*SAFIYYA GALADANCHI*
*JAJIRTACCE ABUBAKAR SADEEQ*
*SHAFI NA TALATIN DA SHIDA*
A babban palon Daddy suka zauna, sai ya sauka kasa yana gaida shi "lafiya lau abubakar, ka koma kan kujera mana" murmushi sadeeq yayi ya kasa komawa kan kujera Daddy yace "abinda ya saka na kiraka shine kawai inaso inbaka hakuri akan abinda ya faru, wallahi koda bakada ko sisi bakada aikinyi na fahimci irin mijin daya dace da ummee kaine, tunda nake maka abubuwa marasa dadi baka taba kin girmama ni ba baka canza mini ba haka ma yarinya ta banga abinda ya sauya daga gare ta ba Kayi hakuri Allah yayi muku albarka Allah ya sauketa lafiya" sadeeq ya dago ya kalle shi ya sauke idonta kasa yace "Daddy baka yimin komai ba bakada banbanci da Abba tun kafin ka bani hakuri dole nake hakuri dakai tunda nakeson abinda ka haifa auren ummee kadai daka bani bazai bari naga laifinka ba koda naman jikina kake yanka" murmushi daddy yayi yace "maganar aiki zan baka a company na nan dan su haidar sun koma Abuja sai mudassir kawai da Buhari suka rage" sadeeq yace "ai jiya muka dawo daga Abuja ina shirin komawa ne dan dama da aikina dalili ya saka ban karba ba sai yanzu" Daddy ya shafa fuskarsa yace "duk da haka ina bukatar takardunka inaso nayi maka abin alkhairi aikin da kakeyi bazai hana wannan ba insha Allahu" sadeeq yayi masa godiya sosai har saida dady ya nuna masa bacin ransa sannan ya hakura da zai wuce yayi masa kyauta sannan yace ina gaida iyalin naka.
Ba karamin dadi labarin nan yayiwa ummee ba tasan yanzu basuda sauran matsala.
tana kwance ya shigo dakin da shirinsa bata san ina za shi ba yana gyara agogon hannun sa wani kamshi yake da bata taba jin irinsa ba, tayi masa kallon tsaf "ina zaka da wannan adon haka"? Kwantawa yayi gefenta yace "naga kema kinyi min wannan kwalliyar ai shiyasa nima nayi miki" dadi taji sosai ta dora kanta gefen kirjinshi tace "babbar matsalata yadda zaka tafi ka barni" yana shafa gashin kanta bayan ya zame mata dankwali yace "nima kaina hakane ummee yaushe zakuyi exam"? Tace "bayan sallar nan zamu yi exam" nasan idan na tafi yanzu kila sai salla kuma exam din zai dauki wata daya idan kun gama seki sameni can amiki booking flight" hawayenta kawai yaji yana jika masa jiki tace "nifa yanzu ne banaso ka tafi ka barni sannan da cikin nan zan iya hawa jirgi ma" hawayen ya share mata yace "to zan zo da mota in daukeki" shuru tayi bata amsa mishi ba ashe bacci tayi a fili yace "da kinsan wahalar da nake sha araina in na tuna zan tafi na barki nima da kin tausayamin".
Dakanshi ya hada mata kayanta wanda zatafi bukata yasa a mota tun karfe biyar suka bar gida dan dole da mota zai tafi, Abba ya kira bayan sun isa ya bude musu gida anan sukayi sallar asuba sannan yayi harmar tafiya, hawaye yagani a idon ummee yayi murmushi yace "baifi sati biyu ba fa zanyi in zo ba sannan gakinan a wurin Anty kiyi hakuri kinji" Anty tayi murmushi tace "kaga kama hanya ka tafi inka biyewa wannan ba yanzu ba kaida barin garin nan" juyawa yayi ya fita yana amsa adduar da Anty take masa, goge hawayen ta tayi ta kwanta dama bacci take ji sai karfe goma ta farka ta fara shirin zuwa makaranta laila kam tuni ta wuce sai anty ce ta kawo mata abinci, ba karamin dadi taji ba ganin tuwo ne, ameera takira bayan ta gama tace tazo dan Allah ta dauketa dan motar shi ce sukazo da ita kuma da ita yayi tafiya.
