JJT 18

20 2 1
                                    


*Safiyyah Galadanchi*

*JAJIRTACCE ( ABUBAKAR SADEEQ)*

*shafi na goma sha takwas*

Shaddar yake kallo sai yanzu yake ganin kyaunta da aka dinka, wallahi da badan bashida yadda zaiyi ba da bazai saka wannan shaddar ba, karamin tsaki yayi ya dauki rigar ya saka ya fesa turare, gyara zaman hularsa yayi sannan ya saka agogonsa mai matukar tsada, gaba daya se yake ji kamar rayuwarsa ta da ce har turaren daya daina amfani dashi dole seda ya nemo shi saboda shiga cikin irin mutanen nan dole sai an shiga da kamala saboda gudun wulakanci.

Yana kammala shiri wayarsa tai kara sunan masoyiyar yagani ya daga da sauri tace "kafita waje ga Emma can ya kawo maka motata kazo ka dauke ni nida Aisha" ya amsa da to ya kashe wayar, fita yayi wajen ya karbo dawowa yayi ya dauki wayarsa da hanky ya sake fesa turare yana duba agogo karfe takwas saura.
Da fitar sa saida ya tsaya masallaci yayi sallah sannan ya fita, gidansu ameera ya nufa bayan ya Isa ya kira wayarta basu jimaba suka fito.

Murmushi yayi ganin leshin dake jikinta kalar shaddarsa bayan sun zauna a motar ya gaisa da Aisha ya kalli ummee Tasha makeup kamar ba ita ba yace "kunyi sallar ishai kuwa"? Ta gyada masa kai tana cewa "yanzu mukayi seda nayi alwala sannan nayi kwalliyar".

Amarya ta rigasu isa Hall din da za a yi dinner koda sukaje har an shiga Anfara gabatar da bikin, da shigarsu kallo ya koma sama sadeeq ya kara daure fuska kamar bai taba murmushi ba, Aisha ko tana biye dasu a baya duk Wanda ya kalleta yasan tanada ciki, basu Dade da shiga ba wayar Aisha tayi kara mijinta ne tana dagawa yace "yi maza ki fito mu wuce gida" dan bata rai tayi sannan tace to.

Ummee ta karaso da daurin kudi na Dari biyar-biyar ta ajiye gaban sadeeq  Aisha tace "Dr yazo fa zan wuce" ummee tace "OK muje na raka ki to" fita sukayi sadeeq yabi bayanta da kallo mayafinta da babu duk daya se yaga mazan dake wurin duk ita suke kallo har wani ya mike tsaye yabi bayanta.
Kallon kudin dake gabansa yayi yayi tsaki babu dadewa yaga ta dawo fuska a daure da wannan gayen ya biyo bayanta yana cewa "Numbern ki kawai nakeso Dan Allah" kallon gefen sadeeq tayi suka hada ido yayi saurin dauke kansa, tayi murmushi tana Nuna masa sadeeq tace "kaga wancen? Da sadakinsa a kaina saura wata biyu da kwanaki auren mu" daga haka taci gaba da tafiya tana zuwa ta zauna kusa dashi sosai tace "kayi hakuri na barka azaune, ya baka sha ruwan ba"? Ya girgiza kai yace "na koshi da ruwan ne bana jin kishi" ta gyada kai tana cewa "kaga mutumin can dayake ta bina? Beda hankali saura kadan fa ya rike min hannu" murmushi yayi yana kallon fuskarta sosai yace "kin masa kyau ne kamar yadda kika yimin kyau, meyasa kika saka wannan karamin mayafin" ta kalli gyalen tace "just to cover ne ai garama ni bakaga sauran yan Matan ba" ya Shafa sajenshi yace "just to cover what? Me wannan abin yayi covering? Yan mata karki deceiving kanki wannan abin bashida banbanci dasu da basu yafa ba, wata acikinsu ma kinfita jikin da za a kalla a sake kallawa" saurin dukar da kanta tayi saboda kunyar zancen tana turo baki yace "to yanzu yaushe zamu wuce gida" ta kalleshi tace "karfe goma zamu bar nan amma yanzu muje ka gaisa da angon" mikewa yana gyara rigarsa ita kuma ta tsaya taba harhada wayoyinta da kudin dake kan table sai hasken flash suka gani ta dago zata kalli daga inda hasken take ta sake ganin sa, camera man ne yaga sun masa kyau juyawa tayi ta kalli sadeeq tana murmushi saita dage mata girarsa daya yana murmushi shima, dariya tayi tace "ranka ya dade abari mu shirya mana wannan unexpected hoton haka ya Isa" dariya yayi yace to "bismillah" komawa sukayi suka zauna seda ya daukesu hotona kusan dozen sannan tace ya tura mata ta WhatsApp.

