yadda ake daura niyya:-
Bayan mutum ya kammala wanke al'aurar sa kamar yadda mukayi bayani idan ma mace ce ta kammala wanke al'aurar ta gaba daya da kuma duk inda suka san maniyyi ko Jinin al'adar ya ta6a to anan ne mutum zai dora niyyah, duk da dai kowwa ya sani cewa tun lokacin da mutum yazo yana kokarin samun ruwan wanka ya rigaya yasan wane irin wanka zaiyi a Zuciyar sa to amma anan anaso ka kudurce niyyah cewa ga irin wankan da zakayi, shin na janaba ne ko kuma Haila ko kuma Biqi, to yadda akeyin niyyah din shine, mutum zai kudurce acikin Zuciyar sa cewa ga irin wankan da zaiyi, kuma lallai kusani dukkanin wanda ya bayyana niyyar sa a baki to shirme yayi kuma yayi bidi'a domin baiyi koyi da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ba, don haka sunzo da wani abu ne sabo wanda Addinin Allah baisan dashi ba.
![](https://img.wattpad.com/cover/220004279-288-k407054.jpg)
YOU ARE READING
hukunce-hukunce da mas'alolin mata
Spiritualhukunce-hukuncen al'ada menene istihala(jinin ciwo) ? menene kudra da sufra(brownish discharge)?da hukunce hukuncen su menen nifasi, haila da mas'alolin su ? shin menene alamomin tsarki? ya akeyin wankan tsarki? ya ya kamata ace mace ta tsaftace...