JJT 20

27 3 1
                                    

*safiyyah galadanchi*

*Abubakar sadeeq (jajirtacce)

*shafi na ashirin*



*sadeeq da ummee kawata tace tana tayaku murna sannan zatazo kallon amarci yau*😂

Zaune kawai yake a gida tareda jabir suna jiran yaji ance matar shi tana gidan shi, sai wani bata rai yake jabir yace "ni muje in saukeka gida wallahi na gaji" tsaki sadeeq yayi ya mike tsaye yace "bari inga Anty" ya nufi cikin gidan, dakin anty ya leka wata abokiyar wasanshi tace "kinga idon munafiki kamar na kwarai" ya harareta yana cewa "Anty danzo dan Allah" tabiyo bayanshi tana cewa "yanzu na kira hajiya luba wannan kai amarya kamar cin kwan makauniya fisabilillahi dare ai ya gama yi kuma" yace "aini wucewa zanyi dan jabir ya gaji idan ya barni nan Inaga saidai in tafi da motar baba" tayi karamin tsaki tace "to ko kabarshi ya tafi ga makullin motar da habeeb yazowa Abban ku da ita" ya girgiza kai yace "zaifimin idan jabir din ya sauke ni, saida safe" ta tabe baki tace "shikenan Allah yakaiku lafiya dan Allah a kula a lallaba da yarinyar nan" bai iya amsa mata ba dan baisan inda maganarta ta dosa ba tana nufin ummee yar masu kudi ce se ya kula kokuma tana nufin yau ranar farsonsa da ummee din karya wahalar da ita.

Ficewa yayi yanajin matar daga daki tana cewa "semunzo ganin amarci" yayi murmushi kawai yana tunanin yaufa sai idan baiso ba.
Koda suka Isa ya samu motocin frnds dinshi da wayanda suka masa kara sukaje daukar amarya amma yasan dayawa motocin empty suka zo" jabir yayi dariya yace "mutanen fa da alama suna nan" yayi karamin tsaki yace "sha biyu saura fa? Mutane wani lokacin saikaga sunayin abu kamar dagangan" yana rufe bakinsa sai ga tururuwar yan mata da dattijai sun fito nan take suka watse kafin wani lokaci seyarage friends  dinsa kawai ne sukayi masa rakiya tareda addua suka fito.

Ummee kuwa har lokacin abinda Daddy yayi mata yana ranta sai kuka take yi, da sallama ya shiga dakin ta dago tana amsawa tare da kallonshi, yadan bata rai alamar baiji dadin ganin yanayintaba yakarasa kusa da ita yace "duk kukan rabuwa da momy ne" kwantar da kanta tayi kafadarshi tana kuka tace "kayimin alkawari bazaka taba cutar dani ba, bazaka wulakantani ko ka rabu dani ba" mikewa tsaye yayi yacire babbar riga da hula ya ajiye gefe sannan ya sake zama tareda rungumeta duka jikinsa yafada mata magana a kunne ta gyada masa kai sannan yace "tashi muyi salla" mikewa tsaye sukayi a tare ya cire mata mayafi sannan ya dauketa har zuwa bayin atare sukayo alwala suka fito, bayan sun gama salla da adduaoi ya kalleta yace "bari inkawo miki abu kici kuma dan Allah kukan nan ya isa haka, daddy fushi yakeyi saboda ba irina yaso ki aura ba nikuma nayi miki alkawari zan yi iya kokarina namiki alkawarin farin ciki wanda baya Yankewa" kanta na kasa kawai saitaga babu albarka a aurenda aka daura babanta yana fushi da ita, nama ya kawo mata da madara tace ta koshi murmushi  yayi yamatso da ita kusa dashi ya fara deba yana bata dakanshi yayi mamaki taci sosai alamar tana tareda yunwa kenan.
Toilet ya shiga ya tara mata ruwan zafi  yace taje tayi wanka sannan ya fita wani dakin daban ya shiga yayi shirin bacci sannan ya dawo koda ya dawo tana zaune gefen gado ta saka rigar baccin amma ta yafa mayafi wutar dakin yakashe sannan ya hawo Gadon kwantar da ita yayi yafara  yi mata tausa yana yi mata hira a hankali tace "abokanan daddy dayawa sun bani kyauta harda wanda yabani mota amma daddy ya hanani bansan meyasa ba" murmurshi sadeeq yayi yace "yanaso yaga na inganta rayuwarki ne amma karki damu kinji watarana zai baki abinki" tayi masa shuru tana jin dadin yadda yake yimata tausa.

