Chapter 31

1K 50 7
                                        



Da sauri suka isa inda sukaji ihun kwance suka tadda Dije Tana juyi a kasa,
Idannunta na kakkafewa " Hajiya she drank all that rat poison o",
Sai a lokacin momy ta lura da kolbar dake hannunshi da sauri tasa aka kinkime Dije sai hospital,
Ba bata lokaci doctors sukai kanta dan ceto rayuwarta bleeding take sosai sosai suka shiga tashin hankali,
Inda su granny da 'dasu umman Asiya ke gida,
Hatta Aaliyah sosai hankalinta ya tashi sun jima kusan tsawon 2hrs doctor ya fito,
"Doctor ya jikin nata"
"Jiki da sauki thank god kunkawota akan lokaci,
" amma meyasa tayi attempting kashe kanta bayan she is pregnant and I am sorry to say we lost the baby",
Momy ba damuwar ta bane wannan damuwar ta lafiyar Dije din kanta cikin ikon,
Allah doctor ya tabbatar mata da lafiyar ta,
Tasha kuka sosai koda tasama tadawo hayyacinta inda tayi ta rokar yafiyar momy,
Fada sosai momy tayi mata kwananta biyar aka sallamota ta cigaba da aikinta sosai,
Momy haka tayi ta jansu umma ajiki har saida sukai sati biyu gidan kafin suka tafi,
Sosai suka sama Alkhairai agun momyn sunji dadi kwarae da gaske.

" Uhm Faruk kamar wasa gashi tare zamuyi angwancin juna",
Dariya sosai Faruk yayi " ai hakan yana da kyau",
" amma Faruk inajin Anya zan iya rayuwar Aure da Aisar kuwa bayan kasan Aaliyah ce a raina",
Tausayi sosai yaba Faruk hakan yasa ya zauna yabar gyaran kayan da yake yadaura hannunsa kan kafadar Aayan,
" Aayan inaso kasa a ranka haka Allah yaso ka kuma yita yin addu'a",
Murmushi Aayan din yayi " Ameen dan uwa Allah yasa hakan shi yafi Alkairi ka karbo mana kayan",
" Ameen why not bari na ciro maka",
Nan suka cigaba da shirye2 kan kayan da zasu yi fitar biki dashi cikin Jin dadi sai dai,
Kowa yasan Aayan na cikin damuwa barin rashin mahaifin sa da yayi dan tun randa,
Ya biyosu gidansu Asiya da washe gari da safe akace ya rataye kanshi,
Sosai abun ya daga masu hankali bama kamar momy hakan yasa suka gwmace ayi auren ko zai rage tashin hankali.

"Uhm nafi kowa daukin wannan auren walh",
Aaliyah tafada Ana mata lalle murmushi Alina tayi,
" naga alama kam kina jinta ko Asiya",
Murmushi Asiya tayi " barta Allah yakaimu nata hmm zamu baki mamaki yarinya",
" ke waye yarinyar meyasa baki da respect kowa yasan nice babba",
" to uwar son girma saikiyi tayi dadinta dai marabar baiwuce 1 to 2mins ba",
" eh andai ji koma mins nawane nagirme ki",
Dariya Alina tayi tana kallonsu ana gyaran dilka,
" oh ho yaushe zaku girma ne 'yan biyu a haka ma wae baku girma tare ba oh kuyita fada",
Momyn Alina tafada sanda tafito tsakar gidan saboda hayaniyar su,
" momy laifin Asiya ne fa bata da respect",
Girgiza kai momy tayi " ah ah abun dama bai wuce kan son girma irin naki Aaliyah dama can haka kuke kedae Alina yanzu andawo kan Asiya",
Dukansu tsakar gidan Dariya suka kwashe dashi,
Banda Aaliyah dake ta hura hanci a dole ita fa antabo ta.

Bayan biki
Zaune take tsakiyar gadon amma sosai gabanta yake faduwa,
Saboda tuna cewa Yau darene mai matukar muhimmanci a rayuwarta amma sai dai yabada budurcinta a waje nan,
Damuwa da fargaba da kuma Dana sani suka shige ta,
Koda Faruk ya dawo daga raka abokan nasa murda kofar dakin yayi amma yajita gam,
Ganin hakan yasa ya fahimci me take tsoro ya mata sallama ta waje dakyar ta iya amsa shi,
Side dinsa ya wuce,
Kusan taba dare tayi tana tuna abunda ta aikata sosai Tasha kuka daga karshe alwala tayi,
Ta zauna taci gaba da Azkar da godiya ga Allah da ya bata namiji Wanda yake matukar sonta,
Duk da yasan ba wani abu zai samu gunta ba yayi shahada ya aureta yana sane da abunda tayi a baya,
Sai da sukai kusan 2weeks a haka da lallashi ya samu ta yarda dashi suka raya sunnah,
Tun daga wannan ranar Alina tabar fargabar komai ta kama mijin ta ga dukiya gado su,
Ga Khadijah na matukar son Alina da nuna kulawarta sometimes har baka banbance yar uwar waye ita cikin su haka rayuwarsu ta cigaba.

