JJT 4

18 0 0
                                    


*Safiyyah Galadanchi*

*JAJIRTACCE ( ABUBAKAR SADEEQ)*

*shafi na hudu*

Bude motar tayi ta fito babu kowa a layin yayi shuru kamar ba mutane a unguwar, gate din gidan ta shiga ta danyi tafiya kadan sannan ta shiga cikin gidan da sallama a bakinta Anty dake kokarin shiga korido tayi tsaye tana kallonta sannan ta amsa sallamar ta.

Tsayawa tayi cike da rashin sanin abinda zatayi kuma gaba daya jikinta a sanyaye yake, Anty ta danyi murmushi Dan taga kamar ummee ta fahimci batayi farin cikin ganinta ba tace "sai nace ki shigo kuma kamar wata bakuwa" ummee ta dan sauke ajiyar zuciya sannan ta soma takawa a hankali ta shiga cikin gidan a palon su ta zauna kasa ta Dora kanta jikin kujera Anty ta Dade tsaye tana kallonta kafin ta karasa kusa da ita ta zauna tareda kiran sunanta, dagowa tayi ta kalleta tace "Anty ina wuni" murmushi Anty tayi tace "lafiya lau amma meyake damunki naga kinyi zuru-zuru"? Hawayen da take rikewa ne suka zubo a hankali tace "Anty saboda kuna haka yana nufin bakwa jin dadin rayuwarku? Sau nawa kuke cin abinci a wuni? Idan da hali bakwa dinki duk shekara ko kuma ranar da Allah ya hore ko babu lalurar komai kuyi dinkin sabon kaya? Anty an taba zuwa akace Ku kwashe kayanku daga gidan nan ba naku bane"? Anty ta girgiza mata kai tace "ban taba bakin ciki saboda rashin muhalli ba, bantaba kunci saboda yunwa ba, ban taba fasa shiga jama'a saboda rashin sutura ba ummee" ummee ta riko. Hannunta tace "To Anty idan na fadawa Daddy na wannan maganar zai yadda Sadeeq ya aureni" murmushi Anty ta sake yi tace "kinada wauta ummee, mahaifinki bai San da wannan ba koda ya sani bazai taba yadda ba, ummee kinfi karfin Abubakar" ta fashe da kuka tana girgiza mata kai "ban taba kawo hakan a raina ba Anty Daddy kawai bayason farin ciki nane wannan karon idan ba haka ba bazai yi kokarin rabani da Wanda na kawo na kuma nuna masa ina matukar sonshi ba, baiyi la'akari da kunya da mace take dashi ba Amma ni na ajiye shi gefe, baiyi tunanin tarbiyata ta fara sauyawa ba saboda kin sadeeq da yayi, jiya na fada mishi idan bada sadeeq ba Anty bazan yi aure ba a duniya" shuru Anty tayi daga baya kuma tace "amma bakya tunanin ko takalmin da kike sawa sadeeq bazai iya kula da siya miki irin shi ba? Ummee wahala zakuyi saboda zaiyi kokarin yin abinda yafi karfinsa kuma Har yanzu bashida wadatar da zai kula dake kamar yadda kike samun kulawa a gidanku" sake rike hannun Anty tayi "bai dameni ba zanyi rayuwar irin taku kamar shi" cike da mamaki Anty take kallonta tace "ummee wallahi inasonki da Abubakar kinada hankali kinada tarbiya baki taba wulakanta mu ba dan haka shawarar da zan Baku itace kuci gaba da addu'a insha Allah idan ke matarsa ce zaki sha mamakin yadda abubuwa zasu sauya" dan murmushi tayi tana cewa "Allah ya karbi bakinki Anty" ameen anty ta amsa tana cewa "ki tashi ki wuce kafin a gano kina gidan nan" ta bata rai tace "Daddy yayi tafiya yau kuma ina fushi da gidan can zanyi salla tukunna kafin na tafi" dakinta Anty kaita tayi alwala tana kallon toilet din bazaka taba cewa ana amfani dashi ba babu ko digon ruwa a kasa sai kamshi yake ko ina fess alwala tayo tana cikin salla laila tashigo ta dawo daga makaranta, tayi dan murmushi tace "matar Yaya Abubakar" ta karasa shiga dakin ta ajiye Jakarta sannan ta zauna tana cire uniform.
Tana gama cirewa ta mike da Wanda short skinny sai ves ajikinta gata da jiki irin na Anty ba kiba sosai amma kuma ba siririya bace da alama idan ta samu Hutu zatafi haka ummee ta kalleta bayan ta sallame sallar tace "kanwata laila" da sauri ta juyo ta karasa kusa da ita tace "tun ranar nan kuma, ina yini" ummee tace "lafiya lau bakya jin kunya laila a haka kike zuwa makaranta" laila ta dago ta kalleta tace "menayi"? "kalli bakya saka bra laila bakisan babu kyau ba" tabe baki laila tayi tace "tab...bra ai girmana basu Isa su fara sawa ba nikam gaskiya kunya nakeji aganni da bra ace na girma" girgiza kai ummee tayi tana murmushi tace "asheko wata rana sai uncle dinku ya taba miki nan" ta fada tana nuna mata kirjinta dan ja baya tayi tana zare ido tace "eh mana ko bakisan akwai maza yan iskaba idan sukaga kirjin mace a haka kina tafiya yana motsawa zasu gane baki sa bra kuma kinga Sai suyi tunanin sunada free access to kirjin naki kiringa saka bra kinji babu kyau mace mai kirji haka tana sakinsu duk inda kika juya suma su juya suna tsalle" hannu tasa ta rufe fuskarta saboda kunya ummee tayi murmushi tace "bari in baki wani labari lokacin da muna secondary school Jss akwai wata Hafiza itama bata saka bra gata da girji a cike da wata blessing Christian ce itama bata sawa sedai nata basuda girma sosai idan malamin mu mai physical health education ya shigo sai ya fita damu filin makaranta sai a ringa wasan tseren gudu, kinga hafiza da blessing dinnan sai yayita basu kyautar maki yana sasu gudu yanata kallon yadda jikinsu ke motsi yana tsalle ranar nan seda yayiwa blessing din nan iskanci takai karar wurin director aka koreshi" hankalin laila duk ya tashi dan kamar ummee tasan gudun tseren da sukeyi tace "tab bari in fadawa Yaya Abubakar wallahi ya siyomin kar ayi min wannan iskancin" ummee ta kwashe da dariya tace "ke karki masa magana ki bari zan siyo miki" Anty data dawo dakin rike da plate din abinci guda biyu ta kalli Abubakar daya tsaya bakin kofar dakin tace "lafiya kazo nan ka tsaya" ya girgiza kai yace "magana suke ummee da laila shiyasa" tayi murmushi ta karasa cikin dakin taji ummee na cewa "gobe zan kawo miki kinji" Anty tace "maganar me kuke kuma me za a kawo mata" laila tayi saurin cewa "bra zata kawo min tace maza Na iskanci idan ba a sawa" Anty ta girgiza kai tace "daya fi miki laila amma ko half ves nace kisa se kin kawo min iyayi, kaikuma ka shigo mana abincin na sanyi ka tsaya bakin kofa" ummee ta zaro ido tace "Anty bari in wuce" hararar ta Anty tayi tace "babu inda zaki sai kinci abincin nan" tayi murmushi kawai batayi maganaba saboda shigowar sadeeq gaidashi tayi ya amsa yana cewa "baki tafi makarantar bane yau" plate din abincin ta ja gabanta tana cewa "daga can nake malamin ne bai zo ba shiyasa nayi saurin dawowa" ya gyada kai kawai baiyi magana ba "Anty ta kallesu tace "laila kinyi salla kuwa"? Tace "munyi a masallacin makaranta Anty ina kayan da zan saka" "suna dakinki ai na fitar miki dasu tunsafe ki kuma kwashemin kayan nan kije ki debo abinci a kitchen" ta amsa dato sannan ta fita daga dakin.

