*Safiyyah galadanchi*
*JAJIRTACCE ABUBAKAR SADEEQ*
*SHAFI NA TALATIN*
Koda ta shiga dakin har yayi bacci shirin kwanciya tayi yadda ta saba taje gefen gado ta kwanta bayan ta kashe wutar,da asuba daya tashi saida yayo alwala yazo tashinta yaga bata kan gadon bayan ta kammala salla yanata zuba ido yaganta yaga bata dawowa ba har haske ya fito.
Ita kuma ranar batada lecture sai shabiyu shiyasa kawai bayan ta kammala salla takoma bacci a dakinta ba karamin haushinta yaji ba saida yagama fushinsa baiji motsinta ba sai ya leka dakinta lokacin ta fito daga wanka tana sauri takusa makara, shiga dakin yayi ya rike ta yana cewa "meyasa zaki baroni nikadai" dauke idonta tayi daga kallonsa ya juyo da fuskar yana cewa "kalleni, ni zakiyiwa fushi" kwace jikinta tayi tana cewa "dole nayi maka fushi saboda bakada dalili akan abinda kakeyi" turare take fesawa saiji tayi ya zare mata towel yana cewa "zoki bani abinda kika hanani jiya" kokarin barin jikinsa take ya riketa sosai tace "inada aji shabiyu ka kyaleni" bai saurareta ba saida yasamu abinda yakeso amma batareda gudunmawarta ba, ba karamin baci ransa yayi ba mikewa tayi zata shiga toilet ya danneta yana cewa "wane irin zama kike so muyi"? Shuru tayi masa tana ssurarenshi harya saketa ta tashi tsaye tace "irin zaman daka zabar mana muyi" sake baki yayi yana kallonta harta shige toilet, fita yayi daga dakin itama bayan ta fito shirinta tayi ta saka hijab fuska ba walwala tafito zata wuceshi yace "ummee" ta tsaya kawai ba tareda ta juyo ba yace "yau bazaki makaranta ba sai kinzo kin fada mini wanene yake zugaki kiyimin rashin kunya" juyowa tayi tace "ni babu wanda yake zugani sannan ba rashin kunya nayi maka ba, kuma bayan haka kace na daina shiga abinda bai shafeni ba na daina shiga gara na tarkata na koma gefe tunda a hanya na hadu dakai" saida yayi shuru na dan lokaci sannan yace "zoki zauna muyi magana" kallon wayarta tayi tana zama sannan tace "ka hanzarta zan makara" danne zuciyarsa yayi saboda bayaso ya aikata mata abinda yake tunani a ranshi yace "ummee maganar nan inaso mubarta tsakanina dake karki sake tayar da ita mu dawo da zamanmu kamar da sannan kisani idan karatun danayi ne nafiki sonshi dan baki fini son na wadata da arziki ba amma na hakura dashi kinko san ba karamin dalili bane" tabe baki tayi tace "banfika son ka wadata ba amma ka sani da ace baka aure sannan bayan aure ace ba a haihuwa a auren to har sanaa ka dainayi ka dawo ka zauna, boko ba shine arziki ba duk abinda ka karanta Allah seyaga damar baka arziki amma tayaya saboda zuciyarka kawai zaka tauye Hakkin mutane da yawa" "hakkin wa na tauye"? Ya tari numfashinta cikin bada tabbaci tace "Anty da Abba sunada hakki akanka domin yanzu ya kamata ace sun samu mai dauke musu wasu nauyi dake kansu, a halin yanzu ace laila ta isa aure abin kunya ne a gareka ace gidanta batada cokalin da zata daga tayi begun gaba dashi da sunan kai ka siya mata" ya sake cewa "kenan sanaar da nake batada amfabi bazata iya zama silar da zanyi arziki ba, yanzu da bakinki kika gama fadamin Allah ke bayarwa" "sanaarka ba sanaa bace domin ko kwakkwaran jari bakada shi sannan ka sani Allah sai ya tambayeka hakkina ni matarka da Hakkin abinda yake cikina danka kenan karkayi wasa da damar da Allah ya baka" a tsawace yace "ke baki isa ki fadamin abinda ya dace nayi ba sannan kije idan akan wannan maganar zakiyita fushi dani kiyi karki fasa bazanyi abinda nake ganin shine daidai arayuwata ba duka yaushe kika sanni ke kin san abinda ya faru ne