*Safiyyah Galadanchi*
*JAJIRTACCE ( ABUBAKAR SADEEQ)*
*shafi na uku*
Mikewa tayi tsaye tace to Momy bari naje nayi wanka sai inje in bashi hakurin amma Momy meyasa bazai yadda in auri sadeeq ba shima ai yasan da bashida arziki ko kadan daga baya ya samu" murmushi Momy tayi tace "ba haka bane Daddynku acikin daula ya taso saboda mahaifinshi mai arziki ne bayan haka kuma kinga su biyu ne kawai awurin iyayensu dan haka suka samu gata fiye da yadda kike tunani inaga shiyasa kema yakeso ki taso acikin wannan gatan har abada" dan hawayen daya taru a idonta ta share tace "to bazai bawa sadeeq aiki ba idan hakane" Momy ta kalleta tace "kije din idan kin dawo ki sameni a part dina kinji kuma banason ganin wannan hawayen Allah ya miki albarka" fitowa sukayi a tare wani Palo ne mai girma dauke da set din kujeru biyu ya matukar yin kyau ummee ta nufi wani daki gadon cikinsa yafi wancen haduwa da komai kayan jikinta ta cire sannan ta shiga tayo wanka kamshi kamar da zallar tarare tayo wankan jikinta yadanyi ja saboda zafin ruwan da tayi wanka dasu kayan bacci ta saka Riga da wando ta Dora babban hijab akai sannan ta fita.
Zaune ta sameshi a Palo yana aiki da system ta zauna gabanshi a kasa ta kalleshi tace "kayi hakuri Daddy" ya matsar da system din gefe ya kalleta sosai yace "inyi hakuri kin rabu da wancen kucakin"? Tayi murmushi tana girgiza masa kai tace " Daddy inajin haushi aduk lokacin da wani ya bude baki ya fadi mummunar kalma akan sadeeq kamar yadda bazan taba yadda wani ya fadi mummunar kalma akan ka ko daya daga cikin yan uwa na Daddy dan Allah kar ka rabani da Sadeeq" kofa ya kalla yabuga tagumi sannan yace "karki sake ki gayamin maganar banza awurin nan ummee wannan ai iskanci ne da rainin wayo na gama magana bana bukatar jin koda sunan yaron nan ne kuma menene shi idan ba kucakin ba" shuru tayi hawaye na zuba daga idonta a hankali ta mike ta fita daga palon "wannan karon ta cire rai daga samun Sadeeq indai a wurin Daddy ne bai taba yi mata haka ba se yau, tana shiga part dinta ta kashe wayar ta sannan rufe kofa tundaga Palo wani dakin daban dayake can lungu ta shiga shima ta rufe sannan ta kwanta wannan karon duk yadda takeso kar damuwa ta kama ta hakan bai yuwu ba ta Dade batayi bacci ba daga baya ta mike ta dauro alawala ta gabatar da salla tareda yin addua.
Washe gari yana tashi da asuba ya shiga toilet yayo wanka ya shirya tareda dauko karamar jaka ya zuba abubuwan da yake bukata aciki sannan ya fito kofar Anty ya bubbuga ta fito sanye da hijab ta kalleshi tace " ina zaka tun yanzu Sadeeq" ya Sosa kai yana murmushi yace "Anty zanje durbawa ne gona" ta gyada masa kai tace "amma ai kwanaki danayi maka magana kace akwai masu yin aikin kai yanzu me zakaje kayi, Abubakar wannan wace irin rayuwa ce ka daukarwa kanka kaikenan kullum cikin yawo da bakar wahala ka fada nan ka fada can" ya gyara tsayuwarsa yace "Anty kema bazaki so ki ganni zaune a haka ba bana aikin komai" ta dafa Bango tace "amma Abu Nawa kake yi? Bayan adaidaita sahu kana aiki gona kana harkar shinkafa kuma duk wannan uwar wahalar basu kadai kake yi ba ba kuma wanda yasan Inda kudin suke zuwa wace irin rayuwa ce zaka daukarwa kanka" yayi murmushi yace "Anty ko yanzu shinkafar ce zanje inga idan ancire kamar yadda mukayi dasu se in dauko" ta sauke ajiyar zuciya tace "Allah ya taimaka ya bada Sa'a amma dai tsaya ko tea kasha kafin ka wuce, shigo ka zauna palo" baiyi musu ba ya shiga ya zauna palon ba laifi bashida matsala kujerun bana talakawaba bana masu kudiba sai karamin TV na bango carpet ce a shimfide tsakiyar palon, tea ta kawo masa da bread tace "babanku yace idan ka dawo ka same shi can cikin gari" ta fada tana kokarin zama kan kujerar dake kallonsa sannan taci gaba da cewa "Abubakar akan maganar yarinyar can Ummee inaso inji takamammen damuwarka" ya kurba shayin sannan yace "babanta ne bayasona" Anty tace "kayyah! To meyasa bazaka kyale masa yarsaba babanka fa jiya har cikin dare fada yake harda maganar dake tsakaninka da Habeeb" kallonta yayi kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace "babu wata magana tsakanina da Habeeb maganar ummee kuma Anty ai kinsan da ita" shuru tayi tana kallonsa harya gama ya mike tsaye yana kallonta yace "na tafi" da kai kawai ta amsa masa har ya fita.
