So lemmi dedicate this page to Salmah-D and rukayyakabir444 I really do appreciate you guys ❤
MUZU BA MUGANI 💃👣
12Hannunta ya ture ajikin sa tareda facing dinta yace look nayla kinsani Nasani kin mun laipi amma kuma kina pretending kaman ba abunda yafaru you can't even say sorry Amma dayake kina naneman wani abu ne gurina so kinfara mun wani pity voice hrrn?
Mikewa Itama tayi cike da fitina tace yanzu shikenan kana mijina kafita da wata karuwa kuma ace Banida right din Tambaya ina kukaje? dan na Daketa kuma ai ba laipi nayi ba, kamata ma yayi ace Kai zaka bani hakurin marina da kayi amma na yafemaka sabida ni kai kadai ne agabana, I didn't regretted what happened today Beside duk ranan da tasake binka kuka fita I will make sure I beat the hell out of her,,.Tunda Tafara maganan zuciyansa ke wani tafarfasa Musamman dayaji takira bazla da karuwa, fushinsa yayi kokarin haddewa dan yasan tabbas idan zai dauka wani mataki to bazai wuce na tattakataba dan haka kawai ya dauka extra blanket da niyyan fita,
Nayla na ganin haka tayi sauri ta miki tareda hugging bayansa tana wani munafikin sobbing!!
Wani ajiyan zuciyan bakin ciki yayi yace nayla let go of me kar namiki abunda bazakiji dadin saba dan walh In abunnan ya tafi further I will make sure you regret knowing me,yakarasa maganan dawani kakkausar muryaa daya tabbatar mata da cewa bada wasa yake ba, da sauri ta cikasa whilst shikuma yafice yabar mata dakin!!______________________________________________
Washe da asuba haysam nashiga gida yanufa part din inna ,a hankali ya ke tafiyan sabida baya so inna ko wani ya gansa!! bangaren dakin bazla yanufa inda inna da ke Zaune daga chan karshen parlour take kallan sa amma shi bai ganta ba sabida yanayin duhun gurin, dan murmushi tayi tace dan Jakar uba Ana so amma munafurci fal ciki dan banza!A hankali ya murda handle din kofan luckily yasameta bude, Zaune ya ganta kan sallaya da alamun bata dade da gama sallah ba, juyo wa tayi sakamakon alamun shigowan dataji anyi tace inna na tash-- kasa karasawa tayi sakamakon ba innan tagani ba da hanzari tamike har tana harde kafa dan batayi tsammanin ganinsa ba, cike da dan firgici tace ya haysam ina kwana!
wani shan kamshi yayi shi a dole kar ta gano sa yace lapia lau inna fa nashiga dakinta bata nan, dan shiru tayi sannan tace to inajin ko tashiga bandaki ne bari na Duba maka,
Aa no ya katse ta "barshi idan gari ya yayi haske sosai nazo
, Emm ya kafan naki,?
Da sauki tabasa amsa a takaice, to Allah karo sauki, yana fadan haka yajuya yafita a dakin a hankali yasake bi gudun Kar inna ta ganshi, amma Kash tariga ta sakalosa tun tuni muryanta yaji tace "an muna muna gani nan ai naji kashiga dakina bakaganni ba Abu gulma's!
Dan cije hakoransa yayi yana shafa gashinsa yace kai inna kai inna menene abun gulma anan dama zuwa nayi mu gaisa kuma sai nayi batan daki ko daniyata nadawo in gari yyi haske! Yanzu dai Ina kwana!Dariya inna tayi tace dan banza ka kwantar da kai kasan Mai kake nema ba karinga min shige shigen munafurci ba, gaba yayi yace kinji tsiyarki ai inna ! ni kinga sai da safe!
yau tunda garin Allah ya waye ba wanda ya Leka main sitroom, kowa a part dinsa yayi breakfast,
Haysam kuwa yana gama abun da zaiyi ya bar gidan dan zuwa gurin wani abokin karatunsa,
Bangaren mom kuwa harkokinta take yi na tarbar mijinta da zai dawo wajejen azaahar, ko ajikinta da cewa ta yi wani abu da zai jamata matsala dan gani take dai dai tayi tunda bazla tanema Tamata rashin kunyane,,,Bangaren bazla kuwa tunda ta yi break fast tayi wanka take Zaune a parlour tana Kallon "dead note anime, ta bada gaba daya hankali ta kan Kallon dan tunda inna bata fito ba sannan ita yarda take fushi da amrah bazata iya zuwa nemanta ba so Kallon shi kadai tadan samu yake debe mata kewa!!
