JJT 37

18 0 0
                                    

*SAFIYYA GALADANCHI*

*JAJIRTACCE ABUBAKAR SADEEQ*

*SHAFI NA TALATIN DA BAKWAI*


ummu ta juya zata shiga daki ummee ta rike ta tace "dan Allah mu tafi bakusan me nakeji ba" ummu tace "Abinda nake dashi zan dauko karmuje asibiti ya kasance haihuwa ce ba komai a hannu" sakin ta ummee tayi ta shiga daki da sauri koda ta fito har sun shiga mota ta zauna gaba tana kokarin kiran habeeb, yana dagawa yace "ya akayi wai na fada miki banson kina kirana idan ina wurin aiki ba dazu mukayi magana ba kika ce su ummee sun iso ba" kasa magana tayi saboda yadda ranta ya baci kawai seta kashe wayar tanaji yana ta kira taki dagawa sadeeq ko baima san abinda yake faruwa ba hankalinsa na wurin matarshi dayake yawan juyawa yaga halin da take ciki, asibitin ma duk sai yaga tayi masa nisa yanzu.

Suna isa aka shiga da ita, shuru shuru sai wata nurse ta fito wai abada kayan baby, sadeeq ya kurawa ummu ido yaga ta mika wata yar karamar jaka bayan mintuna talatin sai gashi ankirasu daga ciki babyn aka nuna musu sannan aka wuce dashi ciki za'a sashi incubator saboda dan wata bakwai ne sai sun gama bincike idan yakamata abasu shi, nurse din tana dawowa sadeeq ya tareta yana tambayar ya jikin uwar, saida tayi murmushi tace "yanzu za a fito da ita dinki ake mata" ya zaro ido yana kallon ummu zaiyi magana tace "bakaga babyn duk da bekai lokacin haihuwa yanada dan girma ba, ta samu kari ne dole za a dinke" duk da bai ganeba amma se ya girgiza kai sunfito kenan saiga Habeeb ya shigo mai aikinsu ta fadamai sun wuce asibiti da matar sadeeq, har ya iso yana magana da sadeeq ummu bata ko kalle shi ba amma hankalinta yana wurinshi taga kafar shi daure da bandage.

Suna haka ummee ta fito da kafarta zani ne daure a jikinta sai hijab fuskarta ta dan kumbura kadan ummu tayi saurin mikewa ta bata kujera ta zauna tana cewa "ba daki zasu baki ba meya fito dake" seda ta gyara zamanta tace "Eh Dr din yana fitowa yanzu bana son zama dakin ne" Habeeb ya matsa kusa da ita yana yi mata sannu yace "kunsanar a gida"? Sadeeq yace a'a yayi karamin tsaki ya janyo wayarshi daga aljihu Daddy ya soma kira suka gaisa cikin mutunci ya fada masa aikuwa yayi murna sosai kuma yace gasunan zuwa, baisan abinda ya faru ba da sadeeq yazo sokoto dan haka da karfinsa yakira anty yana fada mata ta hau fada inda take shiga ba nan take fita ba ta kuma shaida masa ya gaggauta maida ummee sokoto tunda gashi babba acikinsu ya barsu suna hauka da shirme.

