*Safiyyah Galadanchi**JAJIRTACCE ( ABUBAKAR SADEEQ)*
*shafi na goma sha hudu*
"Babu ruwana idan hawayenki ya kare yarinya, bakisan nine zan ringa yi miki wanka ba? In shafa miki mai, in saka miki kaya, nine zan baki abinci abaki inringa goyaki sannan in lallabaki kiyi bacci bayan haka inmiki wanki da guga ummee in share miki gidanki da ingoge miki idan kinaso ma nine zan miki girki" ya danyi kasa da murya yana cewa "sannan idan zan tashe sallar asuba intasheki da kiss" tunda ya fara magana taji kunya ta damamaleta daga karshe kuma ga maganar daya fada tayi saurin buge masa hannu kadan tana cewa "nikam ka bar fadamin dan Allah" yayi dariya yana cewa "ai laifinki ne zaki tayarmin da hankali harda kuka" tayi murmushi kawai tana goge hawayenta yace "to ni baki fadi abubuwan da zakiyimin ba saboda kauna" ta Dan turo karamin bakinta tace "basai na fada ba kuma kabar zancen nan kona gudu" yayi dariya sannan yace "Ummee kinsan kullum addua ta itace idan akwai ranar da zan tauye miki hakki na cutar dake to Allah yasa ranar bata cikin ranakun da zan gani a duniya" ta sauke ajiyar zuciya tana gyara zanan mayafinta tace "Nina haka sadeeq" "meyasa bakya son daura dankwali" ta yamutsa fuska tana cewa "yana damuna seya hade da nauyin gashi" murmushi yayi yana cewa "sekace wata India ina gashin yakai yayi nauyi"? Tayi murmushi tana cewa "nan gaba kadan zaka gani ai idan yakamata yayi nauyin" zaro key din mota yayi ya mika mata yana cewa "to bari na wuce dare nayi kuma nasan kina tareda gajiya" ta karba tana cewa "ina kuwa ka sani yawo ne dai bana part dina bana na Momy, ko kawayena su suka raba abun dakansu sai ameera da Aisha na debarwa yanzu daga naje kwanciya zanyi inyi bacci" ya gyada kai yana cewa "saida safe kenan"? Tace "a'a wani nikam Dan Allah a wane mataki ka tsaya da karatu ko bakayiba"? Ya bata rai yana cewa "nayi amma karatun bashida amfani awurina kuma Dan Allah kibar yimin maganar karatun nan" ganin ya daure fuska yasa tacewa "Allah ya baka hakuri" ya fito daga motar yana cewa ameen rakiya tayi masa har gate ta dawo.
Duk yadda suka rabu be mata dadi ba ko kadan Dan haka ta kasa bacci bayan ta kwanta sai ta kirashi muryarshi lafiya lau taji kafin tayi magana yace "hajiya ummee meyasa dazu baki fadamin abubuwan da zakiyimin ba bayan ni na fada miki" dariya kadan tayi tace "to zan maka girki ingoge maka takalmi" yana murmushi irin Wanda yakeda sauti yace "saura dayan fa mai muhimmancin" ta tashi zaune tace "Girki"? Yace "a'a" Dan shuru tayi tace "to nidai gaskiya bansan shi ba" lumshe ido yayi yana gyara kwanciyar shi yace "na baki Assignment duk sanda kika sanshi sai ki fadamin" tace "to shikenan yakamata ka kwanta kayi bacci Nima bacci nakeji" sallama sukayi daganan ya kwanta bacci saboda dagaske yagaji.
