*Safiyyahgaladanchi*
*JAJIRTACCE ABUBAKAR SADEEQ*
*SHAFI NA TALATIN DA DAYA*
"lafiya dai ummee"? Mommy ta fada hankali a tashe "lafiya lau momy kafin wani yasan da zuwana yanzu dan Allah zauna in miki bayani kema ki taimakeni" rike hannunta momy tayi dan gaba daya hankalinta ya gama tashi a tunanin ko sakin ummee sadeeq din yayi.
A takaice tayi mata bayani yadda zata fahimta tace kuma "na bibiyi labarin abindabya faru na gane dalilin fushin nasa to yanzu shine nake wannan yakin dan abin nashi yayi yawa, amma dan Allah momy kawai ki nunawa daddy yaji nayi yadda idan ya yadda sai sadeeq ya wahala kafin ya samu kaina" mommy ta shafa kanta tana murmushi tace "kina son sadeeq sosai saboda kina taimakonsa Allah ya kama miki amma mijinki yanada wani irin hali mara misaltuwa da wuyar shaani" gefen kafadar momy ta ajiye kanta tace "ina wahala saboda wannan halin ahakan ma saboda yanada saukin kai idan anzo ta gefena" nan momy ta shiga kwantar mata da hankali bayan ansha ruwa bata iya cin komai ba momy tace "wannan wane irin ciki ne wannan dayake hanaki shan koda ruwa kin kuwa je asibiti"? Ummee tace "naje amma dai ba canji harna hakura nikaina inajin irin ramar danayi".
Daddy yana zauna momy ta gama fada masa yajin da ummee tayi saboda talaucin sadeeq tace ta gaji har ya zabura zaije dakin ya kori ummee mommy ta rike shi tana cewa "tsaya kaji wannan fa dama ce ta samemu yarmu ta dawo karka manta ummee yar gaban goshin mu ce, nasan shirin da zamuyi masa zamuce ko zata koma saiya sauya mata gida ya siya mata mota ya siyawa kanshi sannan ya samu kwakkwaran aiki kaga ko idan bazai iyaba sai ya sauwaqe mata" komawa yayi ya zauna yana nazari batare da yace komai ba.
Sadeeq sai yamma ya koma gidan da yan kayan cefanen shi a hannu sai wani hura hanci yake shi ala dole ga mai gida, yasha mamaki ganin bata gidan gabansa ya fadi sai yanzu yasan yayi kuskure amma zuciyarsa ta kasa yadda yaji tayi masa a yau da ake shirin kai azumi na farko, zama yayi har aka kira salla dakyar yasha ruwan tea ya tafi gidansu.
Anty na ganinsa ta washe baki tana cewa "lafiya dai daga ina haka"? Ya zauna gefe yana cewa "daga gida" ta sake cewa "ai ummee ta kawo mana kayan arziki munata godiya Allah yayi muku albarka" cike da mamaki yace "ummee"? Ta amsa da eh yace "ummee bata fa gidana Anty yaji tayimin" Anty ta ajiye robar hannunta tana cewa "kamar yaya"? Yayi shuru ta sake cewa "baka jini bane, kayi mata haukan daka saba ko"? Ya girgiza kai yace "akan maganar karatun danayi ne ta dage saina nemi aiki dashi nikuma naki tun kwanaki take fushi dani yau kuma ta siyo kayan abinci nace seta fitar dasu daga gidan shine koda na dawo ban same ta ba" Anty ta tabe baki tana cewa "dakyau! Shiyasa nake son yarinyar nan, badai mu ka gama nuna mata bamu isa dakai ba? To itama ta nuna maka baka isa da ita ba wannan ma cin amana ne ka dauko yarinya acikin daula kasata a talauci, wanda dagangan kasa kanka aciki ga yaron ciki da kwadayi baka kawo mata kayan kwadayin ba da kudinta kuma ka hanata siya taci sannan ga aikinka a hannu ma saboda wata banzar zuciya kaki karba wallahi bazance ta dawo ba kaji na rantse kuma kaje ka sami babanku da zancen ka gani idan zai kula ka, wallahi tashi ka fitarmin daga gida dan nagano kai da amutanen farko aka halicce ka bazaka karbi musulunci ba saboda muguwar kafiya da taurin kai" shuru yayi baida abin cewa sai tunani yake yana gani kamar da gangan ake kin fahimtar shi. Mikewa yayi ya fita daga gidan ya koma gida wata zuciyar na cewa ya kyaleta ai dole zata dawo. Shuru anty tayi bata sanarwa da Abba ba.Ummee kuwa duk da tana missing sadeeq sosai da gidanta amma tana samun kulawa fiye da gidanshi dan ranar da tayi azumi kwana tayi tana sheka amai har daddy ranar baiyi bacci ba dakanshi ya kira Dr aka sa mata ruwa washe gari da sassafe ya leka ta yanata jera mata sannu, yana murmushi yace "badan wannan babyn mai zuwa shine first jikana ba da sai na rankwashe shi idan yazo duniya saboda ya wahalar mini da gudar yata" kunya taji ta kasa amsa shi momy tace "yanzu sai ka daki angon nawa sabon jini" yayi dariya yana cewa "na fasa bari na tafi dan Allah a kula inaga sai nayi sati daya kafin na dawo idan wani abu ya taso zaku iya kirana" ummee ta kura mai ido tana kallon shi tana tunanin yaushe rabon da taga haka a wurinshi.
