"Haba Umma, Ke ko kunya ma bakyaji ace Jiya ankawo miki Suruka Yau har kin fara nuna mata halinki, Hava Umma wannan ba ajinki bane gaskiya, kamata yayi ki gode Wa Allah ma da ya baki surruka mai hakuri Amma wlh ni babu wata tsohuwan da ta isa a kawo ni gidan danta jiya ta Sani wanki yau, inaa Allah saidai ayita ta qare Ehey" Na fada ina hararta ta qasan ido
"Ke dallah rufe ma mutane Baki, Me kika Sani a zama da uwar miji?, insha wahalan Daukan cikinsa , haihuwa da raino , Wata tazo da rana tsaka tace zata rabani da Dana?😏 , Ai ko kece nasan zakiyi fiye da hakan mah"
"Mtsww" Naja tsaki tare barin wajen Har na kai bakin kofa sai na waiwayo nace
"Umma ina Rabaki,.....Ban iya waazi ba da nayi miki waazi ko Zaki gane ki fahimta zama damatar da ba zama da baiwa bane, Don kin haifeshi kin Raine shi ita ba haifan ta akayi ba?.....Ohw no wonder JJC ne ke damunki tunda baki ta6a aurar ba shiyasa kike Son shinfida tsiya da na farko ko?......abege duk ba wannan ba mah, ah no fit talk for this matter.. kije ki kar6i wankin ki kiyi da kanki,Inba haka ba ina komawa gida zan fadawa Abba," Ina dasa aya NASA kai na yi ficewa ,Na barca da Bakin cikin maganganun da na Gasa Mata,
Duk cikin 'Ya' Yanta Babu wacce take kallon ta kaitsaye ya Gasa Mata maganganu Sai Ni, Ta rasa mai yasa,bata iya maida mini martani ko ta kwa6e ni Akan Rashin kunyan da Nike mata ba, Ko Dan halaccin da iyayena suka yi Mata a lokacin da suke Raye ne oho!Ina fita daga dakin Umma kai tsaye parlor na nufa inda na tarar da kawayen Amarya ,Na karasa inda suke fuska sake inagaishe su.
Yasira babbar kawar Amarya ta kalleni tace "Wai ina Amarya ta shiga ne inata trying numbern ta yana Ringing amma Baa dauka ba, To nayi tunanin may be suna tare da angon ne ,kuma kinga bai kamata na takura ta ba"
Kalamanta na karshe sun bani dariya _(wato suna tare DA Ango_ ) saboda haka sai da nadan dara "hehehe aikam Suna Tare da Ango Fa, Kuje Common Room zaku ganta wankin kayan uwar angon takeyi" Ina gama fadin haka nayi gaba ina dariyar mugunta😂Gaba daya kallon kallo sukeyi babu mai cewa uffan Dan basu Fahimci inda maganganuna Suka nufa ba.
Suna Haka sai gata ta fito Riqe da bucket mai dauke da wankakkun kaya.
Turus tayi ganin kawayenta zaune duk sai kunya ya kamata, ita shar ta manta sun kirata sun fadamata zasu zoJiki a sanyaye ta ajiye bokitin wankin ta nufi inda suke zaune sun Zuba mata ido, ta kakaro murmushi tace "aah Yassy,Rukky ai banyi zaton zuwanku yanzu ba na dauka sai da rana ne"
Rukky da ta kasa hakuri tace "Amarya kece da Wanki da kanki?,"
"To laifi ne Don nayi wanki?"
Yaseera tace"Ba laifi bane,Amma wannan ai ba kayanki bane, ji uban kayan fa?,In ma naki ne daga jiya zuwa yau ai bai ci ace kin bata Uban kayan nan ba koke waye kuwa"
Cikin in ina Ramla(Amarya) tace "Eh dama kayan umman shine tace nadan wanke mata"
Rucky tace "baga kanwarshi ba?,Meyasa bata bata ta wanke ba?,Sai ke zuwan jiya,kuma kinsan yanayin jikin ki baki da lafiya akayi auren nan maimakon ta......"
Muryan Umma Sukaji abayan su tana fadin" To Sannu uwarta Sannu Mara kunya, ke har kin isa ki tako kafarki har gidan Danakice Zaki ci min mutunci?, ko gidan ubanki ne nazo kia min haka?,Ballantana Gidan Dan da na Haifa da kaina"Sai ta tsagaita tana nunasu da yatsa manuniya tace"banason dogon magana daku domin yin hakan barazana ne a gare ku kafin in kirga Uku Ku fice min a gida Banason Sake ganin wata daga cikin ku ta tako kafafunta tazo gidannan oya Get owt of my Sight jare" Ta karasa tana nuna musu hanya
Ruky tayi Yar dariya harda tafa hannaye "Lallai tsohuwa ai ko baki kore muba fita zaayi,Allah yaso badaga gidan matsiyata muka fito ba,kowa da gidan ubanta, Mtsww aikin banza" Tana dasa aya ta dau jakarta ta fice ba tare da ta waiwayo ba, yaseera ma tabi bayanta Suka shiga motarsu Suka bar harabar gidan
Bayan fitar su Umma ta kalli Ramla tace "Tunda haka kika za6a wato kiran kawaye ana ci min mutunci to bismillah mu zuba dani dake Dan halak ka fasa " Tadaka mata tsawaZaki je ki karasa aikin da nasaki ko inje inyi da kaina?"
