MUZUBA MUGANI 🖊💜
39
Few months later
Skirt take ta kokarin sawa jikinta amma yaki shiganta, dariyan da taji ana mata abakin Kofa ne yasaka ta juya Taga uban wane dan tunda cikin nan yaƙara girma kullum cikin masifa take musamman idan ta Kalla kowa ɗos dashi ita kuwa tagan Abu gaba yana tokareta, kaman zata fashe tace " amrah na rantse da Allah Zan miki bakin wulakanci, ai kinsan cewa yanzu hips dina sun karu uban wa yasa kisaka amun wannan matsatsen skirt din for God sake,Wata maketaciyar dariya amrah tayi tace Ashe dai kinsan kin karu din, "mai ciki wallahi banisan sunan nan, takarashe da waka, wani kuka bazla tasa da saida amrah ta nutsu tareda karasawa inda take tace "ke bakida lapia daga wasa sai kuka? Dan Allah ki rufa mana asiri kinga gida ancika abun da kunya aga karuwa mai cikin wata biyar tana kuka dan anmata waka, ai kaman ta sake turata ta fashe da wani kukan, kaman hadin baki kuwa sai ga mom tashigo dakin "
"Subahanallah, karasawa tayi tareda Riko bazla hankali tashe, lapia mai ya faru, ta Kalla amrah wadda tayi tsuru tsuru da ido tareda daga hannu tana girgiza kai,
Cikin kukan bazla tace to mom ba wai Zan saka atamfan anko dinnan bane yake shigana, kuma ita ta kai dinkin ai, ina mata magana akai tana mun wakan mai ciki kuma tasan banasan sunan ina cewa itama aurentan Za'a daura jibi zamugata iskancin cikin da kaman tuntube ake dashi a bakin kofa, kafun mom ta juyo Amrah tafita da gudu a dakin tana dariya,Mom haɗe dariyan da yazo mata tayi, tareda shafa gashin bazla da yasha gyara tace okay its okay yanzu abunda zaayi ki Kawo kayan sai akai gun tailor yasan yarda zaayi and inace akwai wannan atampan da kika dinka bikin maryama inajin complaining kika ringayi sun miki yawa and lastly baki sa suba, yanzu yarda zaayi dress in them, sai akai a gyara wannan din, come on tafi wani so called ankon bikin amrah ma kyau, hakan nan kaman wata yarinya mom tayi ta lallabata kafun tana gwada kayan sukai mata dai dai tho sun kamata,
Dan gyara fuskanta ta shiga yi bayan fitan mom, wayanta ne yafara ringing, sunan haysam ta gani ,a silent ta saka wayan, dan in zai kirata sau Dubu bazata dauka ba, dan bikin maryama ma abunda yabata dadin zuwa kaduna shine baya nan, and tunda taji labarin ya saki nayla kuma shikenan ya sakota gaba Dakira wanda take ganin yama raina mata hankali saida yaga babu matarsa and probably yana bukatan mace din shiyasa yake kiranta, sauda dama zai zo kano amma hakan baya taba sata tabari su hadu har yagama nacinsa ya tafi, sai dai yayi ta damunta da love messages, how he missed her and all,
Cigaba da ringing wayan yayi amma taki dauka, then taji Karar shigar message, kaman bazata bude ba sai kuma ta bude,
I will never give up on you babe, keep running and lastly you'll fall on my arms, for I know you missed everything about me
XxAje wayan tayi dan she's already use to sakonninsa irin haka, aranta sai dai tace kayi kagama ya haysam Indai nice,
Sharp sharp tagama abunda zatayi ta fita kasancewar yau yinin amrah da muhedeen so sabida yawan jamaan da suke sa ran Zasu hallaci gurin yasaka suka kama marhaba event center, hakura tayi da bude ankon dan tasan tana haife cikin nan zai iya mata dai dai, ɗakin inna ta nufa dan tunda ta tashi bata saka inna a ido ba kasancewar yarda mutane sukama innan yawa!Flat takalminta da tabari dakin inna ta dauka tareda fita dan ko ganin innan ma bata samu Daman yi ba,
Part din mom ta nufa taga anayiwa amrah makeup, kunshe dariyan da kecinta tayi tace"sweet bazzy kizo amiki kwalliyya please, nasan sure yaya zai zo," banza ta mata ta shiga dakin mom sanin ba kowa dakin yasa kawai ta haye gadon mom sudden bacci kuma taji yazo mata, takalminta ta cire sannan ta cire riganta da skirt din leaving only long vest dinta, duvet ta shige, tana dora kai a pillow ta saki wani ajiyan zuciya, tace awwnnnn lastly nayi bacci without wani hayaniya, but damn I won't miss dinner,
Bayan amarya ta shirya ne tanema bazla ta rasa dan su Daman ba gurin yini zasuje ba, frnds dinta already sunzo so bridal shower zasuyi, dakin mom ta ganta deeply asleep so kawai ta rabu da ita,
YOU ARE READING
MU ZUBA MUGANI(completed)
RomanceLifehacks Romance Drunk in Love Challenges Lost Lust Hatred Regrets Ku dai biyoni I assure you'll like it insha Allah.....