yayyankewar jini

18 2 0
                                    

YAYYANKEWAR HAILA (WATA RANA TAGA JINI WATA RANA YA DAUKE)
WANNAN YANADA HALI  2:

(1)●Idan ya zama koda yaushe tana cikin jini to wannan jinin ciwo ne,hukuncin jinin ciwo ya
tabbata ga wacce take cikin wannan halin.

(2)●Ya zama bako da yaushe bane take cikin jini, tana ma da tsayayyan lokacin tsarki,saidai duka cikin haila d'aya jinin yake zuwa yadauke, to irin wannan daukewar dadawowar nashi ana daukan sha amatsayin duka jinine na haila.

☆Wata a kwanakin hailar natane  hailar zaizo sannan yadauke tsawon yini
koma kwana d'aya biyu bata ga jini ba, sannan sai yadawo kuma ya cigaba dazuba, wad'ancan lokacin da aka dauka babu jinin to ba tsarki bane har sai in kinn ga alamun tsarkin sun bayyana a cikinsu. Daukewar jinin ak'asada
yini guda ba tsarki bane sai inda ma k'arshen lokacin  al'adarkine ko kuma kinga alamun tsarki  sun bayyana.

hukunce-hukunce da mas'alolin mataWhere stories live. Discover now