*Safiyyah Galadanchi**JAJIRTACCE ( ABUBAKAR SADEEQ)*
*shafi na farko*
Tafiya yake acikin adaidaita sahun shi kadai tunanin da yake kuwa bai wuce akan ummee ba har ya Isa gida kamar ko yaushe haka ya shiga da sallama a bakinsa Anty dake zaune tsakar gida kan tabarma tana ninke kayan data wanke da safe ta dago ta kalleshi bayan ta amsa sallamarsa, durkusawa yayi ya gaisheta ta amsa fuskarta ba yabo ba fallasa kujerar roba dake bayansa ya janyo ya zauna yayi shuru kamar yadda ya saba.
Anty ta kwalla kiran wata yarinya tace "Laila! Idan kin gama sallar zoki dauki abincin yayanki kikai masa dakinsa" fitowa yarinyar tayi akalla zata kai shekaru goma sha biyar ta ajiye hijab dinta kan tabarma zata shiga kitchen ya tsayar da ita yana cewa "Laila idan kin dauko ki bawa almajirin can da yake bara ni na koshi" ta amsa da to tana kokarin shiga kitchen din Anty tace "ka koshi me kaci? Kai ba a Isa dakaiba ko sadeeq"? ya mike tsaye yana cewa "A gidan suhail naci abincin Anty" ta ajiye rigar dake hannunta tace "to bari in fada maka tunda baka tsoron a tare mahaifinka ayi masa wulakanci da cin mutunci kar in sake ji labari ance ko hanyar gidan nan kabi wannan wane irin rashin sanin ciwon kai ne Abubakar ita kadai ce mace da zaka nace mata yarinyar tafi karfinka ka rabu da ita mana ga yara nan ko a yan uwa" ya juyo ya kalleta yana cewa "Anty maganar nan koda yaushe sai an nanata ta ne? Banaso nayi abinda za a zo ana zagina kuma ana zaginku duk yarinyar Dana aura bana sonta bazan iya yi mata adalci ba kawai kuci gaba da yimin addua" ci gaba tayi da kallonshi cike da rashin abin cewa kuma saida ya kama hanyar shiga dakinsa tace "wallahi abubakar kabi a hankali ina tsoron ranar da zanyi maka rantsuwa akan yarinyar nan" Dan juyowa yayi ya kalleta sai kuma ya nufi kofar fita daga gidan gaba daya. Adaidaita sahunsa ya shiga ya kama hanyar barin unguwar wayarsa tayi ringing tsayawa yayi ya dauka yayi shuru daga bangaren da akayo kiran kuma akace "inada lecture 4 to 6 idan babu damuwa gani a kofar gidanku ka raka ni mana" "kijirani ganinan" iya abinda ya iya fada kenan ya juyo tana zaune cikin mota ta ganshi ya dawo ya bude gate ya saka adaidaita sahun ya fito.
Kafin ya karaso ta bude motar ta fito tana sanye da doguwar rigar atamfa super Holland kalar purple da adon peach ta yafa mayafi karami peach.