Ramla ta share hawaye kamar tace mata eh amma bazata iya ba, Dole ta je ta karasa abinda ta umurceta tayiDadare 11:00pm na dare Aryaan ya Shigo da ledar kaji da fresh milk Dan jiya Umma ce ta cinye masa kazar amarcin Sa Wai yunwa takeji gaskiya kuma ita kazar take so(ohh ni 'yasu 🙆🏻♀️,see me see wahala yau ga uwar mijin novel me cin kazar amarcin matar danta😆)
Cikin Sanda ya Shiga gidan ya tarar babu kowa a falon sai karar TV yasan wannan aiiki nane (barin TV a kunne),Ya karasa ya kashe Tvn, ya haura sama kamar wani barawo zai bude kofan bedroom yaji an kira sunansa Ta baya" Aryaan har ka dawo?, To ina zaka da Leda haka?"..
Baki na rawa yace "Ehm dama kazace da fresh milk, Kinsan ban kawo mata jiya ba, Shine nace...."
Bai karasa ba yaji tace "Kaza da madara?, nifa?, ka barni da yunwa ka siyo ma wata gardiya kqza harda madara?,"
Sai ta fara sharar kwalla
"Daman na Sani auran nan ba alkhairi bane a gare ni shiyasa na nace akan bazaka aureta ba,Amma ka nuna min ban isa ba gashi Tun baa kai koina ba ka fara wulakantaniAryaan ya rumtse ido cikin matsanancin 6acin rai yace " Umma ba dai akan kaza bane?,To gashi" ya bata ledar kajin bakunya ba tsoron Allah ta sa hannu ta kar6a
Yace to sai da safe ya juya zai shiga daki ya dakatar dashi " Ai ba shi kenan ba ,dama Tun dazu nake jiran dawo muyi hira"
Ya kauda zancen da cewa "Umma yaushe Zaki koma?"
Tace "Ka kosa in tafi ne?"A ransa kaman yace eh amma sai ya girgiza kai "Aa Umma dama gani nayi an gama biki kuma..."
"Kuma na takura maka ko?" Sai ta fara sharar kawalla "Da nasan haka zaka wulakanta ni aryaanu da Ko gidan nan ban tako ba , yanzu zamani ya chanza da ke korar uwarsa a gida akan yayi mata!😭😭"Aryaan ya dafa kai "ohh my god🤦🏻♂️, in hira ne Umma idan nayi wanka na ci abinci zanzo"
Umma ta share kwalla tace "Muje part dina kkayi wanka sai muci Kazan nan tare nima yunwa nake ji"
Aryaan bakin ciki kaman ya kashe shi haka babu yanda ya iya ya biye mata yayi abinda take so
Ramla da ta Dade tsaye bakin kofa tanajin su ta share hawaye ,Tun ranar amarcinta tafara fuskanta matsala da uwar miji ina ga nan gaba, jiki a sanyaye ta koma ta kwanta tana tunanin kalakala akan yanda zaman su da Umma zai kasance
Washe gari Monday Nida Hafsah muka shirya Tun Shida da rabi ko break fast bamuyi ba Saboda lecture dinda muke dashi7:00am gashi shegen lecturer ne baya daukan excuse, Gashi yana taking attendance serious
Nida Hafsah muka shiga motana naja Muka fice da gidan A hankali muna Dan ta6a hira
Hafsah tace "Sis kinji Draman DA ya faru jiya da daddare?"
Na juyo na kalleta sannan na maida hankali na ga tukin da nikeyi
Nace" bani nasha"Shin Wai wane irin gulma hafsah ta kwaso?Me zaku fada akan wagga uwar mijin?😂
Please share
And
CommentFahnaan🖋️
Acigaba da wanke hannu😂
Stay safe😀
9^Aug^August
YOU ARE READING
HAWAN JININA (Uwarmijina)
AcciónLabarin Uwarmijin da ta Takura Wa surukarta, daga baya Ta hada danta Aure da Wata Yar Uwarshi saboda wata 6oyayyen kudurinta ,Amma me?, sai Yarinyar ta zamar mata Raina kama..........