JJT 8

15 1 0
                                    


*Safiyyah Galadanchi*

*JAJIRTACCE ( ABUBAKAR SADEEQ)*

*shafi na takwas*

Musamman tayi kwanciya irin wadda zata ji dadin zubar da hawayenta gaba daya, tunani babu kalar da batayi ba ko zata bar garin nan ne ta gudu ko kuma ta tafi dangin mamanta? Daga karshe dai ta goge hawayenta tace "rayuwa ta ce bazan taba yadda hakanan ta lalace ba"
Gyara kwanciyarta tayi ta dauki wayarta takira layin sadeeq ya Daga amma sai taji kamar yana cikin hayaniya a bangarensa kuwa sai yace mata "ina cikin kasuwa ummee zankira ki idan na Fita" ta kashe wayar ba tareda tayi magana ba.

Usman ya kalli Daddy yace "Daddy inada shawara mana game da ummee akan yaron nan" Daddy yayi murmushi yace "ai usman na gama magana akanta danma bance a hada aurenku da Nasu ba itada lukman" Wanda yake karami duka acikinsu ya gyara zamansa dakyau yana cewa "Daddy nifa banga amfanin takurawa ya mace ba awurin zaben abokin rayuwarta bafa wanine zai zauna mata dashi ba it's zata zauna da kayanta iyaka ci Daddy idan kaji zaka iya taimakawa kawai zakayi saboda tana yarka amma meye amfanin auren mijin da bata so kuma adawo ana Dana sani kasan fa halin yarinyar nan" dama shi haka yake Mudassir bai taba yin abinda yake ganin takurane ga rayuwar wani kuma shi inba shawaraba bayason yaga antilasta mutum yin abinda bayaso karami ne shi acikin su amma da halin manya Daddy ya juyo yana kallonsa yace "kai karamin yaro ne akan wane dalili zan dauki yarinya inbawa talaka Wanda ko certificate bashida ballanta ayi maganar degree ko masters ko a ganinka Mara future irin wannan ya dace da kanwarka"? Ya gyada kai yana murmushi yace " amma Daddy Kanada damar da zaka maidashi yadda kakeso ummee macece tanada rauni idan har ka tilasta ta ka hadata da lukman zaka lalata rayuwarta ne maimakon auren da tayi saboda Neman aljana sai ya turata zuwa ga Neman halaka wallahi Daddy kiyayya a tsakanin mata da miji ba karamin balai bane" usman ma yace "bayan wannan ma zata iya yin wani tunani da ba shikenan ba gashinan muna gani ya kalli haidar yace "ai kasan kanwar BIG da mukayi karatu tare a UK? Wallahi exactly irin abinda ya faru da ita kenan wai babansu da babanta basa shiri sai suka hana auren at the end ba ciki yayi mata ba saida cikin yakai wata biyar aka gane Ashe tun bayan lokacin suka kulla wannan sharrin da auren aka yi musu duk da bai kai ga haka ba kuma Daddy ga lukman nan ka sani agabanshi nake fada maka wannan maganar wallahi har yanzu bai bar shan sigari da giya ba bayan haka kuma yan mata da bibiyarsu sai abinda ya karu" Daddy ya danyi shuru sai yace "zanyi tunani naga abinda ya dace" mudassir yace "Daddy ka yi tunanin abinda ya dace kamar yadda kace ya kalli haidar dake hararar su yace "kaga haidar yana cikin masu Baka shawara ka tursasawa ummee ba kuma abinda ya ka mata bane ka sake bincike akan yaron" Daddy ya tabe baki kawai da alkawarin tabbas sai ya nunawa ummee fushinsa matuka.

Tundaga lokacin ta daina cin abinci taredasu idan har zatayi farin cikin to idan tana tareda sadeeq ne ko kuma Suna waya amma daga ta shigo gidan duk wata fara'a da farincikin ta suke gushewa.

Yauma dawowarta kenan daga makaranta sadeeq ya sauka bakin gate yace "Indai kikaga Nazi gidanku harna wuce nan nashiga to wurinki Nazo amma irin yanzu da nadawo dake daga makaranta nan zan ringa tsayawa muyi sallama" Ta kalli ledar da suka siyo Abu a ciki ta kalleshi tace "ka dauki dayan mana" ya girgiza mata kai yana cewa "ke kika ce kinaso ai" bata yadda ba saita juya ta Ciro dauri daya tasa a wata ledar bayan ta cire drinks dinda me ciki ta saka ta hada da drinks din ta mika masa tana cewa "ka kaiwa laila idan kai Baja so ni sunyimin yawa drinks din nan ma akwai a part dina kaga zai zama barna wannan" ya karbi ledar yana cewa "ki gaishemin da mutanen gidan".

