Chapter 26

388 28 0
                                        



" Haba! Haba!! Dae yanzu ni zaka ci Amana usman Muna can Muna plan nida kai,
" Ashe a gefe kai akwai abunda kake shiryawa kaida dan ma kuma gashi nan yayi nasarar bata mata rayuwa",
Dady Wanda baisan me ake ba tsayawa yayi yana kallon alh.sanin,
" wae duk me ya kawo wannan maganganun",
Nan Alh.sani ya zayyane mishi abunda yasani kan batun Aisar da Aayan,
Jawo wayarsa yayi dady ya shiga kiran Aayan a waya amma shiru Aayan bai dauka ba tashi yayi yafara kaiwa da komowa a office din nashi,
Shiru Alh.sani yayi yana binsa da kallo dan duk sanda abokin nasa ke cikin bacin rae haka yake,
Knocking din da suka jine yasa dady tsayawa " yes come in",
Yafada tare da kallon kofar dan ganin me shigowa Aayan ne ya shigo duk jikinsa a sanyaye,
" ke! Yanzu abun kunyar da zaka dauko mun kenan a cikin garin nan karasa matan da zaka bi sai yar sani",
Dady Yafada tare da tashi cike da fada kamar zai cinye Aayan danye,
" ae kabar wannan zancen kawae kai zauna nan"
Alh.Sani Yafada yana nuna mishi kujera dady ko sai ajiyar zuciya yake tsabar bacin rae,
" inaga usman abunda yafaru ya riga yafaru yanzu kawae zancen aure yakamata ayi".

Da sauri dady ya dago yana kallon Aminin nasa,
" Auren wa"
Cike da mamaki Alh.usman ya kalleshi " bangane tambayar taka ba ta auren wa",
Shikansa Aayan tambayar Dadynsu ta bashi mamaki matuka,
" kace zancen aure shine nake tambaya nawa"
Dakewa dady yayi kai kace kamar ba abunda yake faruwa ko baisan abunda ke faruwa bama,
" to bara namaka dallah2 auren Aayan da Aisar",
" wa kace" dady ya kuma tambaya,
" Abunda kaji nace mana dama anyi tuwona mai nane ae",
Alh.usman Yafada yana kakalo murmushi ganin Aminin nasa na kokarin juya mai baya,
" Alh.Sani kaga tsakaninmu babu boye2 a gaskiya bazan iya yarda Dana ya aura yarka ba sam",
Cike da mamaki Alh.Sani yatashi yana kallon Aminin nasa,
" meyasa zaka ce haka bayan nasan koda ba raina kai me kula da iyalina ne amma yanzu,
" saboda ansama yar matsala da laifin danka ne kakeson ka juya min baya iye, yakarasa cike da takaici,
" surutunka bazai sa na amince da zancen auren nan ba kabari zanba da aurenta ga daya daga cikin ma'aikatanmu amma badai Aayan ba",
Cikin daga murya Alh.sani ya nuna Dadynsu Aayan,
" ba zai taba yuwuwa bafa walh tallahi sai anyi auren nan dan zan iya komai naga na kwatar mata 'yan ci karka manta nine sani fa".

Nan suka cigaba da musayar yawu kan zancen inda Alh.sani ya fita cike da bacin rae,
" Dady meyasa bazaka yarda na aure ta ba",
"Kai! Rufe mun baki sakaran banza kawai nazata kana da wayoo amma ashe wayon ka da wayewArka ta banza ce,
" taya zaka rasa wacce zaka so sai yar sani bayan kasan meke tsakaninmu yasan komai namu",
" amma dady ae amini....."
" maza rufe mun baki maza katashi ka ficemun da gani karka kuskura nasama labarin ka da yar sani",
Jiki a sanyaye Aayan ya tashi yabar office din,
Dady ne keta kaiwa da komowa damuwarsa kar sani ya tona mai asiri dole yasan abun yi dashi,
Wayarsa ce tayi ringing " hello" abunda Yafada kenan yana saurar abunda ake fada mai,
" What! Can't you do your job properly search for them right now I want them all found before tomorrow else",
Kashe wayar yayi tare da dukan desk din " damn it",
" Sani zai iya komai yes"
Yafada tare da daga wayarsa zai fara dialing sai kuma ya karkada Kansa " no bari nabada dan time",
Yafada tare da fita daga office din shima.

