*Safiyya galadanchi*
*JAJIRTACCE ABUBAKAR SADEEQ*
*SHAFI NA TALATIN DA UKU*
Goge bakin yayi da hanky din da ke aljihunsa yana kokarin mikewa Habeeb ya rike shi yana magana da jabir zaunar dashi yayi gefe yana cewa "wai me yake damunka har haka kake tari da jini" dakyar yace "ulcer din nan ne fa na dade bansha magani ba kuma da akayi azumi naso in siya amma banida kudi haka nayi azumin babu magani" habeeb yayi tsaki yana cewa "baka kyautaba wallahi, bari jabir yazo tareda Dr dinnan ya duba ka" basu dade ba ya karaso magunguna ya kawo masa yana cewa "kasan fa tun farko saida na fada maka karkayi wasa tundahar takai haka zai iya zama babbar matsala" shuru yayi yana shan maganin batareda ya kulasu ba wani daki habeeb ya kaishi ya kwantar dashi yana cewa "kawai ku kwana anan" yanaso yace masa ummee ba gida take ba yana jin kunya saida ya fito yana fada mata tace "to ni bari in koma gida dan yanzu momy ta kirani tana ta fada nafita na dade har haka" zama yayi yana cewa "kirata ki bani dan gaskiya bazan bari ki tafi ki barshi ba, bayan haka ma kina gidanki ai ba ruwan momy da inda kika kwana tunda tare da mijin kike" batayi magana ba dan ta lura da baisan abinda yake faruwa ba,mika masa wayar tayi tanaji yayiwa momy bayani ta karbi wayar momy tana cewa "ina na taba ji anyi biko haka? Daga fita anguwa sai ki gudu wajen miji, to Allah ya bashi lafiya mai amfani" tana gama fadin haka tayi mata sallama, dakin da aka kaishi ta shiga yana kwance gefen gadon yana danna waya yace "zo kiji" ta tsaya daga bakin kofa tace "fadi inajinka" shuru yayi ya kyaleta ta sake cewa "kaji"? Yace "idan kinason kiji ki matso idan bakiso kici gaba da tsayuwa anan" ta karasa kusa dashi tana cewa gani ya ajiye wayar yana cewa "dannamin kirjina zafi yake min" tayi dariya tana cewa "bari na samo maka madara dai dannawar ba amfanin da zaiyi" tana gama fadar haka ta fita bata dade ba ta dawo ta kawo masa madarar zuqa biyu ya shanye yana cewa "wallahi naji kamar bansha komai ba nidai su bani abinci yunwa nake ji" ta sake fita ta dawo dauke da tray tana cewa "ni yanzu dani dakai waye zaiyi jinyar wani, na fara gajiya dama yanzu ba jurar aiki nake yi ba" ya sauka daga kan gadon yana janyo tray data ajiye gabansa baiyi magana ba saida yayi rabin plate din yace "kiyi jinyata yau zan baki maganin da zaki warke" kallonsa kawai take batayi magana ba har ya cinye abincin ta zauna kusa dashi tana cewa "kayi hakuri bansan kanada ulcer ba na tafi na barka" hannunsa ya dora kan cikin ta yana murmushi yace "jeki na yafe miki Allah ya ssukeki lafiya, nima kiyi hakuri da halin dana nuna miki ummee ko kadan baki cancanci irin wannan rayuwar ba, abinda nayi miki ban kyauta ba, nasan kinaso na badan wani abu na tare dani ba saboda kinsan banida komai har kika baro daular dake gidanku kika bini, agidana kinci abincin da koni nasan bazaki iya ci ba ban nuna miki haka bane saboda gara kici akan ki zauna da yunwa, bansan na tafka kuskure ba saida na barki kika tafi wallahi inkika sake yin nisa dani irin haka bansan abinda zai faru daniba" hannunta ta dora kan nashi tace "rashi yana saka bakin halaye zuwa uzurin da nayi maka kenan, nasan duk yadda zan kai ga takura ban kaika ba kaida nauyina yake kanka, nima ba a son raina na tafi ba, nasan idan nayi haka dole kayi abinda nakeso sannan kuma yanayin ciwon danake dole ina bukatar kulawa kaikuma bakada wannan lokacin saboda bakada kudi da magani zakaji koda abinci kokuwa da zaman jinyata bayan duk sai ka fita hakan zai samu shiyasa na tafi kaga Daddy kullum saiya dubani sannan idan ina ciwo baya bacci amma bansan zaka iya zama da yunwa saboda rashina a kusa ba wallahi da ban tafi ba, ulcer da aman jini akwai hadari sosai" shuru yayi yana sauke ajiyar zuciya, dakanshi ya fara bata abincin tana karba dukda bata so saida ta cinye shi duka ya kauda plate din gefe yana kokarin hade bakinsu.