Oda tayi aka bude mata gate din bata jira amsa gaisuwar da suke mata ba ganin lokacin sallar magrib yayi ta shige, ledodin ta ta deba tareda jakar ta ta nufi cikin gida a palon kasa babba ta same su zaune kamar suna jiran wani Abu duk suka zuba mata ido, sake daure fuska tayi tamau ta karaso da sallama abakinta suka amsa  karasawa tayi kusa dasu ta durkusa ta gaida kowannensu sannan ta mike zata wuce usman yace "ji mana kanwata" ta tsaya tana kallonshi ya sake cewa "ledar hannunki ta burgeni" murmushin da ba tayi niyya ba ya subuce mata ta juya tana cewa "duk mai so sai ya biyoni in sammasa" ya mike tsaye yana bin bayan ta tareda cewa "shi gani baci ba" saida ta karasa korido din sannan ta tsaya ya karaso yana kallonta yace "kin kuwa San kin rame? Ki jirani inada magana dake idan munyi salla" ta gyada masa kai saida ta shiga kitchen ta dauki plate sannan ta karasa dakinta.

Sai bayan tayi sallar ishai sannan ta fito Palo tareda dauko plate din ta ajiye kan table dake gabanta kankara acikin bowl da cup bude ledar tayi ta juye abinda ke ciki a plate yaawunta ya wani irin tsinke ita dai tunda take bata taba siyan nama a waje ba wannan karon kuma kallonshi kawai tayi taji tana so yadda taga sun gaisa da sadeeq  da alama sun saba da juna, daukar daya tayi ta saka abaki tayi murmushi tace "tab... Wallahi Ashe nabar dadi zata kuma daukar wani aka turo kofar duka yayyenta ne banda lukman ance yaje kano wurin babanshi mudassir ya kalli plate din gabanta yana zaro ido yace "tsuntsu daga sama..."? Tayi dariya tana cewa " mai rai ne wannan tsuntsu ba gasashe bane" yayi dariya ya zauna kusa da ita ya dauki daya yana sawa a baki yace "a ina mai naman nan yake" ta dauki Fanta ta zuna acikin cup tace "can hanyar fitowa daga makaranta ne na gani sai sadeeq ya tsaya ya siyamin" murmushi mudassir yayi yace "soyayya ruwan zuwa kenan, Yaya usman kana ji dai ko" sai dukansu suka saka hannu tareda ita suka cinye sannan usman yayi gyaran murya yace "Yaron nan kafin Daddy yayi masa iyaka dake Dan Allah kin taba ji ko wani acikin securities din gidan nan sun samu sabani?" Mudassir ya karbe yana cewa "sabgogin gabansa ma yake yi Abu daya me shigo dashi gidnnan idan ya dawo da ummee daga makaranta" tayi shuru tana kallonsu sai daga baya tace "Shi Daddy Abu daya yake dubawa a tareda sadeeq din shine kudi, da ace sadeeq dare daya zai tashi ya tsinci Kansa acikin daula yana hawa manyan motoci to Daddy bazai nemi ya binciki halayensa ba haka zai mika masa ni, da ace wani mai kudi zai zo yana sona yanzu karkuyi mamaki Daddy shima bazai binciki halayensa ba shi kudi kawai ya sani" Shaheed yace "kudi kuma ba abinda za'a duba bane a bayar da aure akwai hadisi ingantacce dayace *Mu'awiya yace manzon Allah (SAW) yace idan Allah ya soka da Alkhairi sai ya sanar dakai addininsa* bayani mai mahimtarwa shine koda ka Tara duniya da abinda yake cikinta to Allah bai soka da Alkhairi ba domin ita dukiya musiba ce sai dai yadda zaka yi amfani da ita idan ta halal ce ya kasance ta zame maka hanyar zuwa aljanna" Mujaheed ya karbe yana cewa "sosaima Dan haka yanzu muyi magana akan mafita Daddy duk bazai saurari wannan zantukan namu ba, Sadeeq din nan a zamanku dashi kin fahimci ya taba karatu kuma a wane mataki ya tsaya" ta karkace kai tace "duk lokacin danayi masa maganar karatu sedai kawai yayi murmushi bai taba bani amsa ba" usman ya danyi karamin tsaki yace "karki damu zamuyi bincike a kanshi da dalilin hakan amma ki gwada sake yi masa magana sai ki nuna masa idan har yanada qualification mai kyau Daddy zai soshi ko baya so indai da gaske yana sonki zai yi karatun" mujahedeen yayi murmushi yace "ina mamakin namiji girmansa ace baiyi karatu ba ai yanzu kai ya waye wallahi ni har kama yake min da masu PhD" har ita saida tayi dariya.
Nan suka zauna suna bata labari irin Wanda zai saka ta farin ciki har karfe goma na dare sannan sukayi mata saida safe.

Lokacin daya Isa gida shikuma da laila ya soma cin karo ya mika mata ledar yana cewa "gashi inji ummee tace in kawo miki" ta karba tana murmushi har seda hakoranta suka fito tace "Yaya don Allah ka aureta" kallonta yayi tareda tausayawa kanshi bayaso ya yadda da raunin da zuciyarshi tayi a kan ummee amma sai ya ringa ji kamar bazai sameta ba.

*Jini yafi ruwa kauri*

*FIYYAH NA GAISHE KU*

JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)Where stories live. Discover now