zaki ringa zaqewa" "ba zaqewa nake ba kuma ka sani zan nanata maka sanaar ka ba sanaa bace dan ko jarin dana ara maka banga alamar fitar koda uwar kudin ajiki ko agidanka ba sannan ka sake sanin cewa zan yita fushi kamar yadda ka bukata kaikuma kayita farin ciki da rayuwarka yadda take" take idonsa suka yi ja, wani a duniya karo na biyu acikin mafi kusanci dashi sunyi masa gori akan taimakon da suka yi masa lallai koda zaiyi dako seya biyata kudinta sannan ya gama son abin hannunta har abada" koda ya Ankara bata wajen ta fice, ranar ko ruwa bai saka a bakinsa ba har laasar ta dawo anan palo ta sameshi bayan sallama ta gaidashi kamar dole ta wuce dama da zazzabi ta dawo gidan key ta saka ta rufe dakinta sannan ta zauna tana tunanin abinda Anty ta fada mata tace "ummee kin karasa lalata magana amma bazamu cire rai ba, sedai ki sani dalilin gori yasaka sadeeq ajiye takardun nan amma gara da kika nuna masa cewa shi ba kowa bane face dan Adam farkonsa haihuwa karshensa mutuwa bai isa yace baya hakuri da laifi ba dan bai wuce amaimaita masa irin laifinba kokuma wanda ya fishi muni ki kara jajircewa kuma karki nuna karaya duk yadda kika damu daki kula dashi" ajiyar zuciya ta sauke tare da shigewa bargo saboda sanyin da take ji sai kusan magrib da taga tayi amai sau biyu sai ta fito palon ta sameshi yana zaune tace "zanje chemist karbo magani" batareda ya kalleta ba yace "Allah ya kiyaye" fita tayi dama izini take nema kuma ta samu.Saida suka share sati daya babu mai kula wani ko a wurin bacci kowa gefe daban yake kwanciya. Shine dai yaga babu sarki sai Allah yau ya fara dakonta tana fitowa ya tareta yana cewa "ummee kizo muyi magana dan Allah, kiyi hakuri akan maganar dana fada miki kinji amma kibar maganar nan Allah zai cireni daga wannan jarabawar" kwace hannunta tayi tace "Abubakar rayuwarka ce kayi yadda kaso da ita amma ka sani indai baka ajiye wannan zuciya ba to nima bazan canza ba amma kuma bazan sake yi maka magana ba kuma kasani wallahi duk ranar dana gaji tarkata kayana zanyi inbar maka gidanka" shuru yayi dan bai taba tunanin zata iya yi masa haka ba, ranar wuni yayi jiki a sanyaye dare yayi yanaso yayi lamarin duniya babu hali hajjaju ta kama ta tsare gida.
Washe gari suka tashi da azumi hakanan ta daukeshi dan a tunaninta tunda bazata iya cin abinci ba gara tayi azumin, waya ta kira wani dan uwansu dayake mata kirki matsayin kaninta ne bai dade ba ya iso ta bashi sakon abubuwan da take bukata agidan koda ya kawo mata ana kusan sallar laasar dakyar ta fita ta shigo da kayan yana kallonta yace "wanene wannan kuma kayan na meye wannan"? "Lawal ne, kuma kayan bukatata ne na bayar ya siyo min" ya tamke fuska yana cewa "wallahi kayan nan karki bari su kwana a gidan na fada miki dan iska kika maidani ko me"? Bata kalleshi ba tace "kana nufin kenan harni nabar gidan nan" tsaki yayi yace "duk yadda zakiyi ya rage naki amma ki fitar min dasu daga gida kafin ranki ya baci" yana gama fadar haka yabar gidan, ranta yakai koluluwar baci har saida ta fashe da kuka cikin bacin rai takira wayar Samuel da har ta mance tanada shi kwatancen gidan tayi masa yazo da motar da ake yan bukatu agidansu, katon akwati ta cika dakayan ta yana zuwa ta sakashi ya loda kayan abincin data siyo tace idan ya kaita gida yaje yakai kayan gidansu sadeeq yanawa Anty injita.Momy na ganinta saida gabanta ya fadi.
YOU ARE READING
JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)
Fanfictionlabarin ya kunshi soyayya da k'iyayya ya kunshi Arziki da talauci.