Wanka yana wajaba da samuwar abubuwa guda uku
1) janaba
2) jinin al'ada
3) jinin haihuwa
Janaba ta rabu gida biyu
1) fitar maniyyi tare da jin dadi na al'ada a cikin barchi (a mafarki kenan), ko ido biyu a dalilin Saduwa ko makamanchin sa.
2) boyen hashafa a cikin farji (muddin aka samu saduwa ko maniyyi ya fita ko be fita ba akwai wanka)
-dukkannin wanda ya gani a cikin barchin sa kamar yanayin jima'i amma maniyyi bai fita ba, tho babu komai a kan wannan mutumin.
-amma duk wanda ya ga maniyyi bushashshe a jikin tufafin sa, amma ya kasance bai San a wani lokachi wannan maniyyin ya sameshi ba, sai mutum yayi wanka sannan ya rama abinda ya sallata Bayan ya tashi daga barchinsa na karshe da wannan tufafin a jikinsa. (Kaman ace tun sallan asuba mutum bai sake barchi ba, tho baiga maniyyi ba sai dare tho Zaiyi wanka ya sake sallan wannan ranan)( amma misali Bayan asuba Ace ya koma barchi Bayan azahar mutum baiga maniyyi ba sai dare tho zai rama sallan la'asar, magrib da isha, sallah asuba da azahar kenan Banda su)Fasali
Farillan wanka
1) niyya (a zuciya) kafin a fara wanka
2) gagautawa
3) cuccudawa
4) game jiki gaba daya da ruwaSunnonin wanka
1) wanke hannuwa zuwa wuyan hannu kamar yadda yakeyi a alwala
2) kurkure baki
3) shaka ruwa
4) fyacewa
5) wanke kofofin kunnuwa sabida itace hanya da take shiga cikin kai. Amma su abinda ya shafa fatun kunnuwa wajibi a wanke cikinsu da bayansu.Mustahabban wanka
1) farawa da kawar da najasa
2) sannan sai mutum ya wanke gabansa sai yayi niyya a lokachi da yake wanke gabansa
3) sannan wanke gabobin alwala sau daya daya
4) sannan sai mutum ya wanke saman jikinsa
5) sai mutum ya wanke Kansa sau uku
6) sannan sai mutum ya fara gabatar da tsarin jikinsa na dama kafin hagu
7) karanta ruwa akan gabbai
-dukkannin wanda ya manta da wata lum'a ko gaba na daga wankan da yayi, sai mutum ya koma ga wannan wankan nasa a lokachin daya tuna koda Bayan wata daya ne, sannan sai a sake abinda aka sallata kafin wannan lokachin(Wannan na Nuna mana mahimmanchi maida hankali dayi a natse).
Idan kuma Bayan mutum ya tuna da wata lum'a sai ya jinkirta komawa ya wanke wannan lam'a Bayan ya riga ya tuna tho wankanna sama ya riga ya lalace gaba daya(kenan mutum yana tunawa zai komane ya wanke wannan lam'an Idan ya jinkir ya ne wankan ya lalace) Idan kuma wannan lam'a ta kasance yana cikin gaba na daga gabobi na alwala, sai mutum ya sadashi da wankewar alwala ta wadatar masa.Fasali
Baya halatta ga mai janaba
1) shiga masallachi (anso ne amma ba hani bane)
2) karatun alqurani saidai wata ayaa da makamantanta domin neman tsari da makamantan haka
-baya halatta ga wanda bazai iya wanka da ruwa mai sanyi ba, yaje wa matarsa har sai ya samu abinda zai ragewa wannan ruwan sanyi, sai dai har Idan mafarki yayi tho babu komai a Kansa.
BINABASA MO ANG
hukunce-hukunce da mas'alolin mata
Spiritualhukunce-hukuncen al'ada menene istihala(jinin ciwo) ? menene kudra da sufra(brownish discharge)?da hukunce hukuncen su menen nifasi, haila da mas'alolin su ? shin menene alamomin tsarki? ya akeyin wankan tsarki? ya ya kamata ace mace ta tsaftace...