03

44 4 4
                                    

to kuma kwana nawane mafi yawa ga mai haila kafin ya dauke?

Shaikul Islam bin taimiyya (Rahimahullah) yace: babu karanchin adadin kwanakin haila, kuma babu Adadin tsawon kwanakinta, idan jini ya fito da kamannin haila tho wannan haila ne, ko da kadanne ko da mai yawa. Sannan yace; Allah ya alaqanta haila da hukunce hukunce masu yawa a cikin alqurani da sunna, Amma bai ambachin adadin karanchin kwanakinta ko yawanta ba, ko tswanchin lokachin tsarki tsakanin wata haila zuwa wata haila. Duk da yake akwai bukatar sanin haka.
Sannan yace wasu malamai sun ambace karanchi kwanakinta da yawan kwanakinta amma sun banbanta a hakan, wasu kuma sun fadi adadin tsawon kwanakinta amma basu fadi karanchin kwanakinta ba, ra'ayi na uku wanda yafi zama dai dai shine haila batada tsawon kwanaki kuma batada adadin kwanaki.
(Majmu'ul fatawaa, 19/237).

Zan kafa hujja dai da ayar nan ta cikin Suratul Baqara (wadda ta ce, "Kuma suna tambayar ka game da jinin haila na mata, ka ce wannan qazanta ne, ku nisanci mata a lokacin da suke jinin al'ada kada ku sadu da su." A nan Allah ﷻ Ya gina hukunci ne ba tare da ya iyakance wani lokaci na musamman ba . Wannan iyakance lokaci ya samu ne da ƙoƙarin malamai da ijtihadi domin su sauƙaƙawa mutane don su fi saurin fahimta, ba wai don cewa lallai wannan maganar sai an sami kwana kaza ba, maganar Allah ﷻ ce ko ta ManzonSa ﷺ. wannan ƙaddarawa da malamai suke yi da kwana kaza, duka babu abin da ya zo a cikin littafin Allah ﷻ ko a sunnar Manzon Allah ﷺ wasu sunce kwana goma, wasu kwana takwas,wasu  kwana sha biyu ,wasu kwana goma sha biyar wanda shi ne ya fi shahara a tsakanin malaman yanzu.
            Wannan iyakancewan bai zo a cikin qurani ko hadisi ba Amma saboda abu ne da ya shafi mata, matan nan kuma suna sassauyawa daga gari zuwa gari, ko ƙasa zuwa ƙasa, ko lokaci zuwa lokaci, ko yanayin jiki zuwa yanayin jiki, ko yanayin kwanciyar hankali ko damuwa, ko kuma irin abincin da ake ci, kuma da a ce lallai sai an yi la'akari da wannan za a gina hukunci, da Shari'a ta gina hukunci a kai, domin al'amarin jinin al'adar nan yana da alaƙa da manya-manyan ibadu, musamman sallah saboda idan ana jinin al'ada mace ba ta sallah da azumi.Yana da alaƙa da saki, domin ba a sakin mace idan tana jinin al'ada. Mace ba ta sallah ko azumi ko ɗawafi idan tana jinin al'ada.

hukunce-hukunce da mas'alolin mataTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang