*Safiyyahgaladanchi*
*JAJIRTACCE ABUBAKAR SADEEQ*
*SHAFI NA TALATIN DA BIYU*
Har wani security ya taso yana hargowa Samuel ya rike shi yana cewa "ka kyaleshi bayan haka ma matarshi ce ina ruwanka"? Komawa yayi yana magana kasa-kasa.
Ummee tace "ka sake ni mana baka ganin mutane awurin nan ne" kasa magana yayi sai jera ajiyar zuciya yake ji yake kamar zai mutu, duk matsalar da aka samu ya dauki laifin karanka kaf ya dora mata, itace batasan mutuwa zaiyi ba da ace bai ganta ba yau. Hannunshi ta rike har zuwa cikin gida palonsu na kasa da kowa yake zaune ana jiran abinci ta shiga dashi, dukansu kallonta suke har matar haidar da Ibrahim tsayawa tayi dashi yagaisa dasu yana jin duk ya tsargu da irin kallon da suke mai seya hade rai ya sake tamke fuska kamar bai taba yin dari ba. Sama tana shi sai lokacin yake cewa "ina zaki dani"? Seda suka kai wata kofa ta sake mai hannu tace "ka jirani minti daya" ta wuce part dinta ta dauko wata jaka brown kamar folder amma tana da zip tayi kyau sosai sannan tace ya biyo bayanta bayan da sallama suka shiga, tun daga irin kallon da daddy yayi musu ta fahimci wani abu na farko jikinsa a sanyaye yake na biyu kamar yaji dadin ganin sadeeq din a wannan lokacin amma sai na lyi tunanin kodan kasancewar babban abokinsa ne awurin aboki tun suna yara Alhaji bala wamakko.
Saida muka durqusa muka gaidasu sai naji daddy yace "yanzu nake shirin kiranki ki hadani da mijin naki" Alhaji bala yace "haba Muhammad? Menene aibun wannan yaro"? Ke kuma ummee banyi tunanin haka daga wajenki ba ya zaki baro gidan aurenki a lokacin da kowace mace take burin samun ladar aure a wata mai albarka wallahi naga laifinki ba kadan ba tun shekaranjiya danaji wai kina gida daga wurin babanki niyyata idan nazo in dauke ki da lafiyayyun maruka amma sai na samu ma ashe harda ciki ajikin ki" ummee ta sauke kai kasa tace "kayi hakuri baba nima bada son raina hakan ya faru ba, kaga dalilin daya saka na bar gidanshi a lokacin" tareda mika masa takardun sadeeq yabude ya dubawa ya mikawa daddy cike da mamaki daddy ya kalli sadeeq yace "ya zakuyimin haka ummee"? Tana murmushi tace "laifinsa ne daddy yayansa ne yayi sponsoring dinsa a karatun amma sai aka samu matsala saboda yaki auren kanwar matar yayan nashi har abin ya zama fada a tsakaninsu shine sai yayan yayi masa magana kamar gori yana nuna masa duk wahalar da nayi dakai bai kamata kayimin haka ba shikenan fa sai ya dauki fushi ya ajiye komai ya shiga wahalar rayuwa Daddy duk iya shekarun nan iyayenshi sunyi sunyi sun kasa shine mahaifiyarshi ta rokeni in taimaka musu saboda duk sana'ar da yake taci baya sosai daga a sace kudi sai wurin da yake ajiya ya kone nayi mata alkawari sannan nayi fushi dashi na tsawon lokaci saboda yaki amincewa daga karshe mukayi fada wanda iya shine ransa yake baci nikuma biyan bukatata ne saboda nafiso na tunzurashi din dan yayi tunanin amsar bukata ta sai yaki shiyasa sai mamanshi ta bani shawara akan inbar masa gidan sai na tsaya jiran dalili shine sabanin da muka samu ranar dana dawo gida amma yanzu kallo daya nayi masa nasan ya yadda da abinda nake bukata" Alhaji bala yayi shuru yana kallon sadeeq da duk ya gama lalacewa ya rame saboda wahala yaja karamin tsaki yace "menene amfanin iliminka? Gori makale maka zaiyi? Dan uwanka ne fa idan babu babanku shine zai maye maka gurbin babanku ka kiyaye rayuwar duniya ba a daukarta da zafi yadda ka dauketa" ya juya wurin ummee yace "kin kokari wannan mijin naki akwai shi da zuciya da kafiya amma irin haka saiki sanar da abinda ya faru" Daddy har lokacin yana kallon takardun yana tunanin a wane kamfanin sa zai ajiye sadeeq sannan a wane mataki da gurbi ummee ta katse masa hanzari tana cewa "Daddy ka bani takardun zamuje gidan yayan nasa ne" har zaiyi magana sai alhaji bala yayi masa nuni daya basu, mika musu yayi suka fita.