Washe gari karfe takwas Anty ta aiko musu da abincin safe basu ci ba sai karfe goma dan bacci suka koma sunyi wanka da kwalliya kana ganinsu kaga ango da amarya gidan kuwa kamar nepa sunsan ana angonci basu dauke wutaba ko ina ya dauki sanyin Ac suna gamawa ta dauki plate din taje daurayewa bayan ta fito take Cemasa "kitchen dincan ko wurin tsayiwa babu" yadan ji ba dadi yace "kayanne sukayi yawa naga har store din acike kifitar da wanda zakiyi amfani ki kawo sauran akaisu dakin can inba hakaba kitchen dinnan bazaiyi aikiba" ta amsa masa da to tana cewa "ka huta amma idan ameera tazo ta tayani fitarwa" ya amsa da to a tare suka koma daki tunda babu abinyi, amma mutane da suka fara xuwa ganin gida gasakashi fita dole bayan ya kawo mata drinks da ruwa na tarbon baki.

Saida suka share sati daya sannan kafafuwan mutane suka dauke a lokacin ne kuma anty tace su fara girki dakansu daddy kuma yaki kawo gara badan babu ba hakanan yake raayi.
Nanfa ake yinta idon sadeeq ya soma raina fata, hakanan ya daure ya shiga kasuwa ya siyo musu duk abinda zasu bukata ya zauna zero dole ranar lahadi ya fito da adaidaita sahunsa Ya fara fita.
Washe gari Monday shine ya kaita makaranta, ta saka kayanta atamfa riga sa skirt na jar atamfa mai zanen jirgin ruwa da farin mayafi tun a gida ya bata dubu biyu taci abinci taso taki karba amma taga ya hade rai sosai. "Karfe nawa zaki gama lectures din" tayi murmushi tace "karka damu ameera zata maidani gida bayan laasar zankoma" ya gyada kai yana cewa "ki kula dakanki kuma kici abincin karki zauna da yunwa" ta gyada masa kai sannan ta nufi Hall din, take yan class din suka zuba mata ido har saida ta tsargu, kusa da Ameera ta zauna, Ameera tace "amaryar sati daya har kin soma fita" ta gyada mata kai tana cewa "shima ai ya soma fitar ba dole nima na fito ba" Ameera tace "ni wallahi yau kamar nayi zamana bacci ke idona kamar banyi da dare ba" ummee tace "wannan cikin ne may be yake saki yawan bacci" ta tabe baki tace "ai bantaba ganin abu mai janye-yanye irin ciki ba yaufa da safe bread da miyar kuka naci" dariya ummee tayi sosai tace "wayaga big girl dacin bread da miyan kuka" tsaki ameera tayi tace "kema kwana nawane kila ma kin samu bayyana ne beyiba" murmushi kawai tayi shigowar lecturer din yasa batayi magana ba.

Sadeeq ko yadaiga canji arayuwarshi badan ya mori amarya ba kuma dalilin dayasaka ya daga kafa akan abin saboda bayaso tayi tunanin dan yana shaawarta ya aureta amma yasan yana tsananin bukatarta murmushi ya subucemishi jin wani bangare na zuciyarshi yana cemishi ina tausaya mata randa ta shiga hannuna.

Karfe biyu ya kirata lokacin suna jiran malamin yaxo dagawa tayi suka gaisa yace "ya kindaici abincin ko"? Ta amsa masa "eh naci yanzun nan ma muka dawo daga minimart" yayi murmushi yace "me kikaci" ta harari ameera dake mintsininta tace "Friedrice muka ci sai fanta da ameera tazo mana dashi" yaji wani iri saboda kafin ya aureta koda yaushe motarta da irin abubuwan aciki yace "to sai kundawo ki gaishemin  da ameeran" ta amsa da zata ji sannan sukayi sallam.

Fiyyah na gaisheku
Jini yafi ruwa kauri

JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)Where stories live. Discover now