*JAJIRTACCE ABUBAKAR SADEEQ*

*SHAFI NA ASHIRIN DA BIYU*


Ya danyi mamakin ganin daddy  a gidan amma sai ya durkusa yana gaidashi daddy ya yamutsa fuska ya shigo yana kallon tsarin gidan ya juya ya kalli lukman da suka zo tare yace "filin gidannan zai dauki mota biyu kuwa"? Lukma ya girgiza kai yace "saidai mota karama daya da mashin, ai daddy ko taron suna gidan nan bazaiyi ba"  sadeeq yana daga gefe yana saurarensu daga baya yace "bisimillah Daddy ku shiga" ba tareda ya kalleshi ba yace "ko baka fada ba tunda uwata tana cikin gidan ai dole zan shiga inganta ko"? Shuru sadeeq yayi ummee tana zaune sai ganin Daddy tayi saurin mikewa tayi ta janyo mayafinta ta saka ta durkusa tana gaidashi maimakon ya amsa seya kalli plate dinda ke gabanta ya yamutsa fuska yace "abincin kaji ne wannan"? Ta kalli plate din ta sake kallon daddy tayi murmushi  tace "a'a  daddy ni nake ci saboda yau shinake shaawar ci" tabe baki yayi ya zauna yana cewa "kodai dole ce ta sakaki cin irin wannan abincin" shuru tayi masa shikuma sadeeq har lokacin yana tsaye yana kallonsu lukman yace "gidan nan ba a bawa mutum ruwa ne sai ya roka"? Mikewa tayi ta shiga kitchen ta bude freezer pure water biyu suka rage sunyi kankara sosai daya ta ciro ta fasa ta hada da ruwan famfo takai masa a jug ya tsiyaya yana kurbawa yayi saurin dawo dasu yana cewa "ruwan kanwa ne wanan ko kasheni kikeso kiyi" ta kalleshi dakyau tace "ashe damun mutu mu dan sune ruwan da muke sha ya rage gareka yanzu kasha ko karka sha ruwa kanema kuma anbaka" Daddy yace "ke bana son hauka da rashin kunya kina jina, kinga irin abinda nake guje miki ko? Kalli yadda kika lalace, kalli wannan karamin gidan a takure, ga rashin wuta ga rashin abinci mai kyau yanzu wa gari ya waya"? A hankali ta soma magana tace "daddy banyi nadabar auren sadeeq ba kuma bana tunanin zan taba yin nadamar aurenshi har karshen rayuwata, abinda ya bani mamaki duk bai wuce kai ba daddy, koda duniya zataga laifina wajen auren sadeeq to bazataga laifin sadeeq na kasa daukar dawainiyata ba, kuma Alhamdulillahi Daddy yadda kake son ganina haka kazo ka sameni sann..." Sadeeq yayi saurin katseta yana cewa "ya isa ummee daddy  mun gode da ziyara insha Allah za a gyara" kasa tayi da kanta tana jin yadda zuciyarta ke mata zafi, daddy ya mike tsaye yana cewa "shikenan sai anjima dama zuwa nayi inga ko kina lafiya" ya karasa maganar yana ajiye mata dubu daya sabuwa dal.
Bai bar unguwarba ta dauki kudin ta kallesu dakyar sannan ta yayyagata ta daure a leda ta fita da ita waje ta watsar da ita, tsaki tayi aranta tace babu komai atareda maza sai bakin ciki da takaici, tana shiga gidan taji ya janyo hannunta yana cewa "banida ko sisi zaki yaga dubu daya ya kike so inyi" kallonsa tayi taga da gaske yake sai taga yana murmushi kamar zatayi murmushin kuma sai taga yana kokarin hade bakinsu tsayawa tayi dakyau.

