JJT 28

7 0 0
                                    

*Safiyyahgaladanchi*

*JAJIRTACCE ABUBAKAR SADEEQ*

*SHAFI NA ASHIRIN DA TAKWAS*

Ba karamin tashi hankalinsa yayi ba yakamata ya matse ta jikinsa yana bata hakuri tana kuka tace "dan Allah to kabarni naje wurin momy takaini asibiti" cikin bargon ya sake janta ya rungumeta sosai yana cewa "hakan bazai yuwuba kin manta na daukar musu alkawarin kula dake" shuru tayi masa tana sauke ajiyar zuciya kafin wani lokaci har tayi bacci, shiryawa yayi ya fita duk da yadda yake ji ajikinsa  kasa yin nisa yayi ya dawo dan baima san abu guda dazaiyi ba.
Daya dawo ya sameta ta tashi tayo wanka yajiki yayi mata ta amsa masa ciki-ciki duk sai ya kasa sakewa yakoma dakinsa sai yamma ya fito ya sameta ta dawo palo ta zauna zama yayi kusa da ita yana taba jikinta yace "zazzabin ya sauka bakyajin ciwon komai" kai ta gyada masa tana cewa "awaran unguwarsu ammee dai nake so naci idan da hali ma inason wainan fulawa" tashi yayi ya shiga dakinsa kayansa na wanki ya ringa lalubawa yana duba alhunsa ya samo naira sabain a daya, daya aljihun ya samo hamsin fitowa yayi yanata jin dadi ya fita yana cewa "bari na karbo miki" tabi bayanshi da kallo yanata sauri slippers ne ma a kafarshi da kafa ya isa gida koda ya shiga Anty bata nan sai laila kawai kudin ya bata yace ta siyo awara inda ake siyarwa bata dade ba ta dawo ta mika mai leda yace "akwai kayan da zaki hadawa ummee wainan fulawa" tace "ai kitchen daka sameni shi nake kokarin soyawa kafin anty ta dawo" yace "dan saka akula bada yawaba na tafi dashi nasan tana so" tayi yadda yace ya kama hanya kamar yadda yazo da kafa haka ya koma koda ya isa ana sallar magrib kallon kafafuwansa tayi taga sun danyi kura amma batayi magana ba ta karbi kulan hannunsa tana godiya ya tsaya kallonta daga tsaye ta soma ci, ta dan rage sauran ta mika masa ya girgiza mata kai yana cewa "kici abinki na koshi" bayan kuma yana tareda yunwa sosai karasa cinyewa tayi tabi bayanshi kitchen da taga ya shiga ruwa ya dauko zai sha yaga ta bude fridge babu sai ya mika mata na hannunsa karba tayi tasha ta rage mai da hannunta ta bashi ya karasa shanyewa yanaji kamar ya hadiyi miyau saboda tsabar kishi.
Daki ya shiga ya kwanta yana dafe kansa dake matukar yi masa ciwo har baccin wahala ya daukeshi karar wayarshi ta tadashi jabir ne ya dauka da sauri suka gaisa yace "sadeeq shuru kwana biyu lafiya kuwa" ya shafa fuskarsa yana cewa "inafa lafiya gari yayi zafi ga madam babu lafiya" "innalillahi meyake damunta bakada kirki wallahi" sadeeq yayi murmushi yace "bansaniba amma takusa sati a haka zuwa Thursday dai idan nasamu kudi nakeso na kaita asibiti" tsaki jabir yayi yace "amma banyi zaton kai bakauye bane se yau, saboda ciwon ba a jikinka yake ba? Idan laulayi take fa kasan kuwa yadda suke ji" ya kashe wayarshi tareda dan kara gudu dan dama ya dauko matarshi daga gidan su ne yace bari yaji ko sadeeq yana gida suje.  bayan jabir ya katse wayar shikuma ya fita dan ya duba ummee sai ya sameta a toilet tana ta yunkurin amai  yana rike da ita yajiyo kwankwasar kofa saida ya kwantar da ita kan gado sannan yaje ya bude musu kofar yana cewa "ashe dai kana hanya" tsaki yayi yana cewa "ina patient din" daki ya nuna masa sannan ya amsa gaisuwar maman hanan tabi bayan mijinta ummee na ganinsa tayi kokarin tashi zaune yace "A'a yi zamanki dan Allah" ya fada yana sake cewa "fadamin abinda yake damunki kinji" a hankali tace "zazzabi ne da ciwon kai sai amai" ya taba temperature dinta yana cewa "test ya kamata taje ayi mata asibiti amma yanzu naga ta galabaita bari asiyo ruwa asaka mata zataji karfin jikin ta" suna fitowa sadeeq yace "ya zakace asiyo abu bayan banida kudi" jabir yace "zanci kaniyarka wallahi ni kasan bazaka yimin wannan iskancin ba" shuru sadeeq yayi har sukaje suka dawo  maman hanan tace "ni har ina shirin kiranku amai take ta shekawa tun dazu naga kun dade" zama yayi kan bed side ya jona mata ruwan ya ajiye masa magunguna yana cewa amma gobe kuzo asibitin se ayi mata test" sadeeq ya gyada kai yana cewa "insha Allah" a dakin ya kwana bacci rabi da rabi har ruwan ya kare ya cire mata washe gari da sassafe ya shiryata suka wuce asibitin, gwajin farko ya nuna ciki wallahi shi Sam bai yi wannan tunanin ba ummee kuwa dama abinda yake ranta kenan, murna yake tayi har saida ya wuce gidan Anty da ita, anty ma taji dadi sosai saida bataji dadin yadda yarinyar ta rame ba.

Bayan sun dawo gida take magana da ameera tana fada mata wai ciki ne da ita , ameera tayi murna sosai tana cewa "wai kinsan yanzu mammy ta kawo mini kaya wai idan nayi arbain dasu zanyi amfani nace tun ban haihu din bama" dariya ummee tayi tace "kuma fa kayan wahala ne wallahi ni na daina sha ma kwanaki babarshi ta bani ko bude su banyi ba" Ameera ta sake cewa "nima nace bazan sha ba gaskiya zan daiyi jego na kwarai" nan suka dan taba hira bayan sun gama ta bude wardrobe ta dauko kayan ta zauna tana dubawa sam ba abinda tayi tunani bane, takardun sadeeq ne tundaga nursery school da yayi har Jamia ga degree da masters dinsa har takardun service  dinsa kuma duka qualification na degree da masters da first class ya fita bayan haka ma ba a Nigeria ba sannan bangaren daya karanta mai matukar muhimmanci, kuka takeyi tareda dariya tana rungume takardun, da sauri ta harhadasu ta daure a leda ta sake yi musu kyakkyawan boyo robar dake cikin ledar kuma agogonsa ne masu tsada da zobunan azurfa aciki wannan kuma sai tayi shuru dan tasan kayan a hannun manyan mutane maza take ganin suma dai ajiya me kyau ta musu sai taji kamar batada sauran damuwa saidai ta manta da wanene sadeeq din da take tare dashi.

JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)Where stories live. Discover now