"Salamu alaikum" taji ance a bakin kofa Sarai tagane mai Muryan so da har ta Yan ke shawarar kin amsawa amma kuma kawai sai ta amsa sabida tuna muhimmacin sallaman!
Hankali ta ta maida kan Kallon kaman bata san akwai halittar da ta shigo gun ba!!Guri amrah ta samu very near her tareda kama hannunta tace" haba sis no matter what happened bai kamata ace wai kina fushi dani ba, like seriously I don't have the idea of abunda yafaru cikin gidan nan jiya I was deep asleep wallahi, dan lankwabar da face tayi kana da wata sansanyar murya tace sai dai idan laipin mom dina ne ya shafe ni shikuma I can't help it bazan iya wanke kai naba ko me Zance kiyi hakuri"
mikewa tayi da niyyan tafiya taji bazla ta kama hannunta juyowa tayi, kallonta bazla take idonta cike da hawaye sai kuma ta fashe da kuka tace who told you I was angry with you because of mom did to me? huh?
Hannu tasa ta share hawayen tace I was angry because I missed the prom you dummy!
Da sauri amrah ta zauna tare da hugging din ta tace im sorry sis I'm really sorry I mean it wlh I tot ya haysam zai kaikine shi yasa kawai nace ma driver mu tafi, and tunda naje gurin nan I wasn't on my right sense ni gaba daya prom din bai mun dadi ba because bakije ba, your awards and all ib ne ya karba miki nakasa, he was worried shima sosai and Dana dawo na zo inna tace mun baki dawo ba so kawai na kwanta! I'm sorry!
Cire hugging din bazla tayi ta kalle ta tace "its okay it okay sis, smiling amrah tayi ta miƙe ta daga hannunta sama tace and guess what you got the award of miss beauty and best dresser, dariya bazla tayi tareda bata dukan wasa tace kyaji da shi da Shegen tsokananki,, dariya duka suka saka kana suka zauna dan cigaba da Kallon tare!!!Around 3 daddy ya sauka cikin garin kano, wanka kawai yayi ya nufa gun inna, mom tayi tayi ya ci abinci tukunna amma yace ai kome nene inna nagaba da shi agunsa,
Sosai ranta ya baci amma sai ta hade tare dajin wata muguwar tsanar inna na Kara shigar ta,,,
Koda yaje part din inna cike da ladabi da kewa suka gaisa, "kaci abinci ", shine tambayan da inna ta fara masa inda yabata amsa da aa,
Abinci ta fita dan dauko masa Dan dama already ta shirya masa girki irin nasu na gargajiya, tuwan alkama ta masa tareda miyan ayo da yasha herring fish da naman rago, sai fresh mixed mashed fruits juice!
Daddy kam naganin dish din yafara topping dan dama inna tasan favorite dinsa ne shiyasa ta hada masa,,After dad yagama cin abinci and all zancen da zasuyi da inna kana bazla ta shigo dan gaishe sa, dawo nan yata daddy yace tare da nuna mata kusa dashi ! matsowa tayi ta na mai zama kusa dashi "congratulations yace yana murmushi mai kyau yanzu kuma sai senior class ba??
Murmushi tayi ta daga kanta cikeda kunya,
So yanzu idan na huta zan dauko muku gift dinku ke da amrah and surprise ne cewan daddy,,
Cikeda murna bazla tamasa godia tunkan ma tasan menene kyautan da ya kawo musu!Saida inna tabari bazla ta tafi kana ta umarci daddy da ya kira mata kowa dake cikin gidan!
Bai tambayi daliliba kafun kace Mene kowa ya halarta agun,
Zaune kowa ke a kasa harda mom da gabanta keta faduwa dan tasan kiran inna ba alkhairi ne a garetaba "
Kowa yayi shiru yana jiran jin bayani,
Muryar inna ne ta katse tunanin kowa dan furucin da tayi da ita
"ABUBAKAR SO NAKE YANZUNNAN KA SAKI HAFSA_______
Cliff hang huh😂okay don't kill me I will update, just be sharing, comment, and click that star sign
Xoxo❤
Chuchujay
YOU ARE READING
MU ZUBA MUGANI(completed)
RomanceLifehacks Romance Drunk in Love Challenges Lost Lust Hatred Regrets Ku dai biyoni I assure you'll like it insha Allah.....