yadda ake wankan tsarki:-
Hadisai da yawa sunzo ingantattu akan yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yake yin wankan janaba amma dai zamu takaita akan guda biyu in Allah ya yarda, hadisi na farko shine hadisin Maimunah Allah ya kara mata yarda tace, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kasance idan zaiyi wankan Janaba, to yana farawa ne da wanke tafukan hannun sa sau biyu ko kuma sau uku sannan sai ya shigar da hannuwan sa cikin kwaryar wankan sannan sai ya wanke al'aurar sa da hannun hagun sa
(bayan ya kammala wanke al'aurar sa da hannun hagun sa) sai ya dora
hannun hagun sa akan kasa yayi ta gogashi gogawa sosai da sosai (wato
guga mai tsanani), sannan sai Yayi Al'wallah kamar yadda yake yin al'wallah idan zaiyi sallah, sannan kuma sai ya sanya hannun damansa ya kamfaci ruwa da tafin hannunsa yana zuba wa akan sa yana cuccudawa sau uku,sannan sai ya wanke sauran jikin sa, sannan sai yadan matsa daga wajen da
yayi wankan kawai sai ya wanke kafafun sa, kawai sai nazo masa da wani tawul sai ya nuna min baya bukata"
Wato 'yan uwa wannan hadisi karara ya nuna mana yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yake yin wankan tsarki.wannan hadisi da Maimuna ta riwaito mana hadisi ne ingantacce wanda yana cikin ingantattun littafan hadisai duba (Sahih Bukhari hadisi na 274 da Sahih Muslim hadisi na 317, Taisirul-Alam Sharhin Umdatul-Ahkam na Albassam shafuka na 64-65-66, duba Umdatul-Ahkam hadisi na 34 duba Fiqhul-Muyassar Wa'adillatihi na Sa'ad Yusuf Abu-Aziz shafi na 45-46-47) sai kuma Hadisi na gaba:-
![](https://img.wattpad.com/cover/220004279-288-k407054.jpg)
ESTÁS LEYENDO
hukunce-hukunce da mas'alolin mata
Espiritualhukunce-hukuncen al'ada menene istihala(jinin ciwo) ? menene kudra da sufra(brownish discharge)?da hukunce hukuncen su menen nifasi, haila da mas'alolin su ? shin menene alamomin tsarki? ya akeyin wankan tsarki? ya ya kamata ace mace ta tsaftace...