*Safiyyah Galadanchi*
*JAJIRTACCE ( ABUBAKAR SADEEQ)*
*shafi na biyu*
Mai kudin gaske ne kwatanta irin arzikin da Allah yayi masa bata lokaci ne, kallo daya zakayiwa katafaren gidan da yake ciki ka fahimci cewar dukiya da arziki azaune suke da Kansu cikin wannan gida gidane da a kalla zakayi tafiyar minti biyar da kafa kafin ka karasa cikin gidan part dinda suke ciki kuwa zakayi zaton unguwa guda ce saboda yawan su haske da tsarin gidan yanada matukar daukar hankali. Motocin dake ajiye a gidan bazasu kirgu ba manya manya irin na masu fada aji a wannan kasar.
Gidan Alhaji Ibrahim Dan madina kenan yana da arzikin da har jikokan yayansa bazasuyi talauciba ko da basa aikin komai. Matar sa daya a halin yanzu hajiya Aisha yaranta maza biyar batada mace ko daya, ya taba aure Inda matar ta haifi mace bayan shekaru uku da haihuwar macen ta sake daukar ciki Allah bai yadda ta haifeshiba ta rasu dashi ajikinta wannan ya data bari itace ummee yar gatan daddy da mommy, yar gatan yayyenta maza guda biyar duk wanda zai bude bakinsa a gidan sai ya tabbatar ya ambaci sunanta kafin ya rufe.Hajia Aisha tana matukar son ummee saboda yadda take son yaya mata Allah bai bata ba bayan rasuwar mahaifiyar ummee sai take ganin kamar kyauta ce Allah ya bata dan haka batada amar ummee, kamar yadda suka saba bayan ishai dukansu zaune suke a babban palon gidan Daddy ya sauko daga can part dinsa sanye da kananan kaya jeans baki da Riga mai dogon hannu fara tas, zama yayi gefen mommy fuskar nan tashi daure tamau duka yaran suka gaida shi ya amsa yana kallon ummee, mikewa suka soma yi zasu fita yace "No kuyi zamanku infact magana ma nake son son muyi akan ummee da wancen yaron" kallon shi tayi tana jira taji mai zaice "gobe zanje Dubai inaga zanyi kamar sati biyu idan yadda nake so ya samu har China zanje idan na dawo ummee da lukman zasu wuce UK shi zaiyi masters ita kuma zatayo degree na fahimci saboda suna ganin juna ne wasu abubuwan suke yinsu"
"Daddy meyasa wannan karon bazaka tayani son abinda nake so ba"? Yayi saurin bata amsa yana cewa "saboda abinda kikeso din bai dace dake ba, ko abincin da kike ci bazai iya tsarewa ba ballantana suturar dakike sawa ba matsiyaci ne fak'iri ne"
Ranta ya baci sosai ta rasa abinda zatace ta mike tsaye Daddy tace "Daddy dakai da abinda ka mallaka babu abinda zai kasance tabbatacce, idan kana ganin kana nan kanada dukiya zaka tafi ka barta amma idan banida rabon arziki bazan taba amfanuwa da abinda kabari dinba kuma koda duk abinda Ke cikin duniyar nan mallakinka ne watarana zai iya barinka ka dawo daidai da sadeeq din, ka daina zancen canzamini makaranta Daddy saboda nafison karatu anan kuma banaso kace bana yi maka biyayya amma wallahi kacire aure a tsarin rayuwata idan bada sadeeq zanyi aurenba sai kuwa idan ya mutu ne" tana gama fadin haka hawaye suka zubo daga idonta gyara zamansa yayi yana kallon sauran yayyenta da sukayi shuru cike da rashin abin cewa yace "idan na dawo haidar ka soma nema mata admission asoma processing tafiyarta" hajiya Aisha ta kalleshi ranta a bace tace "idan zaka dauki shawarata meyasa bazaka kyale ummee ba? Dan Allah karka takura mata idan so kake tayi auren jin dadi meyasa bazaka dauko shi yaron ka bashi aiki ba" karamin tsaki yayi yace "aiki? Wannan kucakin? Kinsan ni ko mai