MUZu BAMUGANI 👣💃
Ranan tafiya suk tsayar inda yakasance ranan friday saboda inna tace sai taje tayi bankwana da yanuwa da aminan arziki kuma sai sun hada komai a tsanake.
Daddy ne ma yace ba sai ta kwasa duka abubuwanba saboda wannan din zai zama kaman family house din sune dan koda suntafi ba barin garin sukai ba zasuma zuwa akai akai so aransa yagama planning renovating gidan..Yau ya kasance Thursday saura kwana daya kenan Tafiyan nasu so da wuri inna ta tashi ta shirya tareda cewa daddy shima yashirya dan zata shiga kauyikan Kere da Siyasiya sabida akwai yanuwa wayanda baisaniba dan haka yakamata yabita yaje yagansu suganshi, to yace mata dan a yanzu babu abunda yakeso kaman yasakata farinciki mara adadi.
Koda yacema haysam ya shirya suje tare aa yace sabida yanada haduwa da wani abokin karatunsa cikin gaya kuma sunyi dashi yau dinne zasu hadu, tabe baki inna tayi tace chan ta matsewa mutum dama ai bani na gayyacekaba chan gasu gada,,
Daria haysam yayi yace tsohowarnan wlh kina vani Dariya yanzu Mene na shiga tsakanin da da babansa ..
Gaba inna tayi tace eh ai baban dan ni na durosa dubiya kuma da ban kawosaba da yanzu ba ai haifi wani dan banza ba..bayan Tafiyan su inna chan saiga bazla tashigo tana ta yana ta yan wakokinta as usual Ganin haysam da tayi zaune kan kujera yasaka tafara kwalama inna kira tana inna fito kiji wani bakin labari kinji wai mai mati mai kanti yace mun? Wai ni shegen kazamun mutumin nan yakeso baki kacako kacako duk goro wlh inna kamar nayi kuka.. Inna kina ina ne bakin kofar Dakin inna ta nufa dan shiga wani wawan tsawa haysam ya daka mata yace zo nan dan ubanki.
Bayataja tayi sokotana kallansa tace
Dan ubanakuma baki tarike tace lallai zakinan wlh kaci saar daddy kanin uban nawane da saina Makawankin babban bargo kar kaga anacemaka wani zaki wlh ko dajine ni yanzu zancikinka na haifo ka dan..WAF taji an buge mata baki dan kafun kace mene ya taso yazo har inda take juye juye yake har ya hango dan bulaliyan darbejiyan da ta shigo da shi daukan a yayi yafara hada mata jikinta tun tana zaginsa hartafara bas hakuri shikuwa gogan zuba mata kawai yake yanacewa"ke wato yar iska ko at wannan karamun age din naki kinisa mutane ko ni inkina ma wasu kika mun wlh sai na babballaki shegiya marar tarbiya..
Zanan bazla haysama yacigaba saida yaga tayi lis sanan yacikata ya zauna hannunsa rikeda duka hannunta biyu yace fara tsalin kwadi har sai nace ki tsaya. Ai ba wani musu bazla tafara wanan frog jump din dan wani Alhajin tsoron haysam ne taji ya dirar mata, frog jump take tayi ba tsayawa amma jikinta da kafafunta bakaramin ciwo suke mataba tanayi yanacewa "dangirman Allah zaki kayi hakuri,
Dariya ne takusa kwacema haysam Ganin yarda ta koma hancin nan duk majina amma ya dake yace ina ni Saan kine ba oya go ahead kicigana da kirana zaki anan zaki mutu kina frog jump dinnan,Jin haka da bazla tayi sai tace to dan Allah ya zaki kayi hakuri don a tunaninta ba zakin datake cemasa bane yake Ganin kaman ta rainasa a ganinta dan bata hadawa da yaya ne,, banza yamata harsaida taji wuya Zata kashe ta ne tace dan soyayyarka fa manzan Allah ya haysam kayi hakuri walh namaka alkawarin bani sake fitsara wlh idan na sake kayi yarda kaga dama dani yeee saita karafashe wa da wani mugun kuka..
Hade rai haysam yayi yace oya dawo nan yanuna mata kusa dashi,, da rarrafe ta karaso tana goge hawaye squat a nan yanuna kasa..
Kallonsa tatsaya yi dn ita inzai shekara yana cemata squat batasan menene ba, wani tsawa yabata yace baki jini bane..
Karaso watayi da rarrafe still tareda rushewa da wani kukan tace alquran ya haysam idan zaka kasheni bansan menene wani skuet ba danayi billahilazi bansani ba takarasa maganan tareda jan hancinta..Wani tausayinta tareda Dariya kuma yaji sun sauka masa amma sai ya dake dan yasan wannan yarinyan idan yace zai mata da sauki yanzo zata rainamishi wayau kuma.
