Chapter 2

2.4K 134 2
                                    

MU ZUBA MUGANI👣💃
2
Da karfi ta bugo kofan Dakin inna tana ta haki..
Gyale inna ta jawo daga kan kyaure tanacewa to Allah yasa lapia bawani uban kikaje kika kar tsokanowaba..

Inna na fita kofar gida ta ga dan tani da Audu tsaye bakin kofa har kasa suka tsogunna suka gaidata cikeda Girma mamawa, amsa sutayi tana neman Karin bayani da daga kallo daya tamusu tasan ba lapia ba..
Dan tani ne yafara ma inna bayanin abunda ke faruwa, salami inna tafara dan dama tana ganin bazla tashigo gidan nan a hargitse tasan ba Kalau ba..
Hakuri tashiga basu tare da musu alkawarin hakan bazai kara faruwaba..

Bayan ta sallami su dan tani gidan tashiga tana kwalama ta kira bazla bazla fito dan kaniyanki..
Bayan door din kitchen taje ta dauko wata yar sandanta wadda dama da ita take yawan bugunta idan aka Kawo mata karanta, koda kuwa bata same taba haka zasuyita yar tsere a tsakar gidan,,
Yau dinma kuwa haka ta faru bazla najinta tafito da gudu suka fara tsagaye inna nace cewa aradu yau sai naci kaniyar ki inbanda isakanci dan tani saankine da zaki na masa rashin kunya!!

Yunkurin kamo ta take itakuma tana ta ihu tanacewa wlh inna bani na tsokanesa bafa daga kwai munyi dambe da tine budurwarsa shikenan fa yafara zagin ubana nikuwa yau namasa bar baden Allah tine,

Rike baki inna tayi tace yanzu ko kunya bakiji bakikecemun wai dambe kike dawata dan ya zageki kuma kiyi masa barbadan yaji.. To nima nazaga naci ubanki  muhammadu nima saikimun barbadan Allah tsine din shegiya mai kama da aljannu..

Zinburo baki Bazla tayi ita a dole an zagi babanta yawani sha kunu tace inna kinsan dai muhammadun nan da kike zagi ya rasu dai ko,
Inna ce ta chafke tace inajin kinmanta ni na Haifa Muhammadun ko lokacin da nasamu cikinsa ina kike duk abubuwan da sukafaru kina ina dan ubanki! Saikuma tafara sharar kwalla irin na tsofaffi tace Allah sarki muhammadu Yayi mutuwar kuruciya Allah kajikansa ka gafartamasa.wata majina takara ja tace haka nan baidade da tafiya ba zainabu ta bisa, zainabu baiwar Allah yarinya mai hakuri mai biyayya da halinta kika Debo da kinji dadi bata da hayaniya ko kadan..
Ganin tana ta sharar kwalla yasaka bazla ta zagayo dan inna sosai tasan weak point dinta sunafara haka sai tafara maganan iyayentan da bata wani Wayon saninsu ba sai a hoto innan ta kwai ke gabansa yanzun shiyasa batasan baccin ranta,,,,

Kanta ta dora kan kafadan inna tace inna ni banasan kukan nan Naki wlh, daga yau bazan kara dauko miki magana ba duk Wanda kikagani cikin gidan to yaseen tsokanata yayi! Jawota inna tayi jikinta tace kwai kice mun bazaki daina ba.
Dariya bazla tasa inda inna ke tayata..

Kar
Kacewa tayi inna nikam kibani labarin babana manakince sai na Girma yanzu kinga ai nayi Wayon dayakamata nasan waceceni ko..
Dan dariya inna tayi dan idan bazla na zubo zance sai ka rantse wata babbar macence!,
To aunty bazla sunan da take kiranta kenan idan zatatsokaneta!!

A gajarce tace nidai mutuniyar yobe ce cikin garin potiskum iyayena mu biyu Allah yabasu dagani tafarko sai yadikun ki wadda itace tabiyuna,,
Nahadu da baffanki a wani taro na dangi damuke yawanyi duk shekaraka inda shi mahaifin baffanki yakasance dan aminin mahaifinane shakuwarsu har takai bazakice ba yanuwa bane inba fada miki aikai ba..
Su su baffanki kenan mutanen gayane da ke nan cikin garin kano!
Tafiya dai tayi tafiya inda baffanki yanuna yana so na kuma na amince masa Dari baisa Dari saboda tunda nagansa naji ya kwanta mun!

Wata dariya bazla ta saki tace wayyo inna wai ashe Kema kinsa soyayya saboda tsaban dariya harda rike ciki!
Itama inna dariyan tayi tace jaaira wayace maki azamaninku ne kawai da soyayya tamu ai tafi tako aminci ma...
"Naji nikam cigaba da bani labarin cewan bazla dan batasan taja musun yanzu labarin zai watse..
Goronta gutsora tacigaba "!

So bayan iyayenmu sunsan da soyyan mu sai suka shiga gaba akasaka ranaku kalilin..
So bayan auren mu ne ya Kawo ni nan cikin kademi cikin gaya sabida nan yake kasuwancinsa,
Cikin zaman lapia da kaunar juna muke zaune har Allah ya azurtamu da yaro kyakyawan gaske inda yaci suna muhammadu wato babanki kenan sosai baffanki ke kyaunansa dan haka yana da shekara 7 yafara zuwa kasuwa dashi yana nuna masa wasu abubuwan dan da yarinyansa sai ya fi daukewa..
Anahaka dai Allah ya kara azurtamu dayaro namiji Wanda yaci suna Abubakar kawun ki da ke cikin binni kenan,,
To tundaga shi sai haihuwant ya tsaya kaman dai gado, yarda Nike gun iyayena!!

