jj24

17 0 0
                                    


*Safiyyah galadanchi*

*JAJIRTACCE ABUBAKAR SADEEQ*

*SHAFI NA ASHIRIN DA HUDU*

Saida ta ajiye masa abincin taga yadda ya sake hade rai ta kalleshi tare da rungume hannuwanta a kirjinta tace "Banyi tunanin ko zaka juyamin baya zai zama da wuri haka ba inaga yau muna cikin sati na hudu da auren mu, abinda nakeso in sani laifin me nayi maka? Abubakar nasan bakada ko aikinyi na aureka to saboda me zaka hanani zuwa makaranta dan bakada kudi? Naji bazan siya maka komai na abincin gidanka ba amma inada kudi bazan hana kaina zuwa makaranta saboda wannan dalilin naka ba" spoon din hannunsa ya ajiye duk da jikinsa yayi sanyi sai yace "Fada kike min yanzu ko kuma fadamin kike ban isa na hanaki ki hanu ba? Banason kiyi abinda ni ya dace nayi kuma ina nan akan bakata" rasa abin cewa tayi kawai sai ta juya ta bar masa dakin sai karfe goma sha daya ta dawo dakin lokacin ya kalli fuskarta yaga tayi wani irin alamar tayi kuka shima din baiyi kukaba amma ya tabbatar da za a auna jininsa tabbas za a samu ya hau irin hawan da sai an kwantar dashi asibiti, har tazo ta kwanta yana kallonta yana zaune yana tunanin rayuwar duniya. Sheshekar kukanta yasaka ya maida hankalinsa gareta a hankali ya matsa kusa da ita ya riko hannunta na dama yadora gefen zuciyarshi yace "Fad'imatu Zara kinajin yadda zuciyata take bugawa? Kinajin yadda tayimin nauyi? Kadan ya rage ta soma yimin ciwo saboda na kasa cika alkawarin dana daukar miki na daukarwa mahaifinki dakuma iyayena, raina yana sake baci idan na tuna marainiyar Allah na dauko na barta take dawainiya da kanta. menene amfanin hakan? Na kasa ciyar dake da irin cimar gidanku, sannan kiringa zuwa makaranta da kudinki? Jikinki kawai nake mora kenan Fadima? Dole naji babu dadi dan Allah kiringa yimin uzuri banajin dadin ganin yadda kike damuwa sanadina harda kuka ummee" shuru tayi tana sauraren kalamansa masu zallar gaskiya tareda lallashi tanaji kuma yadda suke tasiri cikin ranta ya sake cewa "kinji ummee"? Dago kanta tayi tace "kabarni na karasa karatuna hanani zuwa zai iya janyomin matsala, zan lissafa maka konawa na kashe a semester dinnan ka biyani duk lokacin daka samu amma saboda bakada bazai hanani zuwaba dan Allah" ya gyada mata kai dan sai yaji ya yadda da shawararta ta sake cewa "kuma kadaina fushi dani sai naga kamar ka daina sona" yayi murmushi daya bayyanar da hakorinsa yace "na daina" itama murmushin tayi zatayi magana ya rigata yace "kinci abinci"? Ta amsa masa da a'a mikar da ita zaune yayi suka tashi tsaye a atare palo ya zaunar da ita ya shiga kitchen ya debo mata, dahannunsa ya bata saida ta cinye shi gaba daya sannan suka koma dakin.