Bangaren Aayan da Aisar suma ba matsala a zaman nasu,
Dan ko wanne yana kokarin faranta ma dan uwansa,
Inka gansu bazaka ce su bane a da Aisar ta nustu sosai dake dama Tana da zurfin ilmin addini kawai  amfani dashine Allah bai bata iko ba,
Sun yi zamansu ba'a Jin kansu momy najin dadin surukar tata duk da bangaren,
Nafeesat Sam bata son auren dan gani take Dadynsu Aayan yayi silar mahaifin ta,
Cikin ikon Allah itama ta sama miji tayi aure a wannan shekarar.

5 YEARS LATER

Yan mata ne biyu kyawawa masu kama iri daya,
Bakin motar sun bude murfin ta layin shiru motoci basu cika gilmawa ba saboda yanayin area din ta masu kudice sosai,
Wato G.R.A  ne babba manyan gidajene aciki sosai,
" Asiya!",
"Aaliyah!",
Juyawa sukai a tare kowa baison kallon dan uwanshi,
" oya go and get us some help infact gida da nan kusa ne kiyi kwana kikira wani agida",
Murmushi Asiya tayi " walh ba inda zanje ke koyaushe in abu yatashi ke bazakiyi ba saini",
" that's saboda I am your elder sister",
" oh really su elder sister my foot",
Nan suka fara hayaniya kamar cat and mouse,
Wata dankareriyar mota ce tazo ta wuce su har tayi nisa ta jawo da baya su Sam basu lura ba,
" What! Dama yan mata kyawawa kamar ku suna fada gashi kamar you guys are twins",
"Yeeees we are!",
Suka amsa mishi a tare da Juyowa gabanshi,
Rufe idonsa yayi yana jira sufara mai jaraba,
Ganin sa yasa Asiya bude baki ta kura masa ido sosai take kallonsa yayinda Aaliyah mamakin yar uwar ta ya isheta hakan,
Yasa taje gabanta gab da ita " hye snipe out of it malama",
Jin hakan yasa ya bude idon "Abdulhamid!"
Tafada tana rufe bakinta cike da murna da dariyar Jin dadi,
" hamid right",
Girgiza kai yayi yana kallonta Sam bai gane ta ba saboda black sunglasses dake makale eyes dinsu.

Ganin haka yasa ta cire still tsayawa yayi yana kallonta,
" it's me Asiya",
Sake zaro ido yayi yana kallonta wani irin dadine ya rufe hamid kamar ya rungumota,
" Asiya kece dama inata neman ki inakuka shiga Aisha ma bankara ganinta ba",
Nan suka fara hira Aaliyah wani mugun takaici ne ya isheta,
" wait wait ga dukkan alamu kunsan juna which is good but in bazaku damu ba,
" help me with your battery saboda I have work waiting for me ita maybe tafasa zuwa lectures din ku zauna for all I care",
Asiya hararta take tunda tafara magana karshe dai hakan ce ta kasance din inda dole yatayar mata ta tafi shikuma gidansu takai shi,
Inda yaci sa'a mom na gida suka gaggaisa,
Cikin ikon Allah ya turo dan baiyi aure ba dama inda Ana shirye2 din bikinsu momynsu Aayan,
Suka zo da batun inda sai a lokacin sukaji labarin rasuwar Aisar gun haihuwa daga ita har jaririn ba Wanda ya rayu,
Dakyar momynsu da ita kanta Aaliyah ta yarda inda aka saka bikin twins din rana guda,
Su umma ma tuni suka dawo nan cikin garin kaduna inda momy ta sai masu katon gida,
Kai kaga yan gidan kasan Masha Allah baba ma yasama jari ya ummi kuwa ji take da Asiya kamar kwai,
Cikin ikon Allah ya Aisha takoma gun haarun ya kintsu sosai inda ya sai masu karamun gida nan kaduna saboda aikinshi.

Tsayawa baku labarin daren su Aaliyah da Aayan bata wane nasan kunsan ya hadu komai yaji,
Romance love dama gogan namu Aayan ba baya ba,
Ya kuma sama yadda baitaba tsamanni ba dan gal take yaji dadi sosai inda yayi ta sa mata Albarka,
Gunsu Asiya ma baa magana ranar hamid yayi aiki sosai da sosai gashi yaro da kudi dama,
Ga hankali ga ilmi Masha Allah kowa su Alina da Faruk anzama iyaye dan yaransu biyu,
Nabil da Nabila kyawawa gwanin sha'awa,
Su Khadijah ma tuni ta sama wani handsome dinta tayi aurenta.

Wait! Wait!! Ina hansa'u Mimsqueen da inna........" suma su shiga picture dan tuni Faruk ya fito dasu gari hansa'u anji kudi tacika burinta na auran me kudi.....amma nan leka naga rayuwarsu ba kunsan ance inda kwadayi da........Tammat👏

            End........sai mun hadu a sabon story dina Wanda yana nan tafe bada jimawa ba😍😍😍 nagode fans dina na WhatsApp da comments da kulawarku gareni👍

KOREN MACIJIDonde viven las historias. Descúbrelo ahora