Ango kuwa yama manta da labarin sadeeq sai yake masa kallon wani shahararren mai taka daloli, sun musu liki tareda hotuna sannan karfe goma kowa ya watse tareda abubuwan arziki da aka rarraba cike da tsari.
Gefe ameera taja ummee tace "yaufa akwai bala'i kinsan mutumin nan awurin nan yake tambayata na shirya ko"? Umme cike da rashin fahimta tace " kinshirya me"? Tsaki ameera tayi tace "muje waje ke kiji" suna fita tace "halakani fa zeyi yau kuma kinsan mommy tamin durin abubuwa wallahi" tabe baki tayi tace "se kika ce masa me"? "Murmushin yake kawai nayi masa amma shawara nake bukata awurinki"  dariya ummee tayi tace "gara ma ke zakisan da abin yau nifa? Babu shawarar da zan baki illah karki yadda ki kwana cikin tsinuwar mala'iku da aurensa akanki" tana rufe bakinta angon yace "meyasa mata kome akeyi sekunyi tsegumi"? Hararar shi ummee tayi tace "nidai ga amanar aminiya ta a kulamin da ita yadda ya kamata zanzo kuma da idona ingani" dariya yayi yana cewa "to kidai bata shawara me kyau naga alamar raguwa CE" sadeeq ya kawar da fuskarshi yana murmushi Dan yaga su biyun basu fahimci abinda angon yake nufi ba.
Sallama yayi masa yacewa ummee "ki sameni amota".

Tunda suka shigo mota zuciyarshi take saka masa koda Dan peck ne yayiwa ummeensa ya rage zafi yau dinnan ta tafi dashi fiye da tunaninsa har ya iso gida yana shirin yi mata sallama ya kalleta cikin ido saitaga kamar idonsa da maiko ta kawar da nata idon tana cewa "gobe babu India zani ina bukatar Hutu" yayi murmushi yace "bazaki je duba amanar dakika bawa ango ba" tayi saurin saka hannu ta rufe bakinta tace "ka rufa ni ka sayani Dan nasan ma naje koroni zasuyi" murmushi yayi yace "to tunda ameera tana wurin angonta nikuma gani gaki me zaki bani" tayi dariya tace "duk abinda kakeso" yayi dariya mai sauti tare da riko hannunta guda daya ya rike da duka hannunsa biyu zuciyarshi ta Shiga bugawa da sauri yakai hannun bakinshi yayi masa kiss sannan yace "gud nyt, dare nayi kiyi tuki a hankali" fitowa yayi yabarta da shock dan zaman ta dashi seyau ne ya taba riko hannunta tabi bayan shi da kallo dakyar ta dawo gefen driver taja motar ta wuce.

Shi kam ranar yaji jiki, sha dayan dare ya saka laila ta dafa mishi Lipton da lemun tsami, Anty ta harareshi yana zaune gefen gado tace "wannan wane irin hali ne yarinya tana bacci zaka tashe ta shan Lipton din jaraba" Abba ya daga labule yace "Dan Allah kisakewa yaron nan Mara yayi fitsari haba Aisha" Anty ta kalleshi tace "ya tashi yarinya tana bacci kuma ace bazanyi magana ba sannan Lipton da lemun tsami duk dare seyasha menene amfanin shan banda daukarwa rai wahala" yayi dariya yace "to ina ruwanki"? Sannan ya sake labulen ya fita mikewa tayi tabi bayanshi tana cewa "yajikin goggo" yana bude dakinsa yace "seyanzu kika tuna da ita kintsaya sa ido" tayi dariya tace "dole nayi magana yarinyar nan yau bako lafiya gareta ba" Abba yace "kidai kyaleshi tunda kikaga yana sha ai yanada dalili idan Allah ya yadda ma ai ya kusa aure ya huta, meyake damun laila din"? Takarbi hularshi da agogo tana cewa "wai fa period ta fara yau shine tun rana take ciwon ciki se magrib tadan ji sauki" yayi murmushi yace "Ashe auta ta girma ta kusa sure" dariya Anty tayi tace "Allah ya nuna mana ya jikin goggo" yace da sauki ashe targade tayi nakaita dai an gyara nacewa Hamisu dai suringa kulawa ama cire mata wannan tile din a toilet asaka Wanda beda tsantsi" daga nan suka ci gaba da hiransu gogan ko daga shan Lipton ya bingire awurin yana baccin wahala laila dama tana ajiye masa ta wuce dakinta Dan bata jin dadin jikinta. Sai shabiyu Anty ta fito rufe gida taganshi yayi mata rashe- rashe a gado ta dauki abinda zata dauka takashe masa wuta.

A kwana a tashi har lokacin biki yazo a lokacin kuma ummee sun koma makaranta level 3 first semester.

*jini yafi ruwa kauri*
*Fiyyah ba gaisheku*

JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)Where stories live. Discover now