tho idan mace tayi bari, menene hukunchin jinin?
matar da tayi barin ciki kwana tamanin (80) ko abinda ya gaza hakan wannan jinin, jinin ciwo ne (istihala). in kuma bayan kwana casa'in (90) ne wannan jinin, jinin haihuwa ne, in kuma ya kasance tsakanin kwana (80) zuwa (90) to hukunchi a nan yana damfare ne da kaga halitta, to abin daya kasance cikin sa na halitta dan adam to jininbda ya zo bayan sa jinin haihuwane, in kuwa babu halittar dan adam to wannan jinin ciwo ne (istihala)
YOU ARE READING
hukunce-hukunce da mas'alolin mata
Spiritualhukunce-hukuncen al'ada menene istihala(jinin ciwo) ? menene kudra da sufra(brownish discharge)?da hukunce hukuncen su menen nifasi, haila da mas'alolin su ? shin menene alamomin tsarki? ya akeyin wankan tsarki? ya ya kamata ace mace ta tsaftace...