Kullum da yar buga Buga bugarsa dayake fita badan yanada takamammen aiki guda daya dayake yi ba, napep dinsa ko ansamu mai siya amma sai ya gama hada kudin sannan za a bashi.
Yau bayan ya fita saida yabiya gida dan ummee bata nan suna exam yana shirin shiga ya hadu da Habeeb sai ya dan tsaya yana cewa "ina yini"? Bai kalleshi ba ya amasa masa da "lafiya" kawai saiyacigaba da tafiya dan kallonsa yayi yaga dagaske ya tafi saiya tabe baki yashiga gidan.
Koda ya shiga yasamu Anty zaune gefen gado tana waya da hajiya ga kudi rike da hannunta yasamu wuri ya zauna bayan ta gama ta kalleshi tace "anya abubakar lafiya lau kake? Kaga yadda ka rame kuwa" yadan dafe goshinsa yace "badole na rame ba anty ciwo ma nake a tsaye kullum da zazzabi nake kwana" tace "subhuhanalillahi magani fa"? Ya gyara zamansa yana cewa "jiya jabir ya turamin sunan maganin a waya amma banida kudin da zan siya dan har zanje insiyo sai ga ummee ta kirani in siyo mata abu" anty ta sauke numfashi tace "to dama yanzu nake shirin kiranka  ga sako inji yayanka yace abaka ka" ta dauko kudi gefen pillow ta mika masa ya girgiza kai yana cewa "Anty ki bashi abinshi ni bana bukatar abinda duk yafito daga hannunsa banaso" Anty tayi tsaki ta maida kudin tace "kanka kayiwa mahaukacin banza" ransa ya sake baci ya tuno irin wulakancin da Habeeb din yayi masa yanzu bada dadewa ba sai yayi mata sallama.

Washe gari da safe ummee tace "zanje gida yaufa" yace "to kijira na karbo motar Abba nasan yana gida sai in kaiki
Ki shirya kafin na dawo" ta amsa da to ya tashi ya fita, lafiya lau ta shirya cikin sababbin dinkunan aurenta wamda bata gama sawa ba sai baza kamshi take bata dade da gama shiri ba sai gashi ya iso, ya kaita bakin gate ya tsaya yace "karfe biyar zanzo in daukeki" tayi masa godiya ta shiga gidan shikuma ya wuce gida.
Taji dadin ganin yayyenta har kasa ta durkusa tana gaidasu Ibrahim ya rike hannunta yana murmushi tausayinta ya kamashi yaga ta rame sai haske data kara sannan ta rage Walwala ko duk auren ne, gefe yajata yana cewa "kafin ki zauna kanwata kiyi hakuri ban kiraki ba" tayi murmushi duk da bataji dadin yadda sukayi watsi da ita ba tace "idan nayi fushi daku dan baku kiraniba in kama wa yaya? Ko kadan ban rike ku ba kuma nasan akwai abubuwa agabanku" ya shafa kanta yana dariya yace "lallai kanwata aure ya saka kin kara hankali, fada mini babu matsalar komai ko?" Ta gyada masa kai tace "babu matsalar komai yaya banyi zaton kuna gari ba mommy nazo dubawa" suka shiga gidan tare yana cewa "duk da daddy  ya hana amma zan baki kudi ki bawa mijinki daga ni sai ke kinji" har zata fada masa halin mutumin nata saita fasa tayi masa godiya, daddy a lokacin yana kokarin fita tayi murmushi zata gaidashi ya tareta yana cewa "badai matsala kika zo da ita ba ko? Dama nasan za ayi haka ki fadawa kafaffen mijinki ni bazan siyarda akuya ta dawo tana cimini dangaba dan haka yatafi wannan jajircewar tashi ta cire shi daga cikin talauci babu ruwana danshi yaciwa bakinsa albasa" ta Danne kukan dayazo mata tana bakin cikin batada halin furta amsa gareshi tace "Daddy ina wuni, zuwa nayi kawai na gaisheku" yayi murmushi  yace "muna lafiya kece dai naga kin rame ko kina ciwo ne"? Tace "a'a lafiya lau nake daddy" ya gyada kai yana cewa "toni zan fita ga wannan ki hau adaidaita sahu dan naga mijin naki ma yanzu da kafa yake yawo" ta kalli hannunsa dari uku ne dari biyu sai naira dari, ta girgiza masa kai tace "Daddy nagode inada kudi a hannuna" ya tabe baki tare da dage kafada sannan ya fita, koda ta duba yaya Ibrahim baya gefenta. A wurin ta tsaya tana kuka saboda bazata iya rike wannan bakin cikin ba, shi daddy hukuncin dayake mata yana ganin kamar horone saboda ta zabi wani namiji wanda baida ra ayi akanshi dan haka bayana nufin bazai taimakaba kawai so yake su duka su dandani kudarsu.

*Fiyyah nagaishe ku*

JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)Where stories live. Discover now