SAFIYYAH GALADANCHI
JAJIRTACCE ABUBAKAR SADEEQ
LAST PAGE
"Yarinya jego fa kike, sauka karki janyomin jidali" dariya tayi tace "haba dai godiya fa zanyi maka ka bari kaga kalar godiyar da nakeso in nuna maka" tabe baki yayi yace "Nifa gauro ne yanzu kibari sai kincika kwana arbain in zaki dawo ki dawomin da godiyar amma don Allah kiyi hakuri yau kam" dariya tayi tana mikewa tsaye shima tsayen ya mike yana cewa "inaso in baki kudi saboda hidimar biki amma account dina yayi kasa ki fadamin nawa zan baki amma karki talauta ni pls" murmushi tayi tace "kaje konawa ne a account dinka ka raba uku ka turomin kaso daya" ya girgiza kai yana cewa "kin tabbata babu matsala" "babu matsalar komai sultan Allah ya saka da alkhairi" ya amsa da ameen yana kama hanyar fita daga palon ta rako shi har waje sannan tadawo palo zaman shayarda yaronta mai ci kamar gara.
Ba karamin dadi Daddy yajiba har saida yabawa yaron kyautar wani gida nashi sannan yabawa uwarshi kyautar kudi da ya kasance sirri ya kuma sauya mata mota bayan kayan jariran daya bawa momy kudi ta jibgo ma baby, ranar da akayi suna har almajiran unguwar basuyi yunwa ba abinci da nama da drinks shi kanshi dady a part dinsa saida abokanansa sukaci suka sha da dare.
Bayan kafafuwa sun lafa Aisha da ameera suka rage a part din ummee aisha tace "wai ummee zaki iya yawon makaranta da wannan babyn kuwa"? Karamin tsaki tayi tana kokarin goyashi tace "yazanyi to? Wallahi harna fara tausayin kaina wani irin bacci nakeji amma nasan ko yau bazan yishi ba" Ameera tace "inda ma momy ta yadda a hada mishi da madara idan yaci gaba da haka wallahi duk sai ya karar dake" dariya Aisha tayi tace "zai daina ai haka hanan tayimin da farko amma gaskiya be kai nashi ba, dan buhu da rabi ga murya kamar gyare" ummee zatayi magana wayarta tayi kara koda ta duba sadeeq ne saurin dagawa tayi tana gaidashi bai amsa ba yace "meyasa zaki barshi yanata kuka haka" ta girgiza kai tace "wallahi a goye nake dashi kukan daine nagaji da tsotso shiko baiki yakwana yanayi ba ko abinci ya hanani ci tunda akayi magrib ya tashi daga bacci yake kuka" karamin tsaki sadee yayi yace "hakuri fa zakiyi ummee kowace uwa haka tayi fama da danta amma ba a cewa angaji kin sauke shi ki bashi yasha bari na aiko miki da fura mara sanyi kisha amma don Allah kidaina barinshi yana kuka haka" gaba daya Jintayi kamar da ace zata iya kwadawa sadeeq mari dakyar ta hadiye kukan daya tsaya mata awuya tace "to shikenan" murmushi yayi yace "saukeshi ina ji kibashi sai muyi magana " ajiye wayar tayi gefe ta sauke shi fuskarshi hartayi ja saboda fitina, saida ta dungure masa kai sannan ta bashi sadeeq yanajin yayi shuru yace "ko ke fa ai gara haka da wannan ihun da yake, Anty ce tacemin dazu da yamma kin aiko da sako wurinta seta kirani inzo ingani ummee kayan nan basuyi yawa ba? Kudin dana baki fa nasan ko rabinsu bazai siya ba" tayi dariya tace "momy ce tayi sannan ita tabani tace akaiwa anty ta bawa mutanen ku babu wani yawa wallahi" ya sauke ajiyar zuciya yace "toshikenan sultana Allah yabiya ku yayi miki albarka" ta amsa da ameen yayi kasa da murya yana cewa "ummee nayi missing dinki wallahi jiya sau biyu ina mafarkin ki tunfa da mukazo salla" mikewa tayi daga wurinsu ta shiga daya dakin tana cewa "to kayi hakuri ai kaga ko yanzu ma ina kan lokaci kuma ga mutane acikin gida balle ince kazo" ya sauke ajiyar zuciya "aiko kince inzo ma bazan zo ba amma ina cikin wani hali" dariya tayi tace "to yanzu dai bari inje inji dasu ameera kafin azo daukarsu" muryar tausayi yayi yace "ni bazaki dan tai make ni ba pls muyi vd call" dariya tayi tace "sadeeq anjima zamuyi amma ba yanzuba" "to Allah ya kaimu sai anjima" tana fita taci karo da ameera zata wuce har anzo daukarta hakuri ta bata sannan ta jaya daya dakin tace "gashinan duk abinda ki dauki duk abinda kike so dan kinsan dai bazan cire miki