A kunne ya rada mata "kisan irin maganar da zaki fadawa iyaye duk yadda ranki yakai ga baci" shuru tayi masa dan gaba daya jikinta ya gama mutuwa, ranar ko wanka batayiba tasaka rigar bacci ta kwanta, kallonta yayi yace "wankan fa" gyara kwanciyarta tayi tana cewa "banajin yin wankan ne" mikewa yayi ya shiga toilet ya hada mata ruwa ya fito tana daga kwance taji ya dagata sai toilet din"mekake shirin yi" yana murmushi yace "na fada miki ai ni xan ringa yi miki wanka to dama wannan ranar nake jira, ta rike masa hannu daga kokarin Rabata da rigar ta dayake yi tace "kayi hakuri zanyi dakaina" ya yamutsa fuska yana cewa "hakuri laifinme kika yimin? Sannan kice bayanzu ba sai yaushe"? Tayi saurin cewa "sai na haihu" yayi dariya mai sauti yace "to ai se an fara haka ake haihuwan" zatayi magana ya debo ruwa ya zuba mata dole tayi shuru, daga nan dai yaga dole wankan nan bazai yuwu ba ya sakar mata sabulun a hankali yace "ki karasa dakanki" yafito dakyar tab...jikinta kawai ta karasa daurayewa tabiyo baynshi daure da towel ya cire kayan jikinshi yan kokarin saka riga yaji ta kwanta a bayanshi, ya sauke ajiyar zuciya yace inkinason kanki da lafiya ki sakeni" tayi murmushi tace "banfa yi niyyar yin wankan nan ba kasakani dole kuma ka fara ka daina ya kake so.." bata karasa ba taji ya kunce mata towel ta sake zaro tana kokarin Tareshi. To mai nema a duhu balle an haska mai.
Yana rike da hannunta kamar za a kwacemai yana sauraren masallaci ana kiran sallah dakyar ya iya bude idonsa ya tashi toilet ya shiga yayo alwala ya dawo ita kuma tana aikin bacci  bai tasheta ba, yana gama sallar ya sake kwanciya sai karfe tare ya bude idonsa kan carpet  ya hangota da alama salla tayi ta kwanta a wurin, cikin bacci taji yana kiran sunanta ta bude idonta tana kallonshi yace "tashi ki koma kan gado mana" mikewa zaune tayi ta gaidashi ya amsa yana cewa "lafiya lau honey🍯, ya jikinki" bata iya amsa mishi ba ta sauke idonta kasa yace "ki kara yin wanka inkaiki gidan Anty fita nakeso nayi Amma ki saki jikinki karta fahimci wani  abu kinji honey" hararar wasa tayi masa sannan ta mike a hankali ta shiga toilet.

Anty tana zaune tana gyara naman kazar da Abba ya kawo jiya dare yayi bata dafa ba suka shigo yana rike da hannun ummee saurin kwace hannunta tayi suka karasa kusa da ita suna gaisheta, ta amsa tana kallonsu cike da alamar tambaya batareda ya kalleta ba yace "bamuda komai agidan sai farar shinkafa damai kuma batada lafiya shine na kawota taci abinci nikuma fita zanyi" Anty ta harareshi tace "kana aikin me har zaku rasa abinda zakuci acikin gida"? Yadan kalli ummee itama shi take kallo yace "Anty ai kin san komai kuma yanzu napep din nan inaga gajiya tayi kullum tana wurin gyara nidai nace idan ya gyara ya siyar da ita yabani kudina" Anty ta gyada kai tace "to sai kayi yaya kuma" yayi shuru ta tabe baki tace "wanda baiji bari ba dai yaji hoho, kanada mafita anata lallashi waikai mai zuciya wallahi kabini a hankali daga naga yarinyar mutane zata wahala zuwa zanyi indaukota se randa kayi hankali" baisan lokacin da yace "amma dai anty matata ce ko kuma yarinya bata gujeniba za a rabamu muna zamanmu lafiya" cije leben kasa anty tayi tace "kayi wasa da magana ta ka gani" daga zaunen da take tayi kiran laila amma bata amsaba mikewa tayi tashiga ciki saiga laila da gudu ta fito tana kuka har saida ta tunkuda ummee da batama son yin dogon motsi sadeeq ya riketa yana cewa "ke kanki daya kuwa"? Anty ta nunata da charger dake hannunta tace "barni da ita marar mutuncin banza wai baccin safe take haryanzu wannan shine na uku ina zuwa tashinta" ummee ta rike hannun laila tace "Anty ayi hakuri banda duka dan Allah kila gajiya tayi shiyasa" Anty tayi kwafa sannan tace "kije ki karasa aikin dana fara akitchen ki hada abincin da ummee da sadeeq" tana goge fuskarta ta nufi kitchen ummee ko ta wuce dakin anty dakyar saboda yunwa jikinta har rawa yake.

*safiyyah galadanchi*

JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)Where stories live. Discover now