Habeeb ya dawo yana cewa ummu "kin duba jikin sadeeq kuwa"? Ta girgiza kai alamar a'a ransa ya nuna ya baci tace "maida wukar ranka ya dade shida matarshi suna daki idan na shiga na katse su fa" yayi gajeren tsaki yana cewa "an fada miki kowa irinki ne? Ciwo yake fa meya hadashi da wancen maganar" tayi dariya tace "to ayi hakuri muje mu dubashi tare" kwankwasa kofa sukayi lokacin ummee ke saka kayanta tayi saurin daura dankwali ta yafa gyalenta ta bude kofar tana matsawa gefe tareda gaishe su habeeb ya shiga dakin ummu na bayansa yana cewa "kaji sauki kenan amma duk da haka bazaka bar gidan nan ba sai safe" ya tashi zaune daga kwancen da yake yana cewa "nasani ai nan ma dana kwanta da bacci zanyi dan tun dazu idona biyu" habeeb ya zauna yana cewa "Allah ya kara lafiya, ka bani key din gidanka za a kwaso kayan gidan nan adawo dasu nan wancen gidan kuma daga baya sai asan yadda za a yi dashi" sadeeq yayi shuru yanaso yayi magana amma ya kasa cewa komai dan yaga yadda yayan nashi ke rawar kafa akan dawowansu kamar da sai ya kakalo murmushi yace "yadda kakeso haka za a yi" ya kalli ummee yace "maman baby sannu fa ansakaki jinya kema gashi kinaji da jikin ki, kiyi hakuri " kunya taji tace "ai ni naji sauki dama rashin cin abinci ne kawai yanzu kuma komai inaci" ya gyada kai yana cewa "to ki biyo ummu ki karbo muku abubuwan bukata" fita sukayi tabi bayansu har suka shiga wani daki saita tsaya a waje leda biyu ummu ta fito dasu ta bata daya ta raka ta da daya.
Kayan bacci ne aciki sai jallabiya da inner wears ta zaro ido tana cewa "Allah yasa ba yaya bane ya siyomin" yayi dariya yana cewa "ai matarsa bata fiki ba kila da jikinta ya kwatanta" ta harareshi kawai tana ciro masa nasa kayan baccin.Washe gari lafiya lau ya tashi karfe bakwai koda ya duba ummee bata dakin , lokacin tana can kitchen tareda ummu mai aikin kuma tana yiwa yara wanka abincin breakfast suka hada sannan suka dafa wanda zasu tafi dashi gidan Anty, sai sha biyu suka bar gidan Anty tana ganinsu a tare taji wani sanyi aranta saita taresu kamar baki, meat pie da cake dinda tayi duk ta kawo musu tareda naman kaji tana ta hidima dasu yan jikokanta kuwa sai binta suke duk inda tasa kafa, laila ta shigo palon tana cewa "anty ummee ko in miki wainan fulawa" ummu ta rigata yin magana tana cewa "kiyi dani don Allah inason abin nan idan nayi bayamin dadi nafison na wani" anty tayi dsriya tana cewa "badai kwadayi kikeji ba dan ga abubuwa nan Allah ya raba lafiya" habeeb ya sosa kai yana cewa "ai Anty batada komai tace ta gama haihuwa" yana rufe bakinsa Abba na shigowa suka durkusa tare suna gaidashi.
YOU ARE READING
JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)
Fanfictionlabarin ya kunshi soyayya da k'iyayya ya kunshi Arziki da talauci.