" Akwai matsala fa"
Cike da mamaki su ukun suka kalleshi " what is the problem",
Momy ta tambaya Faruk dake duba phone dinshi,
" wayar Dana gama daga hospital ne ance anata searching dinmu wasu mutane so i think Hajiya ki koma gida saboda suspicious zasu iya tunanin da wani abu",
" Hakane I think Faruk is right momy kinsan zasu iya komai amma yanzu suka ganki gida da Aaliyah zasu dan hakura,
" inyaso muda Asiya we will countinue to stay away for a while har sai jikin Aaliyah yadan warware",
Cike da kaunarsu da taimakon da suke mata mom ke kallonsu rungume Asiya da Alina tayi,
" nagode sosai yanzu zamu koma gida and zanyi report ma commissioner dan asamun tsoro agidan,
" take care ku kiyaye dan Allah",
Nan sukai sallama inda akafito da granny da Aaliyah suka tafi batare da sunga Asiya ba,
Bayan suntafi ne Alina suna shirin tafiya call din boss ya shigo wayar Faruk,
" kuje i kawae zanzo I have work to do" badan Alina taso ba ta rabu da Faruk yana answer call din,
Yace " I will be there right now" ya kashe gaba daya yaji hankalinsa ya tashi.

Haarun ne daddaure a dakin yayi kuka ya gaji kwance yake da alama baida lafiya sosai,
Duk ya rame ya yamutse turo kofar da akayi yasa ya tashi zaune,
" Hahahahaha malam haarun kenan"
Muryar boss yaji Wanda tun randa aka daure shi bai kuma jiba,
Kunna wutar dakin akayi boss ya karaso amma Sam yasa marks haarun baya iya ganinsa,
" kazata zaka bata mun plans inbar ka katafi batare da na dau mataki kanka ba,
" kasan mutane nawa na yaudara saboda na sama wannan dukiyar har kisa nayi dan samunshi",
" kayiwa Allah boss kabarni natafi walh bawanda zai San komai nayi maka alkawari",
" hahahahahaha Alkawari fa kace nima najima ina ma mutane wannan alkawarin amma bancika ba",
Shigowar yaron boss dinne ya katse su " Faruk is here"
" let him in"
Tashi boss yayi sanda Faruk ya shigo " welcome Faruk "
Boss Yafada yana tafa hannayensa " Ina Alina?",
Tambayar tazo ma Faruk a bazata sosai yaji tsoro ya kamashi kardai boss yasan meyayi,
" oh no na manta bazaka San inda Alina take shhhhhh",
Yafada yana dafa kafadar Faruk din yana dariya,
Kusan da Yau yayi dashi yasa Faruk yafara tunanin kamar yasan voice din nashi,
Faruk yafara tunanin inda yataba Jin voice din,
" kasan waye wannan"
Yafada yana nuna mishi haarun girgiza kai Faruk yayi,
" kaga condition dinshi "
" daga kai yayi yakara kallon haarun da duk ya rage yayi baki.

" wannnan kadan kenan daga cikin hukuncin da zanyi ma duk Wanda yayi betraying dina",
Shiru yayi na wasu lokuta kafin ya kalla Faruk,
" Kasan Alhaji sani"
" yes boss"
" inaso Yau tazama ranarsa ta karshe a duniya and I want it to be done right now",
Mamaki ne yakama Faruk meyasa boss keson kashe Alh.sani bayan kusan mugun aikinsu da abunda sukeso su ukun dayane,
And meyasa baice akashe dady Aayan ba,
" you can go now dalilin kiran kenan and make no mostakes",
" yes boss"
Faruk Yafada yafita yana kallon haarun Wanda Asiya ta basu labari tabbas Hakan ne hukuncinsa sai dai,
sosai yake tausayin shi barin yadda yake ta rokon ya taimakeshi sosai yakara,
Jin tsanar boss yana fita boss yacire marks dinshi,
Haarun na kallonshi cike da mamaki sai yau yataba ganin real face dinshi " kasan me kayi Wanda yafi batamin rae kuwa",
Girgiza kai haarun yayi " Ina nan cikin gidan nan kasa 'Yata kuka nakira nabaka shawara a tunanina zaka zabi aurenta yadda kai nuna kana sonta,
" amma saika aikata akasin haka Aisya jininace yar yar uwatace tilo a fadin duniyar nan,
" muka dai iyayenmu suka Haifa suka bari a a doron kasa matsala ta na fifita son arziki da son duniya a kanta amma hakan bayana nufin na tsane ta bane Sam ko daya",
Haarun kuka ya shiga yi yana rokonsa daya yayi hakuri baisan yarsa bace San baisan alakarsu ba da bazai yiba.......

Ayi akara hakuri da short page masoya green snake Ina godiya fa sosai da comments dinku...especially Rukayya Wamu my kanwa😘

KOREN MACIJIOnde histórias criam vida. Descubra agora