MUZUBA MUGANI👣💕
14Zaune take a balcony ita kadai sai smiling take ta na ayyana abubuwa aranta, yau ya kasance sauran kwana biu kenan ta tafi Kd, so kasancewar akwai bashikan dabata gama biya ba a gidan shiyasa take so ta biya da gaggawa kafun ta wuce Kd, agogon hannunta ta kalla taga karfe 7:30 nasafe Wanda tasan lokacin shine dai dai lokacin da mai binta bashin zata fita school dan haka tun 6:30 ta tashi tagama shirya komai,.
Karan heels taji sunata dukan tiles din da zai sada ka da compound, Kara makalewa tayi sosai yarda bazata ja attention din mai tahowanba, Sabah ce sai wani yauki take tasaka wata baby blue fitted gown dinta wadda duk wani sura da Allah ya mata tagama showing yarda kasan a jikinta a ka dinka kayan,
Daga nesa idan ka hango ta kana kallan yarda fuskan ne ke ta mulka unban sheki sabida make up din datasha kaman wacce zataje party, dan ƙaramun veil tayi rolling tare da Dora shade a Saman ka,
Gashi ta saka wani uban heels mai shegen tsini duk da tsayin da Allah yabata bazaka taba ganinta ba tare da heels ba ko da aka halicceta ansaka aunty heels a goshinta ne oho cewan bazla!Kasancewar Sabah macece wadda indai tana tafiya hardly ne Kaga fuskan ta ba Akan wayanta ba, so as usual yanzun ma hankalinta nakan wayarta tana ta dane dane plus smiling kana kallan ta kasan cikin nishadi take amma me suddenly sai nishadin ya dauke sakamakon wani santsi dataji ya kwashe ta yayi Sama Sama da ita, lokaci daya karar faduwar wayarta dakuma karar ihunta sakamakon yarda taci kasa suka fito!!
Wata iriyar muguwar Dariya bazla dake labe tasaka tana nuna Sabah sakamakon yarda faduwan Nata ya kasance , fuskan nan kaman anzagi shege, da gudu ta yi cikin gida sakamakon muryan mom dataji tana sallallami!!
Da gudu mom ta karaso tana mai dago Sabah dake kukan wahala, kallan gaban Sabah mom tayi taci Karo da bawan ayaba, salati mom tasaka tace oh ni hasfa wanene kuma yaci ayaba ya'aje b'awan anan,
Cike da shesheka Sabah tace mom wlh bazla ce wlh bazan yarda ba yau sai naci ubanta sai kuma tasake fashewa dawani kukan,Sosai ran mom ya baci a hankali ta tallafo Sabah tace taso muje inga irin hukuncin da tsohowar can kuma zata dauka yau, riko ta mom tayi dan ta tallafa mata taji tafashe da wani kukan tare da riki Hannu tana cewa mom na karye na karye nashiga uku, cike da tashin hankali mom fita ta kira maigadi ya tallafa mata kana aka je dauko mai dauri!
Tafe mom take kaman zata fashe tana ayyana aranta yau sai ta ma bazla dukan tsiya acikin gidannan, ko knocking bata tsaya yiba ta banka cikin falon, rarraba ido tafara kozata ga wani gurin yarda tazo cike da masifan nan ta sauke sa kansa!
Sallama ta kwada kaman zata fasa ko ina ba kakkautawa,
Da Sauri inna tafito tana cewa lapia lapia mai yafaru, wani Abu yasamu Abubakar dinne,Wani kakkausan takaicine ya torake ma mom wuya wato sai Abu yafaru da Abubakar ne zatazo da gudunta tsaban munafurci,, ajiyan zuciya tayi tare da sassauta kanta dan in akai rashin saa ta iya zaginta, cike da karfin hali tace inna ina bazla Yau kibani ita Dan Allah na koya mata da'a yanzu ga Sabah chan a karye kuma ba aikin kowa bane inba na bazla ba!!
Yar Dariya inna tasaka kana tace haba Hafsa ina mai hankali zai dauka wannan zancen, naji tayaya bazla zata iya karya Sabah da girmanta!. Wani kololon takaici mom ta hadiye tace inna b'awan ayaba fa tasaka mata a hanya inma ba hakan bane Ai kinfi kowa sanin shedancin bazla ba sai an fada miki ba ''
Sakan baki inna tayi tace LA hafsatu ni kike gayama bazla shedaniya ce to bismillah ga dakinta chan shiga ki koya mata daa,
Bata jira cewan inna ba ta nufa kofan dakin bazla din, knob din ta Kama ta murda tajisa a kulle, batayi wata wata ba tafara knocking,
Bazla da tun shigowan mom take labe tana sauraransu, jin knocking din mom yasaka ta cikin Sauri ta cire kayan data saka ta dauko nighties tasaka gaban mirror taje ta Mayar da gashinta all messy kana ta dauko eye drop tasaka a ido tuni suka chanza yanayi!
Kallan door dinta da mom keta bugawa tayi sannan tayi murmushi tace Yau hajiya mom zakiga sharrin yan zamani,
Clip tasamu ta saka dai dai cikin ta kana ta nufa bakin door din ta bude tareda sakin wata banzar Hamma mai sauti!
YOU ARE READING
MU ZUBA MUGANI(completed)
RomanceLifehacks Romance Drunk in Love Challenges Lost Lust Hatred Regrets Ku dai biyoni I assure you'll like it insha Allah.....