Kadan ummee taci abincin sannan ta mike ta ninke hijab dinda tayi salla tace "Anty zan wuce nagode sosai Allah ya saka da alkhairi ya kara girma" ameen anty ta amsa tana kallon plate din abincin iya rabi taci shi kuma gogan yaci fiye da Rabi ya ajiye yabi bayan ta a Palo ta tsaya ta dauki mayafinta yace "meyasa kika kashe waya" ta dago ta kalleshi tace "Daddy ne yasaka raina yayi matukar baci har saida bacci ya kaura daga idona shiyasa na kashe wayar ko tafiyar sa ma bangani ba" ya dan bata ransa kadan yace "babu kyau abinda kika bakisan tafiya za a dawo a sameki ba kokuma Wanda ya tafi zai dawo ba karki sake yin haka ta gyada masa kai kawai. Suna zuwa wurin mota tace "har ka dawo daga gonar"? Yace "Eh na dawo yanzu dai zan Fita da adaidaita sahu zuwa magrib zanje kalambaina a dafa shinkafar" ta kalleshi cike da tausayi tace "don Allah ka huta gobe wallahi aikin nan yayi maka yawa" yayi murmushi yace "haba ummee zama bai ganni ba wallahi in ba cikin dare ba na kwanta bana tunawa da wani Abu waishi hutu"

*Jini yafi ruwa kauri*

*Fiyyah na gaisheku*

JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)Where stories live. Discover now