Ameera na ganinta ta soma yi mata tsiya tana cewa "naga wannan cikin naki kullum kara girma yake ko duk kulawar da yake samu ce" tsaki tayi tana cewa "lallai ma matarnan ke naki da yayi girma lokacin baya samun kulawa ne karfa ki rainani" Ameera tayi dariya "kulawa kai yarinya kinsan ance mace tafi zaqi in tana da ciki" ummee ta zaro ido tace "ok dama hakane, gaskiya dan jiya naci kwakwa yanzu haka karfin hali kawai nayi na fito kar Anty tayi wani tunanin" Ameera tace "sannu amma na tausaya miki Allah ya saukeki lafiya".
Kullum kwana suke suna hira a waya yanata neman hanyar da zai gudo daga Abuja amma aiki yayi yawa dole sai break din salla da suka samu yazo tareda su Habeeb, acan ya same ta tana kokarin goge gidan bayan ta share cikinta ya kara girma, kallonsa tayi taga yayi kiba yayi haske yatsunsa har kyalli suke tayi murmushi tace "wai nikam hutu kaje yi ko aiki kaga yadda kayi kiba" yana rike da hannunta yace "duk kibar kewarki ce matata" ya fada yana zaunar da ita gefen gadon, dan matsawa tayi baya tace "malam kabari kaci abinci mana nazo dashi daga gidan anty" "Allah ya tsareni inci abinci yanzu gaki a kusa dani nidai kawai ki barni" murmushi tayi tace "matsalarka kenan ko".
Sai magrib ta shiga bangaren ummu suka gaisa Habeeb yace "kidaina biyewa wannan yaron baida kirki tun safe fa muka shigo se yanzu muke ganin ku" kasa magana tayi saboda kunya sai sadeeq ne yace "aiki tayi fa kasan gidan yayi kura" hararar shi habeeb yayi batareda yayi magana ba.
Kwana uku sukayi suka juya dama salla kawai suka zo yi tafiyarsu da sati daya ta fara exam, bayan sati uku ta kammala, cewa tayiwa anty zataje gida anty tace wurin me, sadeeq ne zaizo ya dauketa kafin hutunsu ya kare kallon mamaki anty tayi mata tace " da wannan cikin saboda haukan ku idan kin bishi can kiyi masa uwar me, yaran zamani" shuru ummee tayi gabanta na faduwa dan gaskiya ita saitabi mijinta anty ta sake cewa "ina shi sadeeq din" muryarta na rawa alamar kuka tace "yana hanya" shuru anty tayi dan jiran zuwan nashi kawai take aiko bayan laasar sai gashi yanata washe baki abinci kawai yaci anty ta balbaleshi da fada tace "tafiya mai wannan uban nisa da mace mai tsohon ciki da mota kuma ka wahala ka wahalar da itam, to babu inda zakaje da ita yanzu dai ka tafi da ita can gidan ka tsinci uwar da zaka tsinta ka dawo da ita" Abba da shigowarshi kenan ya kallesu yaga hawaye a idon ummee yace "Aisha don girman Allah ki kyalesu suyi tafiyarsu kedai kiyi addua Allah ya tsare" zatayi magana ya tareta yace "um'um barsu su tafi, sadeeq a lallaba kaji banda sharara gudu Allah yakaiku lafiya ya kiyaye" ya juya ya fita yana mamakin karfin hali irin na anty ita kuma ranta inyayi dubu ya baci bata kara cewa komai ba saida zasu tafi ta amsa musu ciki-ciki, washe gari tun da sauran duhu suka bar gidan suka kama hanya.
Tun a hanya ta fara jin ciwon mara amma bata nuna masa ba har suka isa ko minti ashirin basuyi da shiga gidanba ta fara juyi ga yunwa tanaji amma ta kasa cin abincin da ummu ta basu karshema saita fara kuka ta kama masa hannu ta rirrike kamar zata karyashi, ummu tace "wai nikam wannan cikin nata yama shiga wata bakwai" sadeeq ya girgiza kai dakyar yace "watan shi bakwai ma kenan" ummu tace "kaga asibiti zamuje gaskiya" mikewa yayi ya dauki key sannan ya dauki ummeen data kasa ma mikewa tsaye saboda azaba.
YOU ARE READING
JAJIRTACCE (Abubakar Sadeeq)
Fanfictionlabarin ya kunshi soyayya da k'iyayya ya kunshi Arziki da talauci.