JJT 38

15 1 0
                                    

*SAFIYYAH GALADANCHI*

*JAJIRTACCE ABUBAKAR SADEEQ*

*SHAFI NA TALATIN DA TAKWAS*

Ameera ta zauna tana cewa "karki cemin laifinsa kika gani" karamin tsaki ummee tayi tace "ya bazan ga laifinsa ba  tunda yasan bazan hana a dauki jariri ba duk wanda yazo ai saboda yaganshi yazo, ina kika baro baby kuma"? Ameera tace "tana wurinsu momy ya ake ciki ne wai seji nayi kawai kin haihu " tabe baki ummee tayi tana cewa "Anty hana tafiyar tayi saida Abba yasa baki rabon ayi dai yasa na nace seyaxo ya daukeni muna isa ko abinci banci ba abu ya tasomin gadangadan ko soyayyar da muka je yi bamu samu munyi ba koda na awa daya" dariya sosai ameera tayi tana cewa "maganinku kenan ai, nidai miko mini shi in fara karya dokar ubanshi tun yanzu" ummee tace "gakinan gashi ai ki daukeshi" Ameera ta dauko shi tana kallonshi tace "Amma yaron nan dake yake kama kuma wallahi dagaskiyar babanshi karki bari aringa daukarshi any how kar ajefar dashi yayi karami sosai" ummee tayi fuskar tausayi tace "Saima kinga yadda yake wahalar dani cikin dare, ni har yanzu ba iya daukar shi nayi ba idan zanyi breast-feeding dinshi se an doramin shi saman pillow sannan ga bakin dan mitsitsi yayita ihu seda saka yatsana na tura mai" Ameera tayi dariya tace "duk kankantar wannan abin shine zai kasa shiga bakinsa? Ku ringa bashi a feeder mana" tabe baki ummee tayi tace "wallahi yanzu baya kamawa kamar yasan banbancin su kinga ko ruwa yanzu momy da spoon take bashi" tana rufe bakinta saiga momy ta shigo part din tace "Ameera dauko yaron nan kizo Ema yakaiki gidansu inda kakarshi ta ganshi yau kwana biyar kenan" ameera ta mike dashi a hannunta tabi bayan momy.

Koda suka dawo part din ummee a cike yake da matan su Hydar da sauran yan uwa anata hira sai karar massage taji a wayarta ta duba taga na farko alert ne daga sadeeq dubu dari biyar sai massage dinsa yana cewa ta siya kayanda zatayi amfani dashi gobe da safe kayan daya turo zasu iso za a kirata ta tura a karbo. Bayan ta gama karantawa sai ta kirashi bai dauka ba, ameera ta tacewa dan Allah ta tambaya mata tela zata samu dinki kuwa jibi da yamma, tela dayasan lokacin samunsa ne yazo ba gardama ya amince, sai ta siya wasu kayan guda biyu ta aika masa, washe gari koda aka karbo kayan tasha mamaki dan batayi tsammanin haka ba,  sai ta kira Ema shiya kawo kayan ko momy bata sani ba tasa shi yakai gidansu sadeeq dan tasan aladar mutanen sokoto sai an kawo barka a kayan da sadeeq ya turo abunda babu sedai in bai san dashi bane, Anty tana ganin kayan ta kira sadeeq tace shi yayi aiken akwatuna da kayan barka, sai lokacin kanshi ya kawo wuta ya tuna Anty ya kamata ya turawa sai ya wayance yace "Eh idan babu damuwa yau akai kayan" anty tace "bari na kirawo jama'a kuma kayan akwai kayan wanka da motar itacen dafa ruwan zafi" sadeeq yace "kafin suzo duk an tanadi wannan ni yanzu ina wani aiki ne kinsan gobe zamu taho bana son barin aiki" tayi masa sallama tana jinjina kayan dan ba karamin kokari yayi ba duk da tasan akwai saka hannun yayanshi.

Washe gari da suka zo anty ta kalli yar autarta da take fushi batada kayan sawa ranar sunan tayi shuru tacewa sadeeq "wai kashemini laila kuka yi ne da babu mai kulawa da ita? Fisabilillahi gobe suna ko kayan da zata saka babu" sadeeq ya sosa keya yace "ayi hakuri Anty insha Allahu zata saka sabon kaya gobe, laila zo ki rakani unguwa" tana fushi dan ita bataga alamar zata samu wani sabon kaya ba ta saka mayafinta tabi bayanshi saida ya tafi da ita gidansu yace ta kama masa ya share dakinsa da palo, bayan sun gama gyarawa ya fita da ita shago ta sau leshi guda biyu masu kyau da gyale da takalmi harda jaka sannan ya tafi da ita wurin wani telan ummee da take bawa dinki tun tana secondary school yace yayi masa kokari gobe ze zo ya karba.
Ba karamin dadi laila taji ba tana ta yi masa godiya.

