JJT 9

10 0 0
                                    

*Safiyyah Galadanchi*

*JAJIRTACCE ( ABUBAKAR SADEEQ)*

*shafi na tara*

Bai samu karasawa cikin gidan ba ya zauna nan tunanin rayuwa da yadda ta juye masa kawai yake wallahi ya yadda da Allah shine ya halicce shi da duniya tareda abinda yake cikinta amma da sai yace kamar baya jin dadin duniyar. Dafe kansa yayi yana tunanin kalar wahalar da yayi yau gaba daya jikinsa ciwo yake masa dakinsa ya koma ya shiga ko abinci bai nema ba haka ya kwana washe gari da zazzabi ya tashi sosai amma hakanan yayi shirin fita ya kunu da kosai Anty tayi musu kosai guda daya yaci sai kunu yasha Rabin cup tareda pcm sannan ya fita, hakanan yaketa yawo acikin gari jikinsa a sanyaye, duk Wanda ya tare shi iyakacinsa dashi "ina zakije ko zaka je" idan sun fada sai yace "mu tafi" idan ya saukesu suntambayi kudinsa seyace "ki kwatanta kawai" dama mostly haka yakeyi musamman idan tafiyar ba mai nisa bace.

Kusan magrin yaji jikinsa har rawa yake saboda zafin zazzabi sai yakama hanyar zuwa gida ya kusa shiga layinsu shidai baisan takamammen abunda ya haddasa abinda ya faru ba sai ji yayi adaidaita sahun ta juye dashi ya daki wani Abu da karfi daga nan kuma sai yaji ana cewa innalillahiwainnalilaihirajiun rufe idonsa yayi yana sauke numfashi daga nan baisan abinda ya faru ba sai washe gari.

Tun safe take kiranshi bai daga ba yayi mamakin hakan jikinta duk yayi sanyi tace kodai wayarsa ya manta da ita ya fita ne, haka take ta sak'e sak'e har kusan magrib taji kanta yana ciwo sosai alamar harda zazzabi yana son kamata kallon kanta tayi a mudubi taga kamar ta rame idonta sunyi wani iri tayi dariya mai sauti tace a fili "wuni daya kawai shine harda zazzabi? Lallai Kalmar hakuri ta tabbata akan dady duk ranar daya rabamu to koda banbar duniya ba rayuwata zata kare ne a asibiti tsawon rayuwa..." Bata karasaba wayarta tayi ringing tayi saurin dubawa taga sunanta murmushi tayi sannan tayiwa wayar hararar wasa kafin ta daga sai taji anyi sallama da wata muryar daban tadan gyara tsayuwar ta tana amsa sallamar hakanan gabanta yaringa faduwa "Dan Allah muna magana daga gidansu mai wayar nan ne"? Tayi saurin amsawa da eh mutumin ya sake cewa "to dan Allah azo a daukeshi yayi accident ne yanzu nan kwanar gidan gwamnati" jikinta har yasoma rawa tace "innalillahi yanzun nan za a zo" mayafinta kawai ta dauka ta fita da Sauri daga gidan mommy tabi bayanta da kallo tana cewa "ummee lafiya"? Daga nesa ta amsa ta tana cewa "momy ba lafiya ba wallahi" securities din gidan ma duk saida ta rudasu kafin su bude mata gate suka bi bayan motar da kallo mommy ta biyo bayanta da kafa tana cewa "meyasa zaku barta ta fita a haka" duk sukayi shuru ta sake daka musu tsawa "kubi bayanta idan wani Abu ya same ta fa? kun tsaya kuna kallon mutane useless kawai" ita dinma jikinta rawa yake tana tsoron abinda zai samu gudaliyar ummeensu.

Komawa cikin gidan tayi ta dauki waya tayi kiran Daddy.

Yadda taga an daukeshi ansaka mata shi a mota duk sai ta rasa abinda zatayi komai nata tsayawa yayi wani irin sanyi takeji har kasusuwan ta ta tabbatar bazata iya driving ba takalli daya daga cikinsu "Ku kaimu asibiti Dan Allah" ta fada tana kara hannunta  wurin hanncinsa har zata shiga motar saita fasa ta karasa wurin adaidaitan da aka daga amma duk ta yamutse key din ta cire ta bude safe din ciki ta kwaso kudin gaba daya ta gansu a tsare amma sunada Dan yawa Dan har seda aka danna safe din ya kulle, bayan motar ta bude ta sakasu sannan tashiga ta zauna, wani matashin saurayi ne yaja motar yakaisu wata private hospital da SAHEL saida aka shiga dashi tana tsaye tukunna ta kalli saurayin tace "nagode sosai amma muje wurin mota" yabiyo bayanta har suka Isa bude motar tayi ta dauko kudi tabashi tana yi masa godiya Dan shine ya fara ganin abinda ya faru kuma yana wurin harya taimake su da farko kin karba yayi saidaga baya sannan ya tafi yana yi masa addua. Wayarsa dake hannunta ta karba tana kokarin kira taga gardawan gidansu bisa kanta ta tsuke fuska tace "menene haka"? Daya daga cikinsu yace "Hajiya tace abiyoki" albarkacin Hajiya yasaka tayi shuru sannan tayi tsaki tana jin wayar ana fada mata Minti daya yarage, motar ta koma ta dauko wayarta tayi Kiran.

Lokacin Anty tana zaune tsakar gida tana tuka tuwo wayar tayi ringing tace "laila miko min wayarcan naga wane Dan albarka ne mai kira haka goshin mangariba" sai taga number basuna dagawa tayi tana sallama ummee ta amsa tana cewa "Anty ummee Ce Dan Allah kusamemu a asibiti sahel yanzu akwai yar matsala" gaban Anty yayi mummunar faduwa ta saka murfi ta rufe tukunyar ta kalli laila tace "dauko hijabinki da nawa fito da mukullin gidan nan arufe" laila daga yanayin da taga Anty ta dauki wayar ya saka ta gane akwai matsala sai ta yi abinda Anty ta sakata da sauri, fita sukayi daga gidan suna Neman adaidaita sahu.

Momy kuwa Daddy tayi kira ta fada masa halin da ummee ta fita sai kashe wayar ya kira usman yana dagawa yayi sallama dady ya amsa yace "ka kira su Joseph su fada maka inda ummee take idan sun cimmata, kaikuma kayi saurin kirana" yana tare da manyan abokanansa a lokacin suna tattaunawa akan abinda ya shafi kasuwancinsu. Bayan mintuna biyu ya sake yana cewa "tana ina" usman ya girgiza kai yace "Sahel Daddy" kashe wayar kawai Daddy yayi ya mike tsaye yace ayimasa uzuri yanada family issue ya fita da sauri.

Mukarrabansa da securities dake tare da shi suka rufa masa baya mota uku sannan tashi.

Kasancewar babu yalwar adaidaita sahu a layin ya saka Anty bata Isa da wuri ba tana sauka saiga wasu motocin da bata San masu su ba ta lalibo waya tana kokarin kiran ummee sai taji ummee na cewa "Anty" ta juyo da sauri kafin ta amsa sai taji daddy na cewa "me kike yi anan Ummee dukansu suka juya suna kallonshi.

*Jini yafi ruwa kauri*

*Fiyyah na gaisheku"

JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)Where stories live. Discover now