nata yake aikatawa mutane,
" haba momy tunfa dakika je sau daya keda ummi baku koma ba",
" mai zamu yi masa kuma bacin shiba mutumin kirki bane",
" amma mo.....",
" dakata Aayan gaskiya har kunyar fita nake a garin nan bare naje har hospital dubashi,
" kai mahaifinka ne kacigaba da zuwa amma ni koyaushe naje banjin dadi ga police tare dashi koyaushe I can't",
Girgiza kai yayi yana mamakin shikansa halin mahaifin nasa,
" amma yaushe zamu gidansu Aaliyah din",
" I think kabari komai ya lafa tukunna muje mubasu hakuri kuma kaga ankirani cewan,
"Aisar na dauke da juna biyu",
"What!!!",
Ita kanta momynsa saida ta kalleshi " what do you expect" shiru yayi baice komai ba.Wayarsa ce tayi ringing ganin Faruk ne yasa yaji dadi " atleast zai tayani rarrashin momcy",
Yafada a ransa kafin ya daga wayar da sauri,
" Faruk inakashiga kwana biyu",
Shiru yayi yana saurarshi " eh ka shigo Tana nan",
" Aa Dana ne Yau kwana biyu ko yayi tafiya ne dan ba labarin shi tun faruwar wannan abun",
" I think so nima nayi ta kira bansa munshi",
" amma ko bai kyauta zan mai fada baa tafiya shiru haka kaima meyasa kayi shiru inba lafiya ne bafa",
Gyara zama Aayan yayi " walh mom kaina yayi zafi ne kinsan",
" salamu Alaikum",
Sallamar Faruk ne ya katse su harya zauna cike da fara'a akan fuskarshi " shigo mana",
Yafada su duka suka maida idonsu kan kofa shigowar Alina ta bala'in girgiza Aayan da sauri ya tashi,
" Alina!"
Yafada da karfi momy kuwa binshi take da kallo baki bude,
" dama wannan ita ce Alinar da akace dadynku yayi kidnapping har ance ta mutu",
Momy tafada tana mamaki Aayan karasawa yayi inda take yana binta da kallo,
Fuskarsa cike da hawaye " I am very sorry Alina walh bansan plans din dadyna a kanki ba",
Murmushi tayi tare da matsawa dan kusa da Faruk ta zauna,
" bakomai Aayan ba Wanda yasan meyake faruwa cikinmu sai Faruk Wanda shiya ceci rayuwata".Nan Faruk ya zayyane masu duk abubuwan da suka faru harda dalilinda yasa Dadyn Aayan ya kawoshi gidan,
Momy taji mamaki sosai Aayan kuwa sai kallon Alina yake,
Wacce ke kallon Faruk da duk motsin sa sosai wani irin kishi ke shigarsa sai dai yasan ya makaro,
" Faruk kana nufin Aaliyah nada twins sister duk tsawon shekarun nan",
Murmushi Faruk yayi " eh momy dan Yau ma muka yi wadan da suka rike ta kauye zasu z...",
Ringing din wayarshi ce ta katse shi dauka yayi,
" kun iso to kujirani nan Tasha yanzu Ina nan tafe",
Kallon momy yayi tare da kokarin tashi " momy sun ma iso zanje nakaisu gidansu Aaliyah",
" ae inaga mutafi duka saboda nima inaso dama naga maryam din",
Tashi sukai su duka inda Faruk na fita Alina tabi shi da sauri,
Aayan baigane inda suka dosa ba sam haka koda suka fito tare yagansu a mota suna hira,
Kallonta yayi ya dauke kai yayinda ita kuma take ganin kamar Faruk zai iya fushi da ita saboda Aayan din,
Shiyasa duk ta matsu subar gidan saboda abubuwa da sukai a dakin Faruk din da Aayan,
Wasu ma yana sane gabanshi suke yi sosai duk taji hankalinta bai kwanta ba dashi.Sai mun hadu a next page in Allah yakaimu👏

YOU ARE READING
KOREN MACIJI
General FictionA story about twins sisters who got separated during birth but later got reunited in strange way.