Ya sake kallon daddy yace "bari in fada maka arziki ba hauka bane, naji abubuwan daka sa yaran nan a gaba kana yi musu ina jiye maka ranar da yakumbu zataji wannan maganar nasan ko dukan ka zata iyayi, ka kyalesu sannan ka taimaka musu, ka manta da halaccin zainab a gareka mahaifiyar ummee ka manta soyayyar da kake yiwa ummee bayan mahaifiyarta tabar duniya ya zaka juya mata baya kai tsaye banji dadin abinda kayi ba mutum mai girma kamar ka da hankali ga ilimi bai kamata ace yayi haka ba" daddy dai duk jikinsa yayi sanyi dan tunda yaso raba ummee da sadeeq bai samu wanda zai fada masa gaskiya kai taye ba sai yau.Ummee da sadeeq suna fita daga palon ya rike mata hannu ya matse da hannun shi a rike ta shiga part din ta ta dauko key din mota tareda wayarta har zasu fito tace "kaga part dina, kaga dakin karatuna can kaga wanda kayana suke ciki kaga inda nake wanka da sauran su sai wanda nake kwana aciki musamman lokacin zafi" yayi murmushi yana cewa "yayi kyau sosai amma taimakeni mu kafa tarihi acikin palon nan" yana gama fada ya hade bakinsu, ko iya nan aka tsaya sun tabbatar da missing juna da sukayi, jiki a sanyaye suka fito tana kallon yan uwanta tace "yaya zamu dan fita yanzu ba dadewa zamuyi ba" yayi dariya yana kallonta yace "ashe bikon ba wuya harkin hakura"? Tayi dariya tana cewa "ni dama jinya nazo kuma naji sauki komawa zanyi, idan momy ta tashi dai a fada mata karta nemeni bana nan" sai lokacin matar haidar tace "wai dama yaji tayi" Haidar ya girgiza kansa yana cewa "A'a jinya dai tazo yi saboda batada lafiya mijin kuma baya zama" badan ta yadda ba ta gyada kai tana cewa "Allah ya bata lafiya".
Itace take driving yana nuna mata hanya har suka isa gidan, saida ya dake ya iya shiga gidan tareda sallama ummu matar Habeeb tana zaune tareda yaranta tana ganinsu ta tashi tsaye tana murmushi tace "Ahh yau za ayi ruwa da kankara sadeeq a gidan nan sannunku da zuwa" zama sukayi suna gaisawa yaran duk suka koma wajenshi suna yimai magana lokacin habeeb ya fito cikin farar shadda yana gyara zaman hularshi yana kallonsu ya saki murmushi amma sai yaga sadeeq ya kasa kallonshi ya amsa gaisuwar ummee yace "na gane ke kika kawomin kanina har gida yau dole nayi miki babbar kyauta" tayi dariya tana cewa "shine yace inzo mu tafi ziyara" hannunsa habeeb yaja suka fita yana cewa "bari nayi sirri da kanina" ummu tayi dariya tana cewa "dama babu ruwanmu tare muka ganku"
Wata kofa ya bude ya shigar dasu palon ya zauna yana kallon sadeeq yace "Allah yasa zuciyata tayimin tunani mai kyau akan ka yau ka fadamin abinda kunnuwa suka dade suna so suji" sadeeq ya rasa ta inda zai fara sai yace "kayi hakuri, nayi kuskure" Habeeb yayi saurin tare shi yana cewa "na fahimta kayi hakuri dama duk shaidan ne ya shiga tsakani insha Allahu komai ya wuce, ina abun"? Waje ya nuna masa suka fito tare suka nufi wajen mota ya bude habeeb yace "kaga wannan karon motarka nasa aka zo da ita tunda kaki karba na fara amfani da ita" dakyar yayi murmushi yana mika masa jakar yace gashinan sai ya mika masa key din motar yace "to karbi motarka tunda mun shirya yanzu babu fada, dan Allah sadeeq ka rage zuciya musamman ga yan uwanka rayuwar duniya ba a tsaurarawa ko shawara baka nemana anjima kazo muje wajen Abba da Anty zamuyi magana" ya gyada masa kai shiga gidan sukayi yana cewa ta tashi su wuce dan niyarsa ya tafi gidansa da ita ya samu abinda ya samu sai tari ya sarke shi tun yana iya yi daga tsaye har ya kasa yakai zaune sai jini suka gani yana fita daga bakinsa ummee tayi kansa ta rike shi tana shafa bayanshi.
YOU ARE READING
JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)
Fanfictionlabarin ya kunshi soyayya da k'iyayya ya kunshi Arziki da talauci.