JJT26

13 1 0
                                    


*Safiyyah galadanchi*

*JAJIRTACCE ABUBAKAR SADEEQ*

*shafi na ashirin da shida*

Bayan ya sallame sallar ya duba gefenshi baiga ledar ba ya duba bayanshi nan ma haka nan take zuciyarshi ta fara bugawa ya kalli mutumin dake zaune gefenshi yaga sai Jan carbi yake yana salati jikinshi ya fara rawa amma ya danne liman ya tada salla suka bi bayanshi, shurun dabyayi ko yasan idan yayi magana awurin lokacin salla zai iya shigewa ana maganganu, bayan an kammala sallane yacewa na gefen nashi "Dan Allah dan uwa bakaga ledar dana ajiye ba ko kuma wanda ya dauka"? Mutumin ya girgiza kai yana cewa "banga wanda ya dauka ba amma tabbas naganka da ledaa hannu lokacin da ka shigo, sedai bayan ka kabbarta salla wani mutum ya shigo ya tsaya bayanka nayi tunanin salla ya shigo yi dan ya zauna sedai naga yanzu ba tare mukayi salla ba" tunda ya fara magana sadeeq yake maimaita innalillahi wa'inna'ilaihiraji'un tun yanayi acikin zuciya harya fito fili nan hankalin mutanen masallacin ya dawo kansu, mutumin yace "bawan Allah badai kudi ne ko wani babban abu ne aciki ba" sadeeq ya kalleshi yace "har dubu dari uku kuwa, nan da nazo da zan bada su ne ga abinda na gama maganar siya sai kaddara ta saka na fito lokaci kurarre"  nan masallaci ya kaure surutu suka fito waje dan masallaci wajen ibada ne anata tsinewa wanda yayi karfin halin wannan sata awuri mai Daraja masallaci sadeeq dai jikinsa duk ya mutu ya rasa yadda zai yi suna nan wurin dayake mutanen unguwa ne mutumin dake gefenshi yace "baza kayi bincike ba? Daka saka an kamo maka wani matashi anan unguwar yake mukanmu ya addabemu shekaranjiya  nan aka sacemin akuya kuma danayi bincike sai aka samu yaronshi ne ya tura ya sace saboda gawurta a wurin sata da yayi yara gareshi wata kila cikin su ne yau ya hadu dakai anan" Sadeeq yayi murmushi yace "a'a duk  wanda ya dauka nabarshi da Allah idan zanyi bincike niba nan nakeba wahala kawai zan sake sha nabarwa Allah shine ya bani kuma shine ya aiko da wannan kaddara a gareni kuma na karbala hannu Bibbiyu" dayake mutumin akwai rashin tawakkali yashiga zuga sadeeq amma duk yadda yayi sadeeq yaki yadda har suka koma masallaci sallar ishai, bayan sun kammala sadeeq yayi azkhar dinsa sannan ya daga hannu sama yana rokon Allah yace "Allah na gode maka daka sanya kudin nan nawa ne aka dauka bana wani ba daga hannuna Allah ka musanyamin da abinda yafi zama alkhairi Allah ka kara bani hakuri da juriya akan wannan kaddara data sameni ka bani mafita ta yadda zan bauta maka da imani na samu abinyi wanda zan dauki nauyin kaina da gidanmu da iyalina, Allah kafini sanin daidai da abinda yake alkhairi a gareni shiyasa ka hada aurena da ummee Allah kabani ikon yi mata fiye da yadda ake mata a gidansu Allah ka amshi adduata dan girman zatin ka da daidaituwarka akan alarshinka" ya shafa adduar yana kokarin tashi tsaye yayiwa mutanen wurin sallama ya fita duk da ya rage jin zafin abinda ya faru amma har lokacin baiji jikinsa da karfi ba.

Bayan suma sunfito ne suke maganar sadeeq din dayake maza ma akwai tsegumi yanzu mutumin nan yace "kai wannan bawa akwai tawakkali, addua yake yana yiwa Allah godiya daya saka kudin nashi ne bana wani ba, har ya kammala kuma banji yace Allah ya isarmasa ba banji ya laani barawo ba kai inata mamaki akwai mutane irinsa har yanzu" wani yace "aishine Allah dai ya sauwake".

