MUZUBA MUGANI 👣💃
3
A makarantan special model gaya kuwa bazla tsugunne a kneels dinta tana sharar kwallah sabida yarda ranan ke gasata ita da abokiyar kirinyarta khadijan wadda duk wani rashin ji idan bazla zata aikatasa to da sa hannunta,,
Share tears din dake zuba mata tayi tace khadijan kinsan Allah billahilazi sai malamin english yaci ubansa bani zaiwa sharri gurin principal dinan mai shegen iyayiba ita kuma tasaka baba mai duka yadakeni ba to wlh daga baba mai dukan har malam umar din bazan kyalesu ba wlh sun tabo tsulin dodoKuma shi harisu Din dana sawa biro yazauna akai ina shi ya fara zagina yace mun mu ubana ko ubana sa'an wasan sa ne wlh nan gaba saina sakamasa kwalba ya zauna akai, kuma cikin makarantanan muzuba mugani dan wlh ko principal ce tashiga gona ta sai na fitar daita....
Share hawaye khadijan tayi tace wlh kibari kawai bazla Allah ko bada ban ina tsoran baffanmu kar yazo makarantan nanba wlh da an san an tabani..
Tabe baki bazla tayi tace chap nikuwa kinga inna tayi tayi tagani dan wlh indai kan gaskiya tace ban bari a shafan kashi...Sai bayan wajen 30 min principal maisuna Malama hafsa tayi kiransu office dinta, cire takalmansu sukayi sanan suka shiga suka tsugunna kaman mutanen kirki..
Fada tafara musu tace ku yanzu fisabilillahi abunda kuke a makarantar nan yana dacewa, gaku dai bawasu manya azo aganiva amma ku Adabi kowa. Musamman make bazla muhammad although duk ajinku ba mai kokarinki amma hakan bashi zai baku daman yin iskanci yarda kukeso ba
..
Dafe kanta tayi tace bansan maiyasa kukesan kusa mun damuwaba thank God saura week kurubuta common entrance dinku kuyi kuyi ma ko Allah ya rabani daku kuma wannan ne last warning dazan baku ku kiyayeni,
Door ta nuna musu tace ku bace mun da gani mutanen banza.
Da saurin su suka mike daya na gogar daya suka fita a office din wani harara bazla tabi office din dashi tafara kwaykwayan yarda PC din tayi "kufitar mun a office mutanen banza "
Tsaki tayi tace ko kuma kece mutuniyar banza ba.
Ita dai khadijan bata ce komai ba dan tafara karaya sabida tasan baffan ta najin wadan nan abubuwan da suke ta kade ..
Aji sukaje suka dauko jakunkunansu sanan suka fita a makarantan suka hau motan da ke shiga cikin kyauyen kademi....Yau tunda tashiga gida ta zauna tayi shiru duk abunda inna zatace sai dai tace mata um aa dan kudurin sabama malam english har yanzu yana ranta dan haka kimanta mai zata mai taji dadi take..
Chan tasaki wani mugun dariya da Saida yasaka inna Juyowa tace ke yar inna kin haukace ne? lapia? Mai ke damunki..Hmm inna kenan kedai kici danwaken ki ni inkika biyeni bazaki ciba dariya tasaka tana yar wakarta,"mai rabun ganin badi yagani"
Ficewa tayi agidan tana yan dariyan cin nasara...
Gidan maigari taje siyan wainar fulawa, sosai takesan zuwa nan din koba komai zataci waina kuma duk Wanda yayi mata ta chasa shi, koda tashiga gidan kuwa tine tagani tsugunne bakin mirhun wainar itama tana jira abata,.
Karasawa bazla tayi tace ummimi mai wainar yan gayu a suyan ta hamsin, washe baki umimi tayi tace kai yar inna duk ke kadan zakicinye wainar hamsin..dan bata rai bazla tayi tace yo laipine ko sata nayi nikinga inzaki zubamun ki zubamun inci inyi gaba dan nagaji da shakar tsamin wata,,
Itadai tine duk da tasan da ita ake amma sai tayi shiru dan bata shiryama balain bazla ba..
Bayan ansoya mata wainar zaman dirshan tayi tafara ci tana yar wakarta wadda kanaji habaici ne take da tine, "bandamu da banza banza ta damu dani tasha wuya, dani ke mulki sai naci burauban wata shegiya, inmatayi wasa nacire mata gashin hammata"
Ita dai tine shiru tayi duk da taji zafin wakan amma tasan bazla ba saar yinta bace..
Haka tagama waken ta ta mike tana Kada musu tender hips dinta abun dariya...**
yau Monday ranan dayakasace su bazla zasurubuta common entrance, da wurwuri ta tashi kasancewar zumudin data kwana dashi Nasan ta rubuta once and for all kuma yau ta kudiri niyan sai malam umar yabiyata bashin da take binsa, uniform dinta ta dauko light brown and white hijab Wanda tun friday ta wankesu tasaka kar kashin katifarta sabida yayi shatin gogan,dan bazla akwai san bagu a makaranta tsaftsaf zaka ganta ita a lallai kar ace mata kazama, ammafa idan a gari zaka tsinceta ko a hanyan akace ka dauka kyan kawai zai saka ka dauka...
YOU ARE READING
MU ZUBA MUGANI(completed)
RomanceLifehacks Romance Drunk in Love Challenges Lost Lust Hatred Regrets Ku dai biyoni I assure you'll like it insha Allah.....