Ok zauna sannan yace listen to me very Carefully inason abunan da zan fada miki yashiga cikin wanan dakikiyan kwakwalwan naki hannu yasa ya dongori Kannata..Wani irin majina bazla taja tace naji ya haysam amma wlh na daya nake ci a ajinmu wlh akwai abu a kwakwalwata da yawana ba da kikiyabace...
He was like what tf mamaki yarinyan ke basa amma kuma yakula cewa ita tsakaninta da Allah take maganan, Susan kasa yayi brushing da fingers dinsa yace oh God in frustration lallai yazama dole yasaitama yarinyan nan bakinta dan yasan definitely bazata zauna kalau da mom insaba dan yanasane da yarda mom insa ta tsanesu and yasan how ruthless mom insa take yanzu sai Tamata wani abun..
Ganin yayi shiru yana kallonta yasaka bazla tasha Jinin jikinta tace wlh ya haysam bada rashi. Kunya nafada ba gaskiya tace nafadamaka haka malamin mu yakoyamana yace "say the tru no matter how batter it will soun"
Haysam was like I'm dead kara mtsowa kusa da ita yayi yace later on xakice mun ke ba dadikiya bane ba meye wancan din kikafada dakikiya kawai kulada yayi yarda jikinta ke rawa sabida tsoro yasaka yace let me keep the story short kinga wanan abunda na miki wlh koda wasa naji kinfadama inna ko daddy wlh koda wasa oh God kinzama dead meat yarda muke wa criminals zanmiki sainasaka shocking a kwakwalwanki.
Da sauri tarike bakinta tace wlh ya haysam na tuba inkasan wanan ai mutuwa zan kuma wlh banaso na mutu sainazama likita.Kada kai yayi yace very good then sai kiyi behaving musamman idan mukaje kano tare dole ki iya bakin ki a gidanmu dan duk Wanda ya kawo mu. Karar kinmasa rshin kunya sai nayi maganinki...
Da sauri bazla tafara Kada kai tace ai ya haysam mu bama binku zamuyi gidan ku ba wlh mu ai ba inda zamuje nan ma ya ishe mu nida inna tace anan zamuyi tazama sai ina nagirma mijina da ke tasona zai zo ya daukeni, ni wlh banamasan gidanku takarasa maganan hawaye daya na bin daya..
Baki yasaka yana jin shirmentan yace uban wayace miki Kinada miji ita innar tace miki haka,
Cike da wata da yarinya ta daga kai tace e kuma yace idan na girma zaizo dan Allahkar kutafi damu bazama mubikuba.Mamakinsa ya shanye dan yasan maybe inna tafada mata hakan ne dan kartayi kule kulen maza dan yaga rashinjin bazla din yakai makura..
Hanyar daki yanuna mata tareda mikewa yace wuce kije ki gyara jikinkinda duk yabaci karnadawo gidan nan naganki haka da sauri ta kadamasa kai whilst shikuma yafita a gidan.....~>
Su inna basu tashi dawowaba sai dare koda suka dawo inna tasha mamaki dataga gidan fes dan batasaba barin bazla a gida ba kuma ta dawo tagnsa hakanan tsaf ba, yar inna yar inna kina ina ne cewan inna,, daga chan daki bazla tace inna ina daki kizo bazan iya fitowa ba to lapia cewan daddy da sauri inna takarasa Dakin, bazla naganin inna tafshe da wani fitinanna kuka tace inna kafata bazan iya tashiba, salati inna tafara tanacewa lapia? mayfaru? Ubanwane yamiki hakan tabakii akaiyi? Uban wane saiga hawaye a idon inna sharrDa sauri daddy yashigo Dakin yana tambaya lapia cike da hawaye inna tace wani tambadaden ne inajin ma fade yamata nashiga uku ni yarnan.
Salati daddy yashiga yi tareda karasawa yana dubata yana bazla fadamun mai yafaru kedawanene..
Cikin kkuka bazla tace daddy tsalan kwadi nayi kaji kafafunna kaman ba ajikina sai a sananne inna taji wani sanyi tace to uban wane ne yasaka ki tsallen kwadi.Ubanwanda ta tsokano shiyasakata, a tare daddy da inna sukajuya danganin wane....
Xoxo love yall
Vote, share, comment &follow
Chuchujay❤
YOU ARE READING
MU ZUBA MUGANI(completed)
RomanceLifehacks Romance Drunk in Love Challenges Lost Lust Hatred Regrets Ku dai biyoni I assure you'll like it insha Allah.....