Washe gari Habeeb da Anty tareda Abba ne zaune a dakin Abban magana suke akan gidan da sadeeq ze zauna da kuma kayan lefe saboda sun San mahaifin ummee yanada komai ashirye yake Dan haka lokacin daya deba bamai tsawo bane Anty tace "Ai yanzu adai fara hada kayan, wallahi wannan ma da sukayo duk ya dad'a sanyaya min jiki sai naga shi sadeeq din ba wani karfi ba muma ba haka ba komai zamuyi bazamu burgesu ba karshe ma shi mahaifin nata ba son auren yake ba nasan dole aji ba dadi idan bamu tashi tsaye ba" Abba ya ajiye madubin idonsa gefe yana cewa "Ahhto me za ayi tunda karfi ba daya ba ai ko bai musu ba komai daidai kurji daidai ruwansa haka za ayi idan ansamu ko akwati hudu ne aka zuba kala talatin ai anyi kokari" habeeb ya zaro ido yace "Abba kala talatin ai ko mai aikin gidansu tafi karfin haka Dan Allah Abba ka bar cewa haka" kallonsa Abba yayi yace "dakata habibu yaron nan bashida muradi da hannunka alamarinsa Dan haka bana so ka shiga ko wannan Dan bakayi shawara dani bane yasa kayi amma kabarshi can yaji da haukarshi da bakar zuciya wallahi dole dai angulu ta dawo gidanta na kara" shuru duk sukayi yaci gaba da cewa "nidai zanyi iya kokarina an kwana biyu dai nasan ya siya fili shima a shanun talla naji Dan nasan Wanda ya siyeshi awurinsa sanadin haka ma yamasa ragowa sannan yabishi bashin wasu canji na sama dubu Dari da hamsin to bansan halin da filin yake ciki ba yanzu idan akwai shi seya siyar a kama masa haya" Habibu dai yayi shuru Dan yana tunanin yadda zai bari Dan uwanshi yashiga gidan haya bayan yanada halin da zai iya bashi kyautar gida ma.
Anty tace "da akama gidan haya ba gara yazo nan cikin wannan filin gidan ya soma gini ba Indai Dan daki biyu da Palo sai kitchen bazai gagara ba" Habib yayi dariya yace "Abba maganar gidan nan abarta zanyi magana da shi sadeeq din" Abba yace "Allah ya bada Sa'a" suka amsa da ameen.
Lokacin da Habib ya fito nan yaga dakin sadeeq a bude sai ya shiga da sallama, sadeeq dake shirin fita ya dakata da saka botiran rigar yana kallonshi bayan ya amsa sallamar, rigar jikinsa Habib ya kalla duk ta kode duk da dai mai tsada ce amma taji jiki ya zauna kan kujerar roba yace "Abubakar wai baka gaji ba" ya yamutsa fuska tareda tamke ta tamau yace "da akayi me zan gaji"? Habeeb yayi murmushi yace "kaa saki fuskarka kuma dan girman Allah wannan karon kayi hakuri nasan nayi kuskure kuma inata lallashinka kaki hakura" sadeeq ya tabe baki duk da yaji kunya matsayin habeeb na babba agidansu bai kamata ace yana yi masa haka ba amma dole ce ta saka yace "nifa tuntuni na hakura amma nagode dakayimin haka yanzu nasan ciwon kaina nasan naki abin wani na nemi nakaina kuma na tsayu akanshi nafi jin dadin rayuwata a haka da bana tunanin wani yayi min kuma ban dogara akan kowa ba balle watarana a yarfani acikin jamaa a kunyatani tare da yimin gori wallahi habeeb abin hannun ko burgeni bayayi koda amafarki ne" maganar tayiwa Habeeb zafi fiyeda ko yaushe tunda abinda ya faru ya faru yasan bai kyauta ba ko shine dole zaiyi fushi amma kuma abin abubakar yayi yawa sosai sai yayi murmushi ya mike tsaye yana cewa "da Allah yabawa Dan Adam damar da zai tsaya yayiwa kansa komai akan Kansa batareda Neman taimako ko alfarma awurin wani ba da Allah bai hada Hauwa da annabi Adam aduniya daya ba da Allah yayoka kaikadai cikin duniya batareda kowa ba amma abubakar ka sani wani abin komai taurin kanka bazaka taba iya yiwa kanka shi ba saika nemi taimako awurin wani kuma nayi alkawari daga yanzu Abu daya zuwa biyu zai hadani dakai na kyautatawa daga na kammalasu nayi maka alkawari sai kazo da kanka kana rokona tareda Neman alfarma awurina lokacin ne zaka San ko duniyar nan ka mallaka inada amfani awurinka" yana gama fadar haka ya juya ya fita tareda alkawarin maganar Gidan ma ya fasa duk yadda yaji zai iya yaje yayi sadeeq kuwa jikinsa yayi sanyi Dan habeeb ya Dade yana daukar raini daga wurinsa.*WANENE SADEEQ*?
*WANENE HABEEB*?
*MENENE AINAHIN LABARIN UMMEE DA SADEEQ**JINI YAFI RUWA KAURI*
*fiyyah na gaishe Ku*
YOU ARE READING
JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)
Fanfictionlabarin ya kunshi soyayya da k'iyayya ya kunshi Arziki da talauci.