JJT23

12 1 0
                                    

*Safiyyah galadanchi*

*JAJIRTACCE ABUBAKAR SADEEQ*

*SHAFI NA ASHIRIN DA UKU*



Dayake shima yunwar yake ji sai ya shiga dakin anty ya zauna kan kujera yana kallon ummee, tunani yake ko ya tambayeta ina da ina ne yake mata ciwo ya dan matsa kusa da ita yana cewa "Honey ina da ina ne yake miki ciwo"? Shuru tayi masa dan gaba daya ma haushi yake bata, ya sake maimaitawa ta juyo a hankali tace "ai kafini sanin inda yake yimin ciwo" dan tallabota yayi ya riketa yana yi mata sannu, mikewa yayi tsaye yace "bari na karbo miki abincin harda yunwa ko" fita yayi daga dakin koda ya shiga kitchen din ya samu anty tana yiwa laila fada ranshi ya dan baci yace "Anty dan Allah anty kibar yarinyar nan haka" hararar shi tayi tace "kamar laila ce zata fara tara samari tun yanzu menene amfanin hakan wai duk mugun bakin rai dakaga tanayi yau jiya bako tayi da wayata suke magana ni bansani ba shine abbanku ya ganta ya korota" kallon laila yayi tayi saurin kallon kasa ya riko hannunta yana cewa "kin gama aikin" ta gyada masa kai ya sake cewa "to zo muyi magana, Anty dan Allah ruwan zafi  wai ummee takeso zatayi wanka jikinta duk ciwo yake" Anty ta dakatar dashi daga fitar da yake shirin yi tace "idan dai kasan yarinyar nan batada lafiya sosai kayi magana akaita asibiti" ya sosa kanshi yana cewa "a'a Anty jabir yace zaizo ya kawo mata magani na fadamai abinda yake damunta" ta gyada masa kai kawai tana share kitchen din.

Kafin tayi wanka saida suka ci abinci ya fita ya karbo maganin daga wajen jabir sannan ya fita wajen harkokinsa ita kuma lokacin anty ta hada mata ruwan wanka ta shiga tayi tana fitowa kwantawa tayi sai bacci sai karfe uku anty tace "Ummee wannan bacci haka bazaki salla bane" bude idonta tayi tana kallon Anty dakyar ta tashi zaune maimakon tayi magana sai hawaye dan gaba daya jikinta ciwo yake sannan kuma kanta yayi mata nauyi har cikin ido, anty ta kalleta da mamaki sai taga ta nufi toilet tana tafiya dakyar kyaleta tayi har tayi salla sannan tace "meyake damunki"? Kasa tayi da kanta tace "babu komai Anty" to ita ta ina ma zata fara fada mata abinda ya faru akwai kunya gaskiya amma kuma idan tayi shuru itace zata cutu. Anty ta sake cewa "banason shirme wane irin ciwon jikine sai kace wadda tayi dako wuni guda kokuma akayiwa duka, ko dukanki yayi"? Ummee tayi saurin daga kanta sama ta girgizashi tana cewa "A'a wallahi" anty tace "to menene haka"? Saida ta runtse idonta sannan ta nuna mata inda yake mata zafi tana cewa "dama jiya da dare ne, shine nan yake min zafi kuma jikina naciwo da kaina" tsaki Anty tayi tace "shine kika biye masa kina zaune da ciwo? Shifa ba ruwansa namiji ne ina gaya miki ko a haka kuka koma gida zai sake nemanki ne idan yaga dama ke ciwo ya zamewa matsala" shuru tayi hawaye na cigaba da zuba Anty ta sake cewa "bari muyi sallar laasar kafin lokacin ruwan dana dora ya tafasa" kwantawa tayi kan carpet din tana sauke ajiyar zuciya har tajiyo kiran salla ta tashi tayi, tana daga zaune ta dora kanta gefen gado Anty ta shigo da roba mai fadi da bucket cike da ruwan zafi ta shiga bayin ta juyesu a roba sannan takira ummee, shigowa tayi dakyar Anty tace "zo ki cire hijab dinnan ki shiga ruwan ingani dan nasan shirmenki zaki iya ragewa ko ki kara ruwan sanyi" batayi musu ba ta cire har pant sai towel din Anty data daura da zatayo wanka.
Ba karamin dadi tajiba shiga ruwan nan har suka Huche anty ta kara wasu sannan tabarota tayi wanka da ruwan. Saida taci abinci sannan tasha panadol ta sake kwantawa Anty sai sannu take mata koda dare yayi tareda jabir sadeeq ya dawo ya sameta zaune kusa da Anty tana yi mata kalaba dan ita bata kitso.