"Anty bata yadda bane da zaka dauko yarinyar nan"? Sadeeq yace "tayi fada ta hanani nazo da ita sai Abba yace ta kyalemu, dama nasan intaji setayi fada" girgiza kai habeeb yayi sannan ya maida kallonsa wurinsu ummu suna magana ummee ke cewa "yunwa take ji" ummu tace "bari sadeeq yaje ya sama miki abinda zaki ci" zuwa tayi wurinsu ta kalli sadeeq tana fada masa ummee najin yunwa habeeb ya kalleta yace "ke kinci abincin ne" ta amsa masa batareda ta kalleshi ba.
Sadeeq ya juya da sauri ya fita gidan ya koma dan ya dauki kayan da ummu ta lissafa masa.
Habeeb ya kalli ummu yace "wai wannan cin maganin fa" saida ta kalli ummee taga su take kallo sannan ta bashi amsa tace "ba dole inci magani ba, tun ranar dakace bakason kana aiki ina kira bansake kiranka ba to meyasa bazaka yimin uzuri ba, idan da banajin maganar ka yanzu duk hakurin da nake dakai baka gani duk abinda kace shi nakeyi amma kuma baka yimin uzuri, kaci gaba watarana zaka neme ni baka ganni ba wallahi" rike mata hannu yayi yace "kiyi hakuri idan munje gida zamuyi magana yanzu ki kula da mai jegon can, ni bari naje na kawo kayan baby tunda haihuwa tazo babu shiri" da to ta amsa masa ya juya ya fita, tana zuwa ummee tace "kalli kiga har zanin jikina ya jike" ummu tace "abin mamaki ni dayake gidanmu ba a taba haifar bakwaini ba bansani ba hakan ko normal ne bari a tambayi likita" ummee tace "nima bantaba gani ba sedai inji labari, wai a haka danaji wannan azaba babyn bai gama girma ba, gaskiya na gaida mata" dariya sosai ummu tayi, suna nan zaune suna hira har sadeeq ya dawo yayi magana da Dr aka basu daki acan ta zauna taci abinci sosai, duk yana zaune se mamaki yake wai ummee ce ta haihu, wuri ummu ta basu tace zatayi wayane kamar jira yake ta fita ya koma kusada ummee ya zauna yace "ina yake miki ciwo"? Saida ta yamutsa fuska ta nuna masa da hannu, rungumeta yayi  yana cewa "kiyi hakuri insha Allahu zaki ji sauki, bude ingani ko wani abin ne in fadawa Dr" dariya tayi tace "sannu fa, to babu abinda zan bude maka" yayi murmushi yace "naga kinyi min wayo babyn dake yake kama" tabe baki tayi tace "nifa ko ganinshi banyiba" ya shafa kanta yana cewa "nasan zasu kawo shi ki ganshi ai naji ummu tace baikai sauran jariran  da ake haifa wata bakwai kankanta..." turo kofar da akayi yasashi saurin sakinta ya matsa daga jikinta, sallama mommy tayi ya amsa yana mikewa tsaye sai yaga dady a bayanta, durqusawa yayi ya gaishesu Daddy ya riko kafadarshi ya mikar dashi yana dariya yace "ahhh karkasa yaron nan ya zama soja nan gaba yasa a kulle ni a guard room" Dariya momy tayi tace "har ka tura musu shi soja kuma" yayi dariya yana riko hannun ummee yace "sannu yajiki, ashe dan Abuja ne acikin seda ya koroki kika dawo nan sannan ya fito" kunya taji ta sauke kanta kasa tana gaidashi ya amsa yana cewa "zo ka raka ni naga likitan nan naji ya yaron yake" sadeeq yabi bayansa suka fita, momy kuwa wuri ta samu ta zauna tana kallon ummee tace "yau kinji yadda ake ji ko? Babu dai inda yake miki ciwo"? Ta amsa da "Eh sedai wannan abin yanata zuba sai karni nake yi" momy tace "to Alhamdulillahi yaro ya samu abinci da wuri kenan Allah ya kara muku kafiya ku duka".

Anty tayi masifar duniya bakinta seda yayi tsini amma Abba yace tunda ance saita dawo za a yi suna bazata bisu Abuja ba dan ya lura yadda taketa cika tana batsewa idan taje duk sai rayuka sun baci.
Saida jaririn yayi kwana hudu suka bada shi tareda sharuda da kuma hanyoyi na kulawa, a ranar suka dawo sokoto itada ummu da momy a jirgi sadeeq kuma sai daren suna zasu zo tareda habeeb saboda yanayin aiki.

Da isarsu sadeeq yakira wayarta ya musu ya hanya tare da cewa "kinajin dai abinda Dr yace ba a son yaron nan yana shan iska sosai sannan kuma kar a yawaita daukarshi inba shayar dashi zakiyiba kema kanki yakamata ki kula" tana rungume da babyn tace "yanzu idan ana son ganinsa saina hana gaskiya ina jin kunya sedai inbawa momy waya ka fada mata dakanka ita saita hana" tsaki yayi yace "gatse kike min ko me, ya ina fada miki magana kina cewa in fadawa momy, momy ce ta haifi yaro ko ke? Don Allah karki batamin rai kuma kinji na fada miki kar inji ance ga wani dalili dayasa yaro bashida lafiya, ki kula  dakanki da shi din" dakyar ta amsa masa da to saboda haushin sa ta kalli ameera da isowarta kenan tace "abu yakai ga ma'iya kowane irin iyayi yanzu se anji angani"...

*Fiyyah na gaisheku kuma tana baku hakuri*

JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)Where stories live. Discover now