gadi idan bamai diploma ba bana dauka ko driver na yanada NCE wannan illiterate din zan dauka aiki? Wane irin aiki ma zan bashi, dan Allah abar wannan zancen ummee ninasan irin mijin daya dace da ita" shuru hajiya tayi tana kallonsa har duk saida suka watse aka barta daga ita sai babban d'anta usman tace "ni banaso ne ina nuna zakewa akan ummee idan Daddyn ku yana magana akan wane dalili zai hanata Wanda take so ai arziki na Allah ne" usman yayi tagumi yana kallonta Dama shi bai cika magana ba daga baya kuma yace "nima kaina ina so indan nuna masa ya kyaleta amma su lukman da haidar ke kara zugashi" ta mike tsaye tana cewa Allah ya sauwake ni bari inbi bayan Autar tawa in lallasheta naga ta dau zafi, murmushi kawai yayi yabi bayanta da kallo shikam zama yayi ya yana ci gaba da aikinsa a system.Lokacin da ummee ta shiga dakinta a lokacin ya kira wayarta ransa duk abace Abbansu ya gama yi masa fada tun daga yanayin daya amsa mata ta fahimci ransa babu dadi "meya sameka ne muryar ka ta sauya haka? Ko saboda abinda Daddy na yayi maka ne dan Allah kayi hakuri" yayi murmushi yace "kin manta da abinda na fada miki dazu ummee? Bana fushi da mahaifinki saboda ina so ya bani ke kuma kinsan ba karamin aiki bane dan haka bazanyi fushi ba, Abba ne ya sake nuna min bacin ranshi saboda Daddy ya turo wurinsa wai yayi min gargadi akanki wallahi ummee bazan iya auren wata ya maceba inba keba" ajiyar zuciya ta sauke tana sake rike wayar tace "Daddy yanada kafiya akan ra'ayinsa Sadeeq bansan ya zanyi dashi ba, da ace Daddy zai yadda dakai sadeeq da bamu dauki wannan lokacin yana wulakanta abinda nake so ba, bai taba yimin haka ba ya kasa gano bazan iya rabuwa dakai ba hanya daya ce zata iya fiddamu daga wannan matsalar" yayi saurin magana yace "ummee banda guduwa acikin tsarinmu dan Allah inaso Daddy ya miki aure yadda akewa duk wata ya mace" murmushi tayi tace "haba sadeeq koda zamuyi shekara ashirin Daddy bai yadda ko gidan yan uwa na bazan koma ba balle nayi maganar guduwa tare da kai inaso mu samu albarka a auren mu albarka iyaye zasu yadda sadeeq mafitar itace mu dage da a'ddua" ya sauke ajiyar zuciya yana cewa "Allah ya miki albarka Allah yasa ki gama da duniya lafiya wallahi saboda halayenki masu kyau nake kara sonki" ta amsa da ameen, mommy ta turo kofar dakin ta shigo da sallama amsawa ummee tayi tace "Sadeeq Momy ta shigo sai da safe ko" yayi saurin kashe wayar ba tare da ya amsa ba murmushi ummee tayi tana kallon momy har ta iso kusa da ita ta zauna Dora kanta tayi a kafadar mommy tana cewa "mommy na ki lallasar min Daddy mana" Shafa kumatunta tayi tana cewa "na soma magana dashi ummee amma kinsan halin Daddynku amma kici gaba da addua idan sadeeq mijinki ne ko kintafi sai kin dawo masa sannan kuma ina fada miki ummee kar soyayya ta rufe idonki kifara yiwa Daddy rashin kunya banji dadin abinda kikayi dazu ba batarbiyar ki kenan ba ummee" kara lafewa tayi jikin mommy tace "kiyi hakuri bazan sake ba" gyada kai tayi tana cewa "yanzu zakije wajen mahaifinki ki bashi hakuri shima baiji dadi ba tunda Abu kike nema awurinsa dole zaki kwantar dakai".
*jini yafi ruwa kauri*
*FIYYAH*
YOU ARE READING
JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)
Fanfictionlabarin ya kunshi soyayya da k'iyayya ya kunshi Arziki da talauci.