JJT 12

15 0 0
                                    

*Safiyyah Galadanchi*

*JAJIRTACCE ( ABUBAKAR SADEEQ)*

*shafi na goma sha biyu*

Yana fitowa daga palon yayi gajeren tsaki wannan abubuwan da Daddy yake lissafawa duk shirmene ko sata zai ringayi bazai iya yin wannan abubuwan ba but yayi alkawarin shayar da Daddy mamaki.
Ummee datake jiransa a wajen motar ta ya karaso yana yi mata murmushi irin na masoya ita kuwa gaba daya jikinta a mace yake gabanta na faduwa tanaso taji abinda mahaifinta zaice acikin sharudan, dakyar ta kakalo murmushi amma sai bakin ta ya furta abinda baiyi kamada murmushin ba tace "sultan me Daddy yace maka"? Ya saka hannunshi a aljihu yana cewa so yake inci gaba da yimiki yadda yake miki babu canji ko tangarda, abinci irin Wanda kikeci anan, gida mai daki goma sha biyar kudin semester daya na makaranta daga miliyan daya zuwa sama, pocket money every week daga 50k zuwa sama sannan da monthly salary da bai fadi adadinsa ba kayan sawarki direct daga kamfani ake aiko muku mota wacce takai miliyan takwas zuwa sama" ta zaro ido tanayi kamar zata riko hannunshi tace "sai kaikuma kace masa me"? Kallonta yayi duk ta rikice yace "ummee kwantar da hankalinki mana meye abun razana haka acikin wannan maganar? Na fada masa na amince wannan sune sharudan da zai fada mini kafin yabani aurenki banji ko kadan ajikina zasu hanani aurenki ba amma yazama sirri tsakaninmu dan idan Abba da Anty sukaji to tabbas akwai matsala" ta girgiza kanta hawaye na kokarin zubowa daga idonta tace "Amma sadeeq bakada wannan halin meyasa zaka amince nasan Daddy is planning something worse than this zai yi wani Abu ba wannan kawai ba" da gefen baki yayi murmushi yace "bari na wuce zamuyi magana a waya inaso inje ingani ko angyarmin adaidaita sahuna" jerawa tayi dashi suna tafiya tace "baza a kawo maka sabo ba wannan yayi damage dayawa" ya girgiza kai yana cewa "banida kudin siyan sabo nikam wannan din dai nabayar a gyara" ta kalleshi tace "dan Allah mana insaka akawo maka sabo" bai kalleta ba yaci gaba da tafiya yana cewa "ki koma cikin gida mashin zan hau daganan" taji haushi sosai tace "shikenan" tareda juyawa bi bayanta yayi da kallo yana mamakin abinda yasaka tayi masa haka.

Tunda ya koma gida ya fadawa Anty mahaifin ummee ya basu nan da ssati biyu masu zuwa, tayi farin cikin hakan nan take ta soma kiran yan uwa na kusa tana fada musu fa za aje nemawa Abubakar mata yana zaune yana kallonta yana murmushi yaji ta amsa sallama tana cewa "lafiya lau Habeeb ya abujan"? Ta sake cewa " ashe ma baka kasar dan nayi magana Nuwaila shekaranjiya amma bata fadamin baka nan ba" shuru tayi tana saurarenshi sannan tace "Habeeb ko ina fa hakuri ake ga yara kuma tunda dai halinta ne bazai sauyu ba kaidai karka cuceta kaci gaba da hakuri Allah ya kyauta" sadeeq ya daure fuska Anty ta kalleshi tareda harararshi tace "madalla, gashinan ai yaji sauki ma har angyaro napep din, dama kiranka nayi infada maka baban yarinyar dayakeso yace aturo nan da sati biyu" murmushi tayi tace "to ya muka iya Habeeb adai lallaba hakanan idan babanku yazo sai in fada masa amma dai ka kira shi Dan fushi yake dakai Habeeb yaushe rabonka da garin nan" ta bata rai tace "to amma ai hannunka bazai rube ka cire ka yar ba dan haka ko yayane kayi kokari kazo kaji na fada maka" sai tayi masa sallama tareda kallon sadeeq tace "ni wallahi mamaki kake bani kuma ka sani duniya wallahi bakada kamar Habeeb kuma daga yanzu bazan sake biye ta taka ba" mikewa yayi fuskar nan a daure yace "na fita nidai" ta tabe baki tace "Allah ya kiyaye bazan dai fasa magana ba inka iya kabar garin ba gidan ba".

Tunda ya saura sati daya aje neman auren ummee Sadeeq ya tashi tsaye siya wancen siya wannan, Umma tana zaune tsakar gida taganshi nik'i-nik'i da kaya tun tana kallonshi da mamaki yana dauko kwalaye da drinks har abin ya soma bata tsoro ta zaro ido tace "Abubakar duk kayan meye wannan"? Ya juyo yana kallonta yace "Anty saurafa sati daya" daga haka ya sake fita ya shigo da sauran saida ya kammala shigowa dasu ya samu waje ya zauna yana cewa "Anty gasunan idan ansamu wani Abu da baiyi ba sai ki fadamin" takaici ya kamata yazo ya makure mata wuya a hankali tace "zan duba Allah yayi albarka" ya amsa da ameen sannan ya sake fita.
Anty kawai saita dauki waya tayi kiran babbar yayarsu suka gaisa tace "Hajiya Umma kindaiga dan nan naki bazai taba canza hali bako"? Dariya mai sauti tayi tace "meya miki kuma wannan karon"? Anty tace " shi a duniya bazaiyi shawara da kowa ba fisabilillahi ace ina Raye kuna Raye zai dauki kudi yaje yasiyo kayan nagani inaso harna fitar hankali, kodai dake kuka hada baki akayimin shuru bansaniba" Hajiya Umma ta zaro ido tana gyara zamanta tace "wallahi bansaniba nima amma bari yanzu inshigo inga kayan sai musan abinyi" anty ta amsa da to sukayi sallama.

JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)Where stories live. Discover now