12

20 2 0
                                    

kuma idan jini ya sauko ga mace cikin tsawon kwanaki kamar wata daya cur ko mafi yawan kwanakinsa, menene hukuncinsa a nan?

to nan tanada halaye har iri hudu;
1 wacce tasan lokachin hailarta cikin kwanakin watan, da kuma adadin kwanakim hailar, kuma tana iya rarrabe tsakanin jinin haila da wanda bashi ba, to anan aiki xatayi da kirgen kwanakim hailar da lokachinsa na na asalin al'adarta bada siffar jinin ba.
2 wacce ko tasan lokachin hailarta cikin kwanakin wata da kuma yawan kwanukansa amma kuma jinin kullumsa dai cikin siffa daya ya ke zuwa ma ta, to ita a nan za ta zauna ne gwargwadon kwanakin na lokachin  tsawon wata guda.
3 wacce kuma ta san lokuttan hailar ta cikin kwanakin wata amma ba ta san yawan kwanakin hailar ba, to nan ita zama zata yi na kwana shida ko bakwai (har akai ga mafi rinjayen kwanakin haila) ga yadda za ta gano iyakarsa.
4 to kuma wacce ta san yawan kwanakin ta cikin wata,amma ba ta san lokachin zuwan sa ba, to ita zama zata yi gwargwadon yawan kwanakin ta daga farko kowanne watan musulmi

hukunce-hukunce da mas'alolin mataWhere stories live. Discover now