Sai dare ummee ta kirashi tace masa "sweety ya maganar sunan jaririn nan wai baka ce komai ba" sai lokacin yace ta jirashi gashinan zuwa ya tafi wurin anty dan neman shawara tunda habeeb ya saka sunan Abba wanne ya dace ya saka habeeb ko kuma ya saka sunan Daddy Anty tayi  murmushi tace "Abubakar ummee tayi diya yarinya mai hankali nidai idan kana son habeeb din kabari sai nan gaba ka saka mata sunan mahaifinta zatayi farin ciki sosai" yayi murmushi shima  yana sosa gemun sa yace to "bari naje ki fadawa abba yanzu amma karyaji babu dadi anyanke hukunci bai sani ba" ta amsa da to yana fita ya kira habeeb ya fada masa habeeb yace "ashe da anyi hauka danni yaro tuni nayi masa huduba da sunan mahaifin nata" Sadeeq yayi dariya yace "ai faduwa tazo daidai da zama kenan" sallama yayi masa shikuma ya nufi gidansu ummee, palon dake part din momy ta kaishi ta dauko mai babyn dake ta ihu babu gaira babu dalili da alama yanada fitina, sadeeq yace "meyake damunsa yake kuka haka"? Ummee tace "kukan banza fa, ba abinda yake damunsa" tabe baki yayi ya janyo waya ya kira jabir yana cewa "don Allah kazo ka duba mini yaron nan lafiyar sa kuwa ance kwana biyun nan yanata rigima" dariya jabir yayi yace "ganinan zuwa amma ka fito ka shiga dani kar a hanani shigowa inji haushi" zama yayi yana cewa "fara bashi abincin shi dai kafin jabir din yazo" saida ta dora pillow kan cinyarta tace ya dora mata shi sannan ta fara kokarin bashi yana rike dashi yaki sakewa dan gani yake kamar zai fadi" ummee tace "ni har mamaki yaron nan yake bani jiya fa tun karfe ukun dare bakinsa yake tsotso har biyar da rabi daga na cire seya fara kuka  dakyar naga yayi bacci" sadeeq yace abincin sa dabai ci aciki bane yake karasa ci anan" dariya tayi tace "zan dai tambayi anty inji ko kaima haka kayi fitina" zai bata amsa wayarsa tayi kara ya dauka yana cewa "ummee rike shi da kyau bari na karaso da jabir din gashinan ya iso" fita yayi babu dadewa sai gashi ya dawo tareda jabir, alama yayi mata data rufe jikinta mana, zare babin tayi ta gyara rigarta tana mika masa shi, jabir ya karbe shi yana kallonshi yace "a ido ai lafiya lau yake ko bayan kukan da yake jikinsa yana zafi ko mura" ta girgiza kai tace "ko daya kukan ne dai kawai sai cin tsiya kamar gara" jabir yayi dariya yace "lafiyarsa kenan kedai kiringa cin abubuwan da zasu kara miki madara yadda zaiyi girma da wuri ko yanzu ai wasu jariran da ake haifa da wata tara bazasu fishi girma ba kila sedai nauyi"  sadeeq yace "ko a hada masa da madara" ummee tace ai "momy ta hana tace bayanzu ba sai ya kara girma" bai musa ba yace "to shikenan maganar suna dama zan ce miki an masa huduba da sunan daddy dan haka sai ku nemi alkunya ku saka masa" muryarta har tana rawa tace "don Allah"? Yace "wallahi kuwa dan haka saiki fadawa momy da dady, ina baki shawara tunda sunansa Ibrahim kuyi masa lakani da khaleel ko mu'azzam" jabir yace "sosaima dan duk sunansa ne karku je ku jajibo mana masu kamada sunan indiyawa mukasa fada" tayi dariya kawai takasa magana ma saida jabir ya lura da yadda take kallon mijinta sai ya ajiye jaririn yana cewa "idan ka gama ka sameni a waje zan danyi waya, maman baby gashi ayi hakuri asiyawa mai sunan dadi pampers" godiya tayi mai sosai dan kudin nada yawa kusan dubu hamsin ne, kamar jira take ya fita ta koma kusa da mijinta ta zauna kan cinyoyinshi......

JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)Where stories live. Discover now