3 kuma idan lokachin salla yayi sai haila ko jinin haihuwa ya zo mata bayan haihuwar kuma kafin tayi sallah din ne idan haka ta faru to nan ba ramuwar sallah kanta
4 dole ne ga mace ta warware gashin kanta domin yin tsarki na haila, amma ba dole bane ga mai wankan janaba.
5 kuma an kyamace saduwa da mai jinin ciwo (istihala) ta farjinta, amma kuma matukar mijinta ya bukata zuwa ga haka din to ya hallata a gareshi.
6 ya wajaba ga mai jinin ciwo(istihala), ta rinka yin alwala ga kowacce sallah bayan tayi wanka haila in yaxo mata.
7 ya kuma hallata ga mace mai haila shan maganin da zai tsayar mata da jinin na wani lokachi don yin aikin hajji da umra ko kuma don cikawar azumin ramadan, amma fa duk wannan da sharadin in har ta amince wa maganin bazai cutar da ita ba.
YOU ARE READING
hukunce-hukunce da mas'alolin mata
Spiritualhukunce-hukuncen al'ada menene istihala(jinin ciwo) ? menene kudra da sufra(brownish discharge)?da hukunce hukuncen su menen nifasi, haila da mas'alolin su ? shin menene alamomin tsarki? ya akeyin wankan tsarki? ya ya kamata ace mace ta tsaftace...