Tun yana karamin yaro ta fuskanci yanada matukar kafiya da jajircewa akan abinda yakeso amma wannan hali da ya tsiro dashi bayan ya girma wannan matsalar itace ta uku kenan ana karawa dashi bayan tun na farkon da har yau ba a shawo kansa ba.
Ummee kuwa bata fito ba sai karfe goma shima saboda tana da lectures 12 to 2, sha daya ta kammala shirinta tsaf sannan ta fito da niyyar wucewa makaranta a korido dinda zai fitar da ita babban palon gidan taci karo da momy, murmushi tayi tace "momy ina kwana" bata rai tayi tana kallonta tace "wane irin hali zaki kuma nunawa ummee? Daddy zaiyi tafiya na kwanaki amma ki kama kofa ki rufe waya ma a kashe ya tafi cike da damuwa akanki meyasa zaki haka" shuru ummee tayi tana kallon kasa batayi magana ba mommy tace "Allah ya kiyaye sai kin dawo kuma don Allah a kula kinji" gyada mata kai kawai tayi ta wuce.
Kamar ansan zata fita aka wanke motar sai kyalli take tana zuwa ta shiga sannan tayi addua ta tada motar koda taje skul din ma ta samu sauran course mate dinta cikin hall din suna jiran malamin baizo ba, Inda ta hango kawarta ta nufa tayi mata sallama, Ameera ta kalleta tana amsawa tareda harararta tace "meya samu wayoyinki" karamin tsaki tayi tace "ra'ayina yasa na kashe" shuru sukayi su duka har akayi awa daya malamin baizo ba ta mike tsaye tana cewa "ameera pls muje idan da Abu mai sanyi kibani nasha a motarki" key ta mika mata tana cewa "idan kin dauko ki dawo min da key dina" gyara tssyuwarta tayi tace "ameera ba gida zaki bane saura mishi minti arbain fa" mikewa tsaye tayi tana cewa "are u Ill? It seems you are not OK" saida suka karasa jikin motar ameeran sannan ta dan Shafa fuskarta tace "akwai matsalane amma komai yakusan zuwa karshe insha Allah" Ameera ta girgiza kai tana cewa "ummee komai awurinki sirri ne wace irin matsala ce da bazaki iya fadamin ba" dan murmushi tayi tace "akan sadeeq ne da Daddy ya hana kuma kinsan I can't do without sadeeq I can't even imaging my life without him, bawai boye miki nake ba kawai nasan kema yadda na rasa mafita haka zaki rasa so tsayawa nanata zancen bata lokaci ne" gyara tsayuwarta ameera tayi bayan ta dauko ruwa amotar tace "lallai kam sedai kici gaba da Addua ki kuma bi daddy a hankali, jiya naso muyi magana sai naga kina tare dashi ga yamma tayi Jabir zai dawo daga Ukraine gobe so yace awurina zaici dinner shine nake so ki fada min abinda ya dace na saka ayi masa"
Numfashi ta sauke tace "ki saba da girka masa Abu da hannunki mana Ameera sai kace ba mace ba, zanzo in tayaki karki damu idan na gama tunani zan kiraki sai harhada komai da za a bukata" rungumeta tayi sukayi sallama Ameera tana biye da motar ummee har suka fito daga skul din sannan suka rabu.
Tana shiga unguwarsu saita zaga tabi ta baya wata zuciyar naso ta hanata abinda tayi niyya amma kuma sai ta kafe har ta isa wurin tayi parking.
*jini yafi ruwa kauri*
*FIYYAH*
YOU ARE READING
JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)
Fanfictionlabarin ya kunshi soyayya da k'iyayya ya kunshi Arziki da talauci.