Kamar wasa sadeeq yaga an share sati daya gashi baya samun fuska a gidan anty ko abin shan ruwa bata bashi kullum da tea yake sahur dashi yake shan ruwa ko wata rana ya kwaba indomie yaci, waya ya dauka ya kirata tayi hakuri ta dawo su Sasanta maganar a tsakaninsu ko yarjejeniya ya kama suyi ai sai suyi ba matsala bane, tana zaune taga kiransa ya shigo taki dagawa yakai kira goma daga karshe ya tura mata massage irin na yaudara yana cewa "haba ummee mijinki kike gudu haka ki dauki waya muyi magana pls wallahi ina azabtuwa da rashinki" bata amsa shi ba ta ajiye wayar bayan awa daya ya sake kira nan ma taki dagawa sai sakon shi ta gani ya turo "gani a kofar gida gardawanku sun hanani shiga ki fito muyi magana" taji haushin hana shi shigan da akayi amma nesanta dashi shine abinda yafi zama dole saboda ta dawo dashi kan hanya, ganin babu respond ya saka shi dole ya koma yana tunanin ko ya sanar da amira ne ko jabir amma bai kaiga matsaya ba.
Tun daga ranar kullum sai yabkira koda muryarta kadai ya samu yaji amma bata dagawa ita kuma tana can tana Hutawa amma yana makale a ranta driver ke kaita makaranta ya daukota wata rana ameera ke dawowa da ita duk da ta haihu mijin yaso ta ajiye semester din taki.
Lokacin haihuwar batayi tsammanin samun abinda ta samu daga wurin ummee ba dan tayi zaton halin da take da mijin batada kudi amma sai taga sabanin haka sosai tayi murna ko ranar suna itace take komai daya shafi kawayensu.
Yau kam ta baci ta gefen sadeeq dan har baisan yana hawaye ba yana ji yana gani zaiyi salla batareda ummee ba saura kwana hudu fa haka ya kare azumi bashida banbanci da gauro, da sauri ya tashi ya fita yakuwa yi sa'a Abba yana nan, ya koro masa bayani tareda neman alfarma akan suje masa bikon matarsa Abba yace "wa? Ni? Kaima kasan bazanje ba dan ba karamin mutum bane ni kaji abinda yarinya take so idan kanason kanaso ta dawo sai kayi abinda take so idan kuma bazaka iya ba ka aika mata takarda babu gidan uban da zanje" ya dade a zaune Abba na masa masifa ya kasa cewa komai, ko dinkin salla bai samu yayi ba ranar salla shaddar sa ta angonci ya saka bayan sallar azahar ya shirya ya wuce gidansu yana zuwa tana kokarin komawa cikin gida daga rakiya ita bata ganshi ba ta shiga gidan da sauri ya biyo bayanta yana kiran sunanta ganin yadda securities din suka tareshi ta daka musu tsawa tana masifa, shagala yayi sa kallonta tana sanye ta riga da skirt rigar fitted ta kwanta ajikinta ga cikinta yadan fito kadan tayi kiba da haske atamfar kalar purple yana isa kusa da ita ya kasa hakuri saida ya rungume ta yana tsiyayar da hawayen da baisan kona meye ba, bai san da tana da matukar muhimmanci ba saida bata tare dashi.
YOU ARE READING
JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)
Fanfictionlabarin ya kunshi soyayya da k'iyayya ya kunshi Arziki da talauci.