Yayi wani zuru dashi alamar dai yaji jiki yau dinnan, murmushin yake yayi yana gaida Anty ta amsa tana cewa "kai wannan idonka kenan tun safe" ya sosa kai yana kallon ummee yace "ya jikinki" kasa amsawa tayi dan anty na wurin saboda ta riga tasan komai, yadanyi mamaki da bata amsa ba dan ya lura kamar kunya take ji ya sake kallon anty yace "Abba ya dawo"? Ta girgiza kai tana cewa "nasan dai yanzu zaka ganshi ya dawo" ya furzo da iskan bakin Shi yace "motarshi nake so na tafi da ita yau gobe da safe in kawo mai idan zan fita" Anty ta tabe baki tace "kai ka sani dai yanzu Allah yasa ya baka din" tana gama fadin haka ta fita daga dakin kamar jira yake yakoma kusa da ummee yana shafar kalabar da akai mata yace "yajikinki nace" ta harareshi tace "naji sauki, bayan katafi ka barni saida ka saka asirina ya tonu" yayi murmushi yace "bangane ba nifa ban fadawa anty komai ba" "Aini na fada mata dan wallahi ni kadai nasan me nakeji dazu" ya zaro ido yana murmushi yace "kai ashe yau anty tasan mun girma" dukan wasa tayi masa a kirji ya rungumeta yana dariya yace "na cuci kaina da sai yau nasan yadda abin yake dan Allah idan mun koma yau ki karamin" da sauri ta daga daga jikinsa tana cewa "wa? Kai nifa yau nan zan kwana ma haka kawai" ya cije lip dinsa na kasa yace "hauka kikeyi yarinya aikin lada ai kuma tunda aka fara sai an karasa" yana rufe bakinsa Anty na shigowa ta mika masa makullin mota tace "Abbanku yace ku tafi dare yanayi" karbar key yayi ya fita ummee tayiwa anty sallama anty tace "ki kula dai idan kun isa gida ki sake zama acikin ruwan zafi bama yau kadai ba duk sanda kike jin haka Allah ya bada zaman lafiya" godiya ta sakeyi sannan ta fita, saida ta shiga ta gaida Abba yace "yajikin mamanku tace bakijin dadi" ta amsa da taji sauki sannan suka fito. Leda guda biyu ya fito dasu bayan sun isa gida masu girma ta kama masa daya suka shiga tace "Allah ya taimakemu yau sunbar wuta" yayi murmushi yace "karki damu idan nayi kudi zan siya miki mikano insa miki solar" dariya tayi tace "Allah ya nuna mini" ya amsa da ameen washe gari tayi shirin zuwa makaranta ya kalleta yace "wai bazaki bar makarantar nan har wani sati ba" ummee tayi shuru tace "saboda me" yana shafa mai a hannunsa yace "saboda banida kudi" ta mike tsaye tana kokarin saka hijabinta tace "da akwai kudi awurina ai" "Na fada miki ai banason kinayin abinda ya kamata ace ni nayi ki zauna gida yau bazakije makarantar ba" cike da mamaki ta kalleshi tace "kwana nawa ana lectures banje ba idan na tafi da kudina a goshi zan makala ince bakai ne ka bani kudin zuwa ba? Sannan fa muna kusa da exams I can't be skipping lectures  akan wannan dalilin" shuru yayi mata tayi tsaye tana jiranshi ameera tayi kiranta awaya yana saurarenta "na shirya ke nake jira" bai mata sallama ba ya fita tayi zaton ma zai dawo sai taji shuru har ameera ta iso rufe gidan tayi Ameera ta kalleta tace "Amarya ya jiki"? Kamar bazata fada mata ba sai tace "naji sauki, mutumin can fa ya bata mini rai yau, saboda bashida kudi bazanje makaranta ba" Ameera ta danyi shuru tace "dayawa maza basa son haka shi a ganinsa kasawarsa ce ace kinayin abinda yakamata ace shine yayi wani koda mai kudine indai kikayi abu da kanki saiyaji babu dadi" cikin bacin rai ummee tace "Nawa yakedashi koda na aureshi, nasan bashida ai na nuna naji na gani bai kamata yayi min haka ba abinda yafi bata mini rai baifi wai ko sallama baiyimin ba yau" Ameera tayi murmushi tace "zai sauko ne ki kyaleshi badai shekaranjiya ya fara angonci ba bazai iya dogon fushi dake ba, kinga inda nake kwarar Dr kenan daga yayi fushi dani bai wuce awa biyu dole ya sauko" shuru ummee tayi dan batasan me zatace ba saida suka danyi tafiya ta sake cewa "nifa abinda yake bani mamaki yasan fa dole akwai taimako tsakanina dashi, kinsan kudin dayake account dina amma shekaranjiya fa shinkafa fara da manja mukaci gidan nan yahana insiyo koda indomie, jiya sai gidansu muka tafi acan muka karya ma" Ameera ta kalleta da dan tausayi tasake cewa "karki damu fa aintunda yake kamada masu kudi nasan saiya tara haba yau dama zanga romeo da Juliet a rana haba dai" dariya sukayi a tare.

Karfe biyu ta dawo gida salla kawai tayi ta shiga kitchen ta dora tukunyar tuwo ta zauna tana kallo har laasar karfe biyar ta Kammala aikinta tana mamakin yadda yau ko flashing bai mata ba har zuwa lokacin kuma bai dawo ba. Palo ta zauna tana kiran mommy suka gaisa mommy tace "amarya ya gida ince dai lafiya kuke ko" ummee ta amsa da lafiya lau suka ci gaba da hira har taji an saka date din auren wata yar uwarsu lokacin suna exam ma suna maganar ya turo kofa da sallama ciki-ciki tabishi da kallon mamaki bai zaunaba yace "ki kawomin abinci na daki" bai jira amsarta ba ya wuce sallama tayiwa momy sannan ta shiga kitchen dan dauko masa abincin.

FIYYAH NA GAISHEKU

JINI YAFI RUWA KAURI

JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)Where stories live. Discover now