ba naman suna kuwa ba binki zanyi dashi ba tun yanzu ki shiga kitchen ki deba ki tafi dashi inba haka ba gobe zaki dawo ne" Ameera tace " wannan yaron dai sauna dashi kina bashi nono daga tsaye" zama tayi gefen kujera tana cewa "ubansane sarkin daukar hankali yake so ya dameni yatayar min da hankali ya mata harda fitinarshi ta tsokano naquda" ameera tayi dariya tace "ai duk mazan haka suke yanzu yadda kikasan cin tuwo haka suka maida abin Allah dainya bamu hakuri" ameen ummee ta amsa suka fito tare ta tura aka daukarwa Ameera kayanta har mota ta dawo wurin Aisha ta sameta a zaune da babynta ya tashi daga bacci tace "ga wayarki tana ringing Aisha" tabe baki tayi tace "Dr ne kuma ni nace bazan koma ba yaki ya sakeni hakuri yake bani in koma yaci gaba da azabtar dani" ummee tace "Aisha bafa komai da muke gani yake zama daidai da rayuwarmu ba ko yanzu yasan kinada amfani tunda wata nawa baki gidanshi tun bayan salla karama lokacin baki dade da haihuwa ba ma ga yarinya nan har ta iya zama kuma kina zaune a gidansu" Aisha tace "ba gidansu nake ba dan daina kulani sukayi tunda dama ba sona suke ba saina roki alfarma wurin baba zan koma gidan kanwar umma yanzu acan nake kullum fa saiya bini can sannan wayata har kasheta nake dan yana hanani bacci, ummee banice a gaban Dr ba da zai ragamin kodan zumunci da tsohon cikina yake dukana sannan ko cikin yan uwana baya bari ina shiga duk inda naje banida sakewa ranar agaban kawayena ya Mareni wai na saka mayafi na bude kirjina ina nunawa mazan kan hanya, sannan ya hanani komawa gida haihuwa ko mai dafa mini ruwan zafi banidashi naje nakai kara wurin babarshi se cewa tayi na cika korafi hakanan se makota sun taimaka sun shigo suke rage min aiki bayan haka kuma ranar dana fara salla bai jira nayi kwana arbain ba haka yazomin nace masa yayi hakuri seda ya mareni sannan be fasa ba, bama wannan ne yafi konamin raiba irin yadda yake zomin babu wata kulawa bansan inda ya samo wannan dabiar ba dan ba haka yake ba farkon auren mu" ummee tace "to ai ke zaki koya mai maza fa rawar jiki garesu sannan sunada son kai duk yadda yaso yakai gareki karki yadda sai an taba wancan fannin sannan tunda wannan ne karo na farko da kika bar masa gidansa kuma yanata yawon dangi abaki hakuri yana lallashinki kiyi hakurin ki koma idan bai canza ba zan baki goyon baya ko kotu ne ki kaishi araba auren, yanzu ki daga wayar shi" dagawa tayi dan ta yadda da ummee da son da take mata akwai haduwar jini sosai a tsakaninsu sallama tayi masa ta gaidashi ya amsa yana cewa "Nana ina kika je nazo wurin umma tace kina can mama tace biki kikaje inane wurin bikin"? A hankali tace "ummee ce ta haihu yau ake suna ina gidansu ma" yace "ganinan zuwa don Allah kibari mu hadu" ummee ta gyada mata kai tace "to seka zo" ummee tace "dama gareki fa Aisha karki wasa da ita idan kin koma karki nuna masa tsoro ko shakkarsa duk abinda kikeso kiyi magana kai tsaye amma a cikin kissa da soyayya inason inji kykkywan labari" murmushi Aisha tayi suka ci gaba da bawa juna shawara har ya iso takaita dakin tace ta debi abubuwan da takeso amma sai ta debi kadan saboda kunya, kyaleta tayi ta daukar mata abubuwan kitchen masu amfani da sabon zanen gado sannan ta dauko mata pampers dinda aka kawowa muazzam mai guda arbain da hudu ta hada mata a manyan ledoji sannan ta hada mata da naman suna gasashshe, godiya tayi mata sosai ta rakata har wurin Dr din bayan sun gaisa yabata kudin barka dubu goma asiyawa baby pampers ummee tayi godiya tace "Dr kana fa wasa da damar ka, wallahi In kayi sake ka rasa kawata ni zan zaba mata miji kuma saurayi" dukda maganar ta sosa masa rai amma seyayi murmushi yace "ayi hakuri insha Allah zan kiyaye" tace to saida safe.
YOU ARE READING
JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)
Fanfictionlabarin ya kunshi soyayya da k'iyayya ya kunshi Arziki da talauci.