karancin abinda yake wajibi gurin wanka shine mace ta game jikinta da ruwa har kasan gashi.
--Mace zata dauki ruwan ta da magarya sai tayi tsarki ta kyautata tsarkin, sannan ta sa ruwa a
kanta ta cuccuda shi sosai harya isa ko ina, sannan ta zuba ruwa a duka jikinta, sai tasami aduga/kyalle mai dauke da misk ta rika bin wurin jinin dashi(Muslim).-- Akwai wasu sigogin na wanka wadanda ba wannan ba, sai dai Malam wannan yakawo a
littafinsa, kuma in kikayi shi ya wadatar.-- Ba wajibi bane mace ta tsafe kitso in zatayi wankan tsarki, sai dai in an san ruwa bazai taba ko ina na gashin ba. Don haka masu kitson roba da makamancinsa da zai hana ruwa ta ba gashi wajibi su tsefe.
-- idan mace ta ga tsarki a lokacin sallah to wajibi ne ta gaggauta yin wanka domin tayi sallah akan lokaci.
-- dan kuma tana halin tafiyane kuma tasami tsarki (ga lokacin sallah yayi ko zai fita), gashi ba ruwa, ko akwai amma bazai isa ba, ko tana tsoron ya cutarda ita in tayi amfani dashi, korashin lafiya, to sai tayi TAIMAMA (tayisallar), idan la lurar ta gushe ko aka sami ruwa sai tayi wankan.
(Idan tayi sallah da wannan taimaman ba za ta rama sallar ba bayan tayi wanka).
BINABASA MO ANG
hukunce-hukunce da mas'alolin mata
Spiritualhukunce-hukuncen al'ada menene istihala(jinin ciwo) ? menene kudra da sufra(brownish discharge)?da hukunce hukuncen su menen nifasi, haila da mas'alolin su ? shin menene alamomin tsarki? ya akeyin wankan tsarki? ya ya kamata ace mace ta tsaftace...