Wani wuri ya samu ya zauna yanata tunanin rayuwar duniya, Allah ya gani kudin nan yasaka buri sosai akansu dasune yake tunanin gina sabuwar rayuwa da ummee, yanzu bashida wata mafita dan sabon jari ne aka sace tunda ya cinye wancen wajen gyaran gida da sauran su. Se kusan sha daya da rabi ya karasa gida koda ya shiga Anty harta rufe dakinta sun kwanta, haushi yaji sosai dan yaso ya rungume matarshi saboda wannan hali dayake ciki yana bukatar lallashi palo ya dawo ya kwanta  saiga Abba ya shigo yana cewa "kai lafiya ka tayarwa matarka da hankali gashi ko waya bakada"? Ya mike zaune kamar mara lafiya yace "abinda naje yi ne bansamu na karasa da wuri ba babu laifi ai Abba da safe sai mu wuce" tsaki yayi yace "ba maganar abinda kaje yi ba, har kuka fa yarinyar nan tayi yau dakyar muka samu tayi shuru bacci ya dauketa ka daina yin irin haka" hakuri ya bawa abba sannan Abba yace "ka shiga dakin Antynku tana nan ciki ita kadai ka sake dubata kafin kazo ka kwanta" ya amsa da to a ransa yana cewa mu kwana can dai.
Koda ya shiga saida ya kunna wuta ya cire jeans da rigar jikinsa ya Dorasu gefen gado sannan ya kashe wutar ya kwanta kusada ummee din kamar ya farkar da ita ta riko hannunsa tana sauke ajiyar zuciya, kissing bakinta yayi ta bude ido tana neman fuskarshi cikin duhu tace "ka tsorata ni sultan" cikin wuyanta ya tura fuskarshi yana bata hakuri hardai aka fara nunawa juna kauna saida abu yayi nisa tayi saurin matsawa tana cewa "innalillahi kan gadon Anty"? Tsaki yayi yana cewa "ko gadon Abba ne ai tunda muka kai haka sai an karasa karki cuceni" ta girgiza kai tana cewa "wallahi da kunya ni kazo ma ka fita dan Allah  zata fa iya shigowa daukar abu taganmu" ya janyota yana cewa "sadai ko balla kofar zatayi dan na kulle da makullli".
Saida suka makara sallar asuba koda sukayi har haske yafito, ya maida kayanshi yana cewa "bari na fita kafin anty tazo tana buga kofa" ummee tace "kunyar karya bayan ka tumurmushe yar mutane kan gadon ta" baiyi magana ba ya fita babu dadewa anty ta shigo ta kalli ummee tana cewa "sadeeq ya shigo"? Ummee tace yanzu ya fita ma ashe tun cikin dare ya dawo" ta fada tareda gaisheta anty ta amsa tana cewa "hankali ya kwanta ko matar sadeeq" kunya taji nan anty ta fita kitchen ita kuma ta kamawa laila suka share gidan tsaf suka goge sannan bayan sun karya suka wuce "Allah ya taimakemu kayi dabarar saka nama a freezer da yanzu ya lalace" ummee ta fada lokacin da take ajiye komai daya siyo a muhallinsa ta sake cewa "wai meya tsaida kai jiya, ka karbo kudin kuwa" ya gyara tsayuwarsa yace "nakarbo dubu dari uku da hamsin na siyo waya sabuwa sena shiga kasuwa nasiyo abubuwan nan nakawo gida naje fa da kudin wurin siyan shinkafa aka sace a masallaci jiya jikina a sanyaye yake banaso kowa yasani shiyasa na tsaya seda naji nutsuwa sannan nashiga gida" ta zato iro dana fadin "innalillahi wa'inna'ilaihiraji'un sadeeq garin yaya"? Nan ya labarta mata abinda ya faru addua tayi masa tana ta tunanin yadda zatayi ta bashi kudi sai bayan azahar dabara tazo mata tace masa "da nace ko zan ara maka kudi idan ka juya saika bani kudina ko" har zaice baya so sai wata zuciyar ta hane shi yace ya yadda acikin wata hudu zai biyata, tura masa kudin tayi dubu dari biyu ta account dinsa be zauna ba yanata fara'a tareda yiwa Allah godiya ya fita bai cire kudinba transfer yayi musu da waya aka Killace masa buhuhunansa na shinkafa yace da safe zezo ya dauka idan Allah  ya kaimu, ya dawo yana fada mata "kudin nan sunyi auki ummee Allah yayi miki albarka yabarni tare dake Allah ya rufa miki asiri yadda kika rufamin" ta amsa da ameen tana ajiye masa abinci.

Koda ya tashi washe gari missed calls goma daga numbern wanda ya siya shinkafar wurinsa. Tun kafin ya kira yaji gabansa na matukar faduwa.

*fiyyah na gaisheku*

JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)Where stories live. Discover now