Haka dai rayuwa tacigaba da tafiya inda yaranmu ke zaune cikin so da kaunar juna dan sosai jininsu ya hadu to kinsan dai shi rai da dadi ba dadi dole sai an tafi abbanki nada shekara 17 Allah yama baffanki rasuwa inda bakaramin tashin hankali mukashiga! To bayan rasuwan kinsan kowa dai dukiya dukiya mutum na tafiya to nidai da yarana bamusaka abun aka ba inda Allah ya taimaka kuwa yan uwan baffankin bamasu san abun wani bane sai suka yanke shawaran kancewa abar muhammadu yaciga ba da tafiyar da abubuwan harkan kasuwa!
Haka kuwa akai dayake mutum ne mai kwazo haka yayi ta tafiyar da abubuwan daidai da yarda Allah!
So haka dai muhammadu yanema da yasaka Abubakar a makarantar boko dan Yasamu abunda shi bazai iyasamuba! Bayan Abubakar yagama primary ne wadda duk muhammadu ke raba hankalinsa akai yana hanyar kaisa cikin gari dan makaranta! To karshe dai da zaije aji daya a secondary sai mukatsaya
Akan shawaran asama masa makarantan kwana sabida jigilan kaisa shima muhammadun Yasamu saukin kulada kasuwancinsa inda sosai Allah yasaka masa hannu cikinsa saboda haka Yasamu tarin makiya abokan kasuwanci inda sau dayawa zauna Kawo mun korafin to kullum cikin basa shawarar yarike Allah nake!

Sosai na damu da rashin auren Muhammadu idan na fiya takurawa ma sai yace shidai yabani wuka da nama amma na bari sai Abubakar yabama makarantar secondary da kyardai ya yarda nasamo masa mata a potiskum Lokacin Abubakar na aji na byin karshe a secondary.

Zainabu yar kanwatace inda sosai nayaba da nutsuwanta da Hankalinta kuma wani hadin Allah tana haduwa da muhammadu suka dai daita kansu to bayan auren su saida sukayi shekara wajen uku Allah bai azurtasu da yaro ko yarinya ba hanakarya dai tayi bari saudaya !
To sai suka saka hakuri da dan gana dan samu da rashi duk na Allah ne!

Tafi tafi dai shekaru na ja shekaru biyar kenan da auren maihaifanki amma har lokacin dai shiru. Gulmace gulmace dai sai yinsu ake amma suka kulle kunnuwansu..

To bangaren Abubakar kuwa ya gama karatunsa na jamiaa inda Yasamu aikin lawya sabida haka sai yakoma cikin birni da zama inda nan aikinsan ya kafo duk da nida dan uwansa ba haka muka so ba amma bayarda muka iya dole muka kyalesa ya bi rayuwansa yacika nasa burin..
Bayan shekara daya da aikinsa Yasamu mata nan cikin garin yakawo ta nan gida duk da bawani kwanta mun tayi ba amma ganin yadda yanuna yanasanta ba yarda mukaiya nida dan uwansa illa muka sawa abun Albarka

Bayan shekara daya da auren Abubakar da hafsa Allah yabasu da namiji mai kyawun gaske inda yaci sunan baffanki wato mukhtar to kinsan iyayin sunan na boko mai makwan subarsa da sunan sa muntari amma ina saida suka samo wani suka laka masa acewarsu wai alkunya suke karsufada sunan baffanki sai suke kiransa da HAYSAM (lion)
Aikuwa yana nan dan jakar uba yaci sunan nasa zaki..
Dan dariya bazla tayi tace amma inna ya akai basa zuwa sai kuma ta yaba baki tace kodayake suzo su mun uban me ma..
Inna ta ni alabarin nan har yanzu banji inda aka haife Nibafa..
Dariya inna tayi tace ai kya bi abun asannu ko..
Wasa was Saida iyayenki suka shekara 18 da aure kanasuka haifeki Lokacin da suka san da cikin ki bakaramin murna sukayi ba kaman su maida ki ciki..
Dan share kwalla inna tayi tace Allah sarki zainabu ga dai ya da take ta fatan Allah ya bata kuma yabata amma bai Tsara zata rayu da ita ba dan Kinada kwana 4 aduniya Allah ya dauka ranta sabida zubar da jini da tayi Wanda ba afarga ba sai da aka makara.. To sai aka maida maki sunan ta inda kawun ki Abubakar ne yasaka miki sai yanema da anace miki BAZLA maana kyauta (reward /generous) to shima dai muhammadu zainabu batayi wani kyakyawan shekara ba yabita Allah yajikansu bayin Allah masu hakuri takarasa tana kuka..
Shiru tayi kuma sai taji wani shirun na  bazla tana Leka ta taga tana ta Sharan kwalla. Mikiwatayi tace ni dai inna Kibar bani labarin nan haka shi Kawu Abubakar din ainamanta rabun da yazo nan din da zancen ganin mu bare kasan wasu yayansa..

Umm cewan inna aiki ne yamasa yawa.. Mikewa bazla tayi tace dama ai bazakiga laipin dankiba nikam kinga naje gidan mai tibani dama tace yau naje zata ban gyaran na goma.. Da tsalanta ta fita agidan....

سْــــــــــــــــمِ اللَّهِ الرَّحْمَ الرَّحِيْمِ
_May Allah give us a life full of peace where sadness has no place._
_A truthful life, where gratitude fills our heart with Imaan & Taqwa._
_May He uplift our value, forgive our past & grant us & our loved ones everlasting victory Fid-duniya Wal-Akhirat & make Jannatul Firdaus be our final abode...Ameen Thumma Ameen. Eid Mabrook to the Muslims umma around the world may we witness more more more more & moreeeeeeee eid

Vote, share, comment and follow
Chuchujay

MU ZUBA MUGANI(completed) Where stories live. Discover now