Murmushi yayi ya shiga ya zauna itama ta zaga ta shiga gaban motar a hankali yake driving har suka isa makarantar shiga tayi lecture yana zaune cikin motar harta fito ta shigo motar tana goge gumi tana cewa "jiya bayan kabar gida Daddy yace zai daukeni daga Nigeria dama shi bai yadda da karatun nan na Nigeria ba" yayi shuru har saida ya fara tafiya yace "ko kintafi ummee ai zaki dawo zan jira ki" bata kalleshi ba ta juya baya tana dauko drink dinda ke ajiye tana cewa "bana tunanin zan tafi karatu wata kasar gaskiya kuma na fada masa" bai kalleta ba shima din yace "kin fada masa zanzo gaida shi" ta dafa goshinta tana cewa "kash haba sadeeq, ka bari ka huce daga haushin abinda yayi maka mana" yayi murmushi yace "wallahi ummee tunda daddynku yake cin zarafina akanki hakan bai taba sa na kwana dashi araina ba, haihuwarki da yayi kadai bazaisa nayi fushi dashi ba ballanta kuma inaso ya bani ke" ta kwantar da bayan ta jikin kujerar motar bata sake magana ba har suka iso gida, security din da ke tsaron kofar gidan dayaga motar ummee ce sai kawai ya bude suka shiga sun Dan yi hira kadan sannan ya bude motar ya fito ya zaga gefenta ya bude mata yana mika mata keys din motar Alokacin daddy ya fito tareda mukarrabansa tsayawa yayi ya rike kugu tare da sakin huci kadan yana kallonsu sai kuma ya tura hannunsa cikin aljihun wando ya soma tahowa a hankali, ummee ta kalli Sadeeq da niyyar son ganin yanayinsa Amma sai taga ko kadan bai damu ba saima kara mika mata key din yayi yana cewa "Gobe ina tunanin zanje gona" ta nade hannunta a kirji tana murmushi tace "inga hannun da zaiyi noman" bai bata amsa ba ya juya yana kallon Daddy yana isowa yayi saurin durkusawa yana cewa "barka da fitowa daddy ya aiki" tsaki daddy yaja ya kalli lukman dake gefensa yace "ba yaron nan ne aka bawa warning ba jiya akan ummee"? Cike da hasala lukman din yace "wallahi shine Daddy, wai ummee ko maye kika samu" mugun kallo tayi masa tace "wallahi yafiye min kai duk Inda kabi sai warin sigari da wiwi" ta maida dubanta wurin Daddy tace "Daddy dan Allah mana adaina sako min mutumin can acikin lamarina and kaja masa kunne kar ya sake yimin magana" lukman ya girgiza kai cike da Bacin rai Daddy ya sake kallon Sadeeq yace "jiyan nan na tura mutane har uku sunje wajen talakan ubanka sun fada masa yaja maka kunne akan yata ummee, bai Sanar dakai bane"? Sadeeq yayi kasa dakai gate daddy ya nuna masa da yatsa yace "banason maimata kalamai ko kuma marukan Dana Shafa ma jiya ka bacemin da gani" sadeeq ya juya yana kallon ummee data kureshi da ido ya sake mika mata key yace "ga shi sai anjima ko" ta karba tana cewa "insha Allah zamuyi magana idan ka Isa gida kuma dan Allah ka gaishemin da Anty" bai tsaya ya bata amsa ba saboda yadda ido suka yi masa yawa yaja kafafuwansa yana tafiya a hankali Daddy ya sake Jan dogon tsaki ya juya yana kallon ummee yace "meyasa kike min haka duk abinda kike so shi nakeso ummee to akan me bazaki ki abinda ya kasance ina kinsa ba" ta kawar da kanta gefe zatayi magana lukman ya rigata yana hararar bayan Sadeeq yace "matsiyaci ji yadda yake tafiya sai kace ya bawa miliyan Dari baya, ni wannan shegen nuna Isa da takamar nashi yafi komai kona min rai" juyowa tayi ta kalleshi tayi shuru sai kuma ta kalli daddy tace "yanzu ka gama cewa kanason duk abinda nake so menene aibun Abubakar da bazaka tayani sonshi ba shima kasan ko shekara nawa ya dauka yana wahala dani"? Daga haka ta juya zata shiga gida tana cewa "ni zan shiga ciki Daddy ina tare da gajiya" lukman ya kalli daddy yace "meyasa yarinyar nan bata sona ne? Ga fari ga saje ga ilimi ga iya wanka ga kudi karewarta ma mu jini daya ne" Daddy ya kalli sakatarenshi daya ja gefe da wani bawan Allah sunyi gum da bakinsu yace "Ku tafi kawai na fasa fitar" ya fada yana juyawa ciki shima.*Fiyyah na gaishe Ku*
YOU ARE READING
JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)
Fanfictionlabarin ya kunshi soyayya da